Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Dakarun IRGC Ya Ce: Yakin Kwanaki 12 Kan Iran Ya Canza Tunanin Makiya
Published: 25th, October 2025 GMT
Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Yaƙin da aka ɗora wa Iran ya canza daidaiton da ke tsakanin Sahayonayya da Amurka
Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Hussein Ta’ib, ya ce: Yaƙin kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyya ta ɗora wa Iran, ba wai kawai bai cimma komai ga Isra’ila ba ne, har ma ya canza daidaiton dabarun Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila gaba ɗaya.
A lokacin taron tattaunawa na 31 na ƙungiyar Jaruman Musulunci a Qom, Hussein Ta’ib ya ce: “Dakarun kare juyin juya halin Musulunci da sojojin Iran sun kalubalanci masu girman kai inda suka kai wani mataki cikin saurin na zarce lissafin siyasa da tsaro idan aka kimanta.”
Da yake magana game da bitar dabarun tsaron ƙasa na Amurka bayan rugujewar Tarayyar Soviet, Hussein Taeb ya ce: “Burin farko na Amurka da zarar an shiga shekara ta 2025 shine mayar da hankali kan kawar da duk wata cikas gare ta daga ikon duniya. Duk da haka, a cikin bitar shekara ta 2020, Amurkawa sun yarda cewa ba a cimma wannan burin ba kuma sun ayyana shekaru goma daga 2020 zuwa 2030 a matsayin shekaru goma masu mahimmanci ga makomarsu da makomar Gabas ta Tsakiya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rear Admiral Sayyari: Sojojin Iran A Shirye Suke Su Fuskanci Kowace Barazana October 25, 2025 Shugaban Kasar Venezuela Ya Ce; Amurka Tana Son Kaddamar Da Yaki Kan Kasarsa October 25, 2025 Bangarorin Falasdinawa Sun Amince Da Shirin Gudanar Da Zirin Gaza Nan Gaba October 25, 2025 Nawwafa Salam: Yin Mu’amalar Diplomasiyya Da “Isra’ila” Ba Shi Alfanu October 25, 2025 Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Watsi Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Masa October 25, 2025 Kungiyar Kwallon Kafa Ta Futsal Ta Matan Iran Sun Sami Nasara Akan Kasar Bahrain October 25, 2025 Antonio Gutrress: MDD Tana Bukatuwa Da A Yi Ma Ta Kwaskwarima October 25, 2025 Lebanon: An Sami Shahidai 3 Sanadiyyar Hare-haren HKI A Kudancin Lebanon October 25, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Isra’ila Kan Kasar Lebanon October 24, 2025 Rasha Ta Jaddada Cewa: Kasashen Turai Sun Taka Doka Kan Batun Makamashin Nukiliyar Iran October 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima Ya Isa Abidjan Wajen Rantsar da Shugaba Ouattara
Daga Bello Wakili
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa Abidjan na kasar Côte d’Ivoire, domin wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen rantsar da Shugaban Alassane Ouattara a wa’adinsa na hudu.
Za a rantsar da Shugaban ne a yau Litinin, 8 ga watan Disamban 2025, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abidjan, wanda shugabanni daga kasashen Afrika da sauran manyan baki daga sauran kasashen duniya za su halarta.
Shugaba Ouattara ya sake lashe zabe ne a ranar 25 ga watan Oktoban 2025, inda ya sake samu wani sabon wa’adi na jagorantar kasar. Sake Rantsar da shi na nuna da ci gaban da dimokuradiyya a kasar ta Côte d’Ivoire da kuma kyakkyawar dangantakarta da Najeriya.
A cewar Fadar Shugaban Kasar, halartar Mataimakin Shugaban Kasa Shettima a taron na tabbatar da jajircewar Najeriya kan goyon bayan mulkin dimokiradiyya a yammacin Afrika. Najeriya na ci gaba da jaddada muhimmancin bin muradin jama’a da tabbatar da sauyin mulki cikin lumana a yankin.
Najeriya da Côte d’Ivoire na da kyakkyawar hulda ta aiki karkashin ECOWAS, Tarayyar Afrika, da kwamitin kasashe biyu, inda suke yin hadin gwiwa a fannoni irin su tsaro, kasuwanci, noma, yakar safarar mutane, da tattalin arzikin dijital. Dubban al’ummar ‘yan Najeriya da ke Côte d’Ivoire ma na kara zurfafa dangantakar tattalin arziki da al’adun kasashen biyu.
Ana sa ran Mataimakin Shugaban Kasa zai koma Abuja bayan kammala taron rantsarwar.