Aminiya:
2025-10-24@13:42:28 GMT

Gwamnan Neja ya ba dukkan iyalan wadanda suka kone a gobarar tankar mai N1m

Published: 24th, October 2025 GMT

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sanar da bayar da tallafin naira miliyan ɗaya ga duk iyalin da ya rasa ɗan uwa a gobarar tankar man da ta faru a garin Essa, Karamar Hukumar Katcha.

Haka kuma, ya ba da tallafin naira dubu ɗari biyar ga kowanne daga cikin waɗanda suka jikkata a lamarin.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin da abin ya shafa, inda ya tantance tare da ganawa da shugabannin al’umma da mazauna yankin.

Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027 NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas?

Wannan sanarwa ta fito ne daga Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Bologi Ibrahim, a daren Alhamis.

Mummunan hatsarin gobarar tankar man ya faru ne da misalin ƙarfe 3:45 na ranar Talata, lokacin da wuta ta tashi a cikin tankar man fetur din da mutane ke diba daga tankar da ta kife a kan hanyar Bida–Badegi–Agaie.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, Abdullahi Arah, ya tabbatar da cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai 42, yayin da waɗanda suka jikkata suka kai 52.

Arah, wanda ya bayyana hakan a hirarsa da gidan talabijin na Arise, ya danganta faruwar lamarin da lalacewar hanya da kuma zafin rana a yankin, wanda ya taimaka wajen haifar da gobarar.

“Ina jin baƙin ciki matuƙa da faruwar wannan lamari,” in ji Gwamna Bago, yayin da yake addu’ar samun sauƙi ga waɗanda ke jinya a asibitocin Bida da Abuja.

Sai dai ya soki dabi’ar dibar man fetur daga tankar da ta kife, yana mai cewa hakan na da matukar hatsari kuma babban laifi ne.

“Mun zo ne don yin ta’aziyya da su kan asarar rayuka, da kuma tunatar da su muhimmancin kiyaye rayuka.

“Abin takaici ne a ce tankar man ta faɗi, sai mutane su fito da jarakuna suna dibar man. Wannan sata ce, kuma dole ne a dakatar da ita. Ba za mu goyi bayan hakan ba,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma ce fitaccen ɗan kasuwa, Aliko Dangote, ya yi alkawarin gyara hanyar Mokwa–Lambata, kuma aikin zai fara nan ba da jimawa ba.

A ƙarshe, gwamnatin jihar ta bayyana cewa za ta gina cibiyar kula da lafiya ta farko a garin Essa domin biyan buƙatun lafiyar al’ummar yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gobarar tankar mai

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum

Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja.

Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da tankar ta kife kuma ta kama da wuta yayin da jama’a ke ƙoƙarin ɗibar mai.

Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi

Wasu da dama sun ji rauni kuma an garzaya da su Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Bida.

Shehu, ya ce mata ne suka fi mtuuwa saboda maza sun tafi gona lokacin da lamarin ya faru.

Ya zargi mazauna yankin da ƙin bin gargaɗin da aka sha yi musu kan hatsarin ɗibar mai daga tankar da ta kife.

Hakimin Essa, Alhaji Adamu Bagudu, ya tabbatar da cewa an binne mutum 28, ciki har da mata 24.

Ya ce an sha gargaɗin jama’a kan hatsarin wannan ɗabi’a, amma talauci da wahalar rayuwa ya sa mutane yin watsi da igargaɗin

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), ta ce aƙalla mutum 80 lamarin ya shafa, inda aka kai wasu 17 Abuja domin samun kulawa ta musamman.

Gwamnan Gombe kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, ya bayyana alhininsa kan lamarin tare da kiran gwamnati da ta ƙara tsaurara matakan tsaro da kuma gyaran hanyoyi.

Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta kuma roƙi Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta gyara hanyar Bida zuwa Agaie wadda ke janyo salwantar rayukan mutane.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu
  • Gwamnatin Tarayya ta yi jimami kan mutuwar mutanen da suka rasu a fashewar motar mai a Jihar Neja
  • ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum
  • Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja 
  • Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja
  • Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a fashewar tanka a Neja
  • Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja
  • Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 30 a Neja
  • Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja