Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana
Published: 22nd, October 2025 GMT
Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da alkaluman kasuwar yawon shakatawa ta kasar tsakanin watan Janairu zuwa na Satumban bana. Kuma sakamakon binciken kididdigar da aka yi ya nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Satumban bana, adadin yawon shakatawa da mutanen kasar Sin suka yi a cikin gida, ya zarce biliyan 4.
Haka kuma, jimillar kudaden da mutanen kasar Sin suka kashe a harkokin yawon shakatawa ya kai kudin kasar Yuan tiriliyan 4.85, adadin da ya karu da tiriliyan 0.5 bisa na makamancin lokacin a bara, wanda ya kai kaso 11.5 bisa dari. Daga cikinsu, akwai tiriliyan 4.05 da mazauna birane da garuruwa suka kashe, adadin da ya karu da kaso 9.3 bisa dari. Sai kuma tiriliyan 0.8 da mazauna yankunan karkara suka kashe, adadin da ya karu da kaso 24 bisa dari. (Murtala Zhang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: adadin da ya karu da kaso
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC
Kwamandan ya ƙara da cewa yayin yaƙin “Operation Zero” na shekarar da ta gabata (Disamban 2024 zuwa Janairun 2025), mutane 432 ne suka mutu, yayin da 2,070 suka jikkata a haɗura 533; adadin ya ragu idan aka kwatanta da na baya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA