2025-09-20@10:23:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1705
«Palasɗinawa»:
An shawarci Musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye na tawali’u kamar yadda Annabi Muhammadu ya yi misali da su don yin rayuwa mai inganci. Babban Limamin Masallacin Darul Khair Imam Abdulmumini Abdulrafiu-Onilaru ya bada nasihar ne a cikin hudubar Juma’a da ya gabatar a garin Ilorin na jihar Kwara. Ya ce...
Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar Jigawa, ta shirya taron yini daya a birnin tarayya tare da hadin gwiwar ELIP kungiyar farar hula ta musamman, domin tattara kayan aiki na kasafin kudin 2026. A nasa jawabin kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Alhaji Ibrahim Babangida Umar Gantsa ya bayyana mahimmancin taron, inda...

Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Iran tana da ‘yancin mayar da martani ga duk wani mataki da ya sabawa doka Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa a jiya Juma’a dangane da haramtaccen matakin da kungiyar Tarayyar Turai Troika ta dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran...
A yau Juma’a ne aka rufe taron dandalin tattauna batun tsaro na Xiangshan karo na 12 a birnin Beijing, bayan mahalartansa sun zurfafa tattaunawa karkashin jigon “Mara baya ga odar kasa da kasa da ingiza ci gaba cikin lumana.” An bude taron ne a ranar Laraba, ya kuma hallara sama da wakilai 1,800, ciki har...
Tawagar gwamnatin jihar Jigawa ta shiga sahun sauran kasashe da suka halarci taron kasa da kasa na Halal da ke gudana a Malaysia (MIHAS), domin neman jari da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa na tattalin arziki. Tawagar karkashin jagorancin Kwamishinan Harkokin Kiwo, Farfesa Abdurrahman Salim Lawal, ta hada da Dr. Saifullahi Umar, Darakta-Janar na Hukumar Zamanantar...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa a shirye ta ke, ta haɗa kai da APC, idan an shirye karɓar sharuɗansu. Kwankwaso, ya faɗi haka ne a gidansa da ke Miller Road a Kano, lokacin da ya karɓi baƙuncin tsohon jigon APC a jihar, Buhari Bakwana,...
Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Gombe, ta kama mutum shida bisa zargin tono gawar wani mutum a kabari tare da cire sassan jikinta domin yin asiri. Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Kawuji Sarki, mai shekaru 39, ya amsa laifin. Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Janye...
Matasa takwas a jihar Jigawa sun lashe tallafin kasuwanci na Naira miliyan biyu daga British Council ƙarƙashin shirin Youth Connect. Kowane ɗaya daga cikinsu ya samu Naira dubu dari biyu da hamsin domin fara ayyukan kasuwanci. An gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar Kings Trust International, CITAD, da gwamnatin jihar Jigawa. Matasa...
Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI. Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin...
Wasu kafafen diblomasiyya nakasashen yamma sun tabbatarwa wakilin tashar talabijin ta Al-mayadeen na kasar Lebanon kan cewa gwamnatin Amurka ce zata jagoranci kasashen yamma wajen tattaunawa da karar Iran. Majiyar ta kara da cewa turawan sun mika wuya ga takurawar washintong don jagorantar tattaunawa da JMI kan shirinta namakamashin nukliya da kuma batun yin watsi...
An sabunta wannan ƙididdiga kusan shekaru shida kamar yadda ya kamata a yi. Abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, ƙididdiga da bayanai su kasance masu sahihanci kuma a yawaita samun su. “An sabunta ƙididdigar, kuma ya nuna mana ainihin halin da muke ciki. Don haka, duk wani ra’ayi na...
A ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, sojojin Japan suka tarwatsa wani sashi na layin dogo dake karkashin ikonsu, a kusa da birnin Shenyang, tare da zargin sojojin kasar Sin da aikata barna, domin su fake da hakan wajen kai hari barikin sojojin Sin dake kusa da birnin na Shenyang a daren ranar,...
Rahotannin cibiyoyin kididdiga a HKI sun ambaci cewa, ana ci gaba da samun yin hijirar yahudwa zuwa waje wanda shi ne mafi girma a cikin shekaru da dama. Jaridar “Ma’ariv” ta amabto wani makwararre a fagen kididdiga yana cewa; Shekarar 2024 ta fuskanci ficewar mutane masu yawan gaske daga “Isra’ila” saboda yakin da ake yi...
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun shirya horar da aikin ceto yayin ambaliya, a Ƙaramar Hukumar Auyo. Taron horaswar ya haɗa masu ruwa da tsaki daga hukumomi daban-daban,...
A kokarin ta na ci gaba da zaburar da ma’aikatan ta, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce za ta shirya taron bitar sanin makamar aiki ga jami’an ta dake dawainiya da alhazai a gida da kuma kasa mai tsarki. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed umar labbo ya bayyana haka bayan kamala...
Rundunar ‘yan Sandan Jihar Jigawa ta bada sanarwar nasarar cafke wani sojan bogi da ƙarin wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota a ƙauyen Sabon Sara. Kamar yadda Kakakin rundunar ’yan sanda na Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam ya sanarwa manema labarai a garin Dutse cewa, an kama matashin sojan bogin da abokansa...
Tun a ranar 7 ga watan Satumba, 2025, wani mutum mai suna Hussaini Manager ya kai rahoto ofishin ’yansanda na Kafin Hausa cewa an sace masa mota ƙirar Golf mai launin shuɗi mai lambar MGA 108 JG a Agura Motor Park, Kafin Hausa. Bincike ya gano cewa ɗaya daga cikin mutanen na yin sojan gona...
Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa, SEMA, tare da hadin gwiwar Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, sun shirya gwajin yadda za a gidanar ayyukan ceton ambaliyar ruwa a karamar hukumar Auyo. Gwajin wanda ya tattaro masu ruwa da tsaki daga...
Wani makami mai linzami na Yemen ya tilastawa jirgin saman fira ministan gwamnatin Isra’ila saukar gaggawa Kafofin yada labaran yahudawan swahayoniyya sun watsa rahoton cewa, an tilastawa jirgin saman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu yin saukar gaggawa a lokacin da ake atisayen soja bayan harba makami mai linzami daga kasar Yemen zuwa yankunan...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan asarar rayuka da aka yi a gobarar da ta tashi a ranar Talata a Afriland Towers da ke Broad Street, a Legas. A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya...
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa Naira biliyan 330 a matsayin tallafi. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an raba kuɗin ne ta Ofishin Tsare-tsaren Jin-ƙai na Ƙasa (NASSCO), domin rage wa talakawa wahalar cire tallafin mai da...
Hukumar shirya jarabawar ta kasa NECO ta fitar da jarabawar SSCE dalibai dubu 818, 492 suka sami kiridit 5 zuwa sama da suka hada darasin Ingilishi da Lissafi. Adadin bisa ga sakamakon ya nuna dalibai kashi sittin da biyu sun smai nasara. Magatakardar NECO kuma Babban Jami’in Hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido...
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mani Malam Mumini ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Gumi kan mumunan al’amuran da suka salwantar da rayukan mazauna kauyen Fas su 19 a makonnin da suka gabata. Malam Mumini ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci wasu jami’an gwamnati da suka kai ziyarar jaje ga al’umma, inda...
Kafofin yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa, an gudanar da wani dogon zaman tattaunawa a birnin London a yammacin jiya tsakanin ministan harkokin wajen Syria Asaad al-Sheibani da ministan kula da tsare-tsare na Isra’ila Ron Dermer, tare da halartar jakadan Amurka na musamman Tom Barak. Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa ganawar ta dauki...
Dan wasan kokawa mai nauyi na Iran ya samu lambar zinare ta farko a gasar cin kofin duniya. Wasan karshe da na rarrabuwar kawuna na manyan nau’ikan nau’ikan nauyi hudu na gasar kokawa ta duniya da aka yi a yammacin Lahadi a Zagreb. A cewar Pars Today, Amirhossein Zare daga Iran wanda ya taba zama...
Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi...
Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin...
Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, fiye da Falasdinawa 35 ne su ka yi shahada daga Safiyar yau Laraba zuwa tsakiyar rana,sanadiyyar hare-haren da HKI take kai wa. Hakan tana faruwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta yi gargadi akan cewa asibitocin yankin sun kusa daina aiki baki...
Nijeriya dai ta daɗe tana fama da ta’addancin Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban...
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi...
Falasdinawa 78 ne aka kashe a yau a Gaza, mafi yawansu a birnin Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kasa da kuma umarnin tilastawa mazauna Gaza yin kaura. An bayar da rahoton karin mutuwar mutane uku sakamakon yunwa da killace yankin. Mazauna Gaza sun bayyana tashin bama-baman a matsayin...
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani. Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai...
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa. ...
Yakin da aka kwashe fiye da shekara ana yi yankin zirin Gaza ya haifar da mummunar asara rayukan fararen hula, yayin da lamura ke ci gaba da dagulewa a yankin inda Isra’ila ke ci gaba da kisan kare dangi ta hanyar kai hare-hare ta sama da kasa da kuma tana amfani da yunwa a matsayin...
Tsohon Shugaban Ƙasar najeriya, Goodluck Jonathan, ya isa birnin Accra, na Ƙasar Ghana, domin halartar taron Democracy Dialogue na 2024 da Gidauniyarsa ta shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar. Taron na bana, mai taken “Dalilan Da Ke Sa Dimokuraɗiyya Ta Mutu”, zai hada shugabanni da masana don tattauna ci gaba, kalubalen, da makomar dimokuradiyya...
Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta. Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin,...
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a...
JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa wannan...
Babban daraktan kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya bayyana cewa taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ke tafe yana nuni da wani muhimmin sauyi na hadin kan kasashen larabawa da musulmi dangane da laifukan da ake aikatawa kan al’ummar Palastinu. A cewar Pars Today, dukkanin idanuwa a ranakun Lahadi da...

Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel...

Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake. A cewar...
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki. A ranar 4 ga Satumba, 2025,...
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba. Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi. Sanarwar ta kara...
Jami’an kasashen larabawa da na Musulmi sun bukaci daukar kwararan matakai kan Isra’ila bayan harin da ta kai a birnin Doha, inda suka bayyana harin a matsayin “na matsorata, da muggan laifuka.” Da yake jawabi a gun taron ministocin harkokin wajen kasashen a birnin Doha, Sakatare-Janar na kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya ce...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kakkausar suka ga harin da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan, inda ta bukaci kasashen Larabawa da na musulmi da su dauki matsaya daya kan matakan wuce gona da iri na gwamnatin mamayar. Basem Naim, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas,ne ya yi wannan kiran...