Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur  sun fitar da wata sanarwa a ranar Lahadi suna  musanta rahotannin kafofin watsa labarai game da faduwar birnin El Fasher a hannun Dakarun RSF, tare da bayyan hakan a matsayin farganda da kuma yakin kwakwalwa.

Sanarwar ta ce, “A halin yanzu ana fuskantar wani kamfen na kafofin watsa labarai na ƙarya da nufin tayar da hankali da kuma karya zukatan mayakan, idan aka yi la’akari da cewa kwace hedikwatar rundunar na nufin faduwar birnin baki daya.

” Sanarwar ta jaddada cewa “El Fasher shi ne shinge kumakatangar karfe da ta hana makiya kaiwa ga mafarkinsu.

Sanarwar ta zo ne sa’o’i bayan da Rundunar RSF ta sanar da ikonta na hedkwatar sojojin sa kai a El Fasher, birni na ƙarshe da har yanzu ke ƙarƙashin ikon gwamnati a yankin Darfur na yammacin Sudan.

Masu fafutuka a Sudan sun ba da rahoton ci gaba da faɗa a cikin birnin, suna tabbatar da cewa Rundunar Sojojin Sudan ta dakile wani babban hari da Rundunar RSF da ta ƙaddamar daga sassa biyar. Faɗa ya ta’azzara ne a yankin gabashin birnin, inda Rundunar RSF ta sanar da kwace ginin bataliyar sojoji ta Shida.

Duk da haka, shaidu da majiyoyin manema labarai sun nuna cewa ginin da Rundunar RSF ta sanar da kamawa tsohon gini ne da babu komai a cikinsa. Bayani game da halin da ake ciki a El Fasher  na cin karo da juna. Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance da rundunar sojojin Sudan ta fitar kan batun.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi : Iran na maraba da tattaunawar diflomatsiyya da Amurka amma cikin mutunta juna October 26, 2025 Ana Zaman dar-dar gabanin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Kamaru October 26, 2025 Faransa : An yi Zanga-zangar adawa da isar da makamai zuwa Isra’ila October 26, 2025 Hamas : Ba za mu bari Isra’ila ta sami hujjar ci gaba da yaki a Gaza ba October 26, 2025 ‘Yan Ivory Coast na jiran sakamakon zaben shugaban kasa October 26, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Shugaban Amurka Zai Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rudu October 26, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Ce: Iran, Rasha Da China Sun Aike Da Sako Mai Muhimmanci October 26, 2025 Ja’afari: Iran Tana Da Isassun Makamai Masu Linzami Masu Cin Zangogi Daban-Daban October 26, 2025 Dan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Ce: Dole Ne A Hakunta Isra’ila Kan Laifukan Da Ta Aikata October 26, 2025 Mayakan Kungiyar Kurdawa Ta PKK Sun Fice Daga Turkiyya Zuwa Iraki October 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da Rundunar RSF

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu

‘Yan sandan kasar Ghana sun sanar da cewa tserato da wasu ‘yan Najeriya 57 da aka yi faskwaurinsu, haka nan kuma wasu mutane 5 da suke aikata laifuka ta hanyar sadarwar na “Internet”

Jami’an ‘yan sandan sun kwace nau’ra mai kwakwalwa 77 da wayoyin hannu 38, sai kuma wasu motoci 2, akwatin talbijin 3, da kuma wasu na’urori da suke amfani da su a yaudarar mutane.

A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an ‘yan sandan kasar ta Ghana su ka sanar da kai farmakin a birnin Accra a ranar Laraba 22 ga watan nan na Oktoba.

Shekarun mutanen da ake amfani da su wajen yaudarar mutane ta hanyar internet suna a tsakanin 18 zuwa 26,tuni kuma an kai su asibiti domin kula da su.

Ana amfani da mutanen da aka kama ne dai ta hanyar karuwanci domin yaudarar mutane.

A watan da ya shude ma dai, ‘yan sandan kasa da kasa -Interpol- sun sanar da kama 260 a cikin kasashen Afirka 14 da suke aikata laifuka irin ta hanyar internet. Mutanen kan dauki hotunan tsiraici na mutanen da suke son cutarwa, domin daga baya su rika karbi kudi a wurinsu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada October 24, 2025 Gaza Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani  Zai Ci Gaba  Akan Yara Da Matan Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko  yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An zabi Catherine Connolly a matsayin shugabar Ireland
  • Dan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Ce: Dole Ne A Hakunta Isra’ila Kan Laifukan Da Ta Aikata
  • Jami’ar ABU Ta Karyata Zargin Da Ake yi Na Kera Makamin Nukiliya A Asirce
  • M D D Ta ce Akalla Mutane miliyan 1.5 Ne Ke Bukatar Taimakon Gaggawa A Gaza
  • Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa  A Ivory Coast
  • Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Dakarun IRGC Ya Ce: Yakin Kwanaki 12 Kan Iran Ya Canza Tunanin Makiya
  • Antonio Gutrress: MDD Tana Bukatuwa Da A Yi Ma Ta Kwaskwarima
  • Lebanon: An Sami Shahidai 3 Sanadiyyar Hare-haren HKI A Kudancin Lebanon
  • ‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu