2025-10-17@13:32:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 986

«Herbert Macaulay»:

    Iyalan marigayi Herbert Macaulay sun soki matakin gwamnatin tarayya na haɗa sunan fitaccen ɗan gwagwarmayar cikin riƙaƙƙun masu laifi a jerin waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa bayan ransu. A wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas ranar Alhamis, iyalan tare da goyon bayan dattijo kuma Atona Oodua na Yarabawa, Chief Olabode George, sun bayyana cewa kodayake sun yaba da yadda shugaban ƙasa ya girmama rawar da Macaulay ya taka a tarihin Najeriya, ba daidai ba ne kuma abin ƙasƙanci ne a haɗa shi da wasu da ake tuhuma da manyan laifuka. Akwai yiwuwar matsin lamba ya sa Tinubu cire sunayen wasu da ya yi wa afuwa saboda cece-kuce Saudiyya ta zaftare wa Najeriya guraban...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Ismail Baqaei yayi maraba da dakatar da bude wuta da aka yi tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, kuma yayi kira ga kasashen biyu da su warware sabanin dake tsakanin ta hanyar tattaunawa da kuma diplomasiya. Iran ta dade tana ba da shawarwarin magance matsalolin tsaro a yammacin Asiya da kuma Kudancin Asiya, da kuma nuna rashin amincewa kan tsoma bakin kasashen waje kan rashin fahimtar dake tsakanin kasashen musulimi,  yace rikicin dake tsakanin Kabul da islam abad barazana ce ga zaman lafiya yankin, kuma zai amfanar da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi masu so su yi amfani da tarzoma a iyaka. Rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan yayi Kamari a yan kwanakin nan inda...
    Majalisar Dattawan ta Najeriya  ta tabbatar da naɗin Farfesa Joash Amupitan, mai mukamin SAN, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a yammacin ranar Alhamis.  Tabbatar da Farfesa Amupitan, ta kasance ta hanyar kuri’ar murya da ‘yan majalisar suka gudanar bayan kammala tantance shi tare da amsa tambayoyi daga mambobin majalisar na tsawon kusan sa’o’i biyu. Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ne ya gabatar da sunan Amupitan, don maye gurbin tsohon shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya sauka daga mukamin makonni biyu da suka gabata. Amupitan, wanda ya samu rakiyar gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, da wasu jami’ai zuwa majalisar, ya gabatar da tarihin inda ya yi aiki kafin fara amsa tambayoyin ‘yan majalisar....
    Rahotanni na nuna cewa akwai yiwuwar Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire wasu sunaye daga jerin wadanda ya yi wa afuwa bayan cece-kucen da hakan ya jawo. Hakan dai ya biyo bayan ci gaba sukar lamirin hakan da jama’a ke yi, musammam kan saka wasu rikakkun masu laifi da kotu ta yanke wa hukunci daban-daban. Saudiyya ta zaftare wa Najeriya guraban Aikin Hajji da sama da kujeru 28,000 ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara Afuwar shugaban kasa da ake bayarwa a lokutan bukukuwan ƙasa, ana yin ta ne don rage cunkoso a gidajen yari da kuma ƙarfafa sulhu da haɗin kai. Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce an yanke shawarar ne bisa shawarwarin...
    Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Israel Sunny-Goli, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ya guji duk wata matsin lambar da wasu ƴan siyasa ke yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Sunny-Goli ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin halartar shirin Politics Today na tashar Channels, inda yake mayar da martani kan ficewar gwamnan Bayelsa, Douye Diri, daga jam’iyyar PDP. Ya ce, “Ina ganin Jonathan zai karɓi wannan lamari da zuciya ɗaya saboda mutum ne mai son cigaban jiharsa. Duk da maganganun da ake yi kan zai tsaya takara, bana ina ganin zai yi kuskuren hakan saboda lokaci ya riga ya wuce.” Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya...
    Jaridar Wall Street Jouranl ta kasar Amurka ta buga labarin da yake cewa, kasar Amurka ta fada girke makamai a kusa da tekun Caribbean da kuma wasu jiragen sama a arewacin kasar Venezuela. Labarin ya kara da cewa;Rundunar da ma’aikatar yakin Amurka ta “Pentagon” ta girke ta zaratan mayakan kundunbala ce wacce ta kashe Usama Bin Ladan a kasar Pakistan. Wani sashe na rundunar ya hada jirage masu Angulu da ake iya amfani da su wajen kai hari. A cikin kwanakin bayan nan dai Amurka ta kara matsin lamba akan kasar Venezuela ta hanyar kai wa jiragen ruwan da suke fitowa daga kasar hare-hare, bisa zargin cewa suna dauke da muggan kwayoyi zuwa Amurka. Gwamnatin Venezuela da kasashen yankin masu...
      An dage ci gaba da binciken har sai ranar 20 ga wata. Maris na shekara mai zuwa, a makon da ya gabata, dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Manchester domin gudanar da jana’izar Hatton, wanda ya kasance shahararren dan wasan dambe a kasar Ingila.   Dan wasan gaban Oasis Liam Gallagher, tsohon dan wasan Ingila da Manchester United Wayne Rooney da kuma tsohon zakaran ajin masu nauyi na duniya Tyson Fury na daga cikin taurarin duniya na wasanni da suka halarci jana’izar Hatton. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc  October 15, 2025 Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo October 14,...
    Wani binciken tattara ra’ayoyi da aka gudanar a shekarar nan ta 2025, ya nuna kaso 72.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun gamsu da manufar Sin ta bude kofa, da kasuwarta mai amincewa da kyakkyawar takara. Kana kaso 79.8 bisa dari na ganin babbar kasuwar Sin ta samar da muhimman damammaki ga kasashensu na asali. (Saminu Alhassan)   ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya October 16, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona October 16, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025
      “Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana ƙarshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.”   Lamarin ya jawo damuwa daga al’umma da shugabannin siyasa, yayin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙoƙari wajen gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi da tabbatar da zaman lafiya a yankin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025 Labarai Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku October 16, 2025 Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025
    Amupitan, wanda ya samu rakiyar gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, da wasu jami’ai zuwa majalisar, ya gabatar da tarihin inda ya yi aiki kafin fara amsa tambayoyin ‘yan majalisar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025
      Hichilema ya kuma jinjinawa kamfanonin Sin, bisa yadda suke inganta darajar albarkatun dake kasarsa ta hanyoyin zuba jari, kana ya godewa Sin bisa yadda ta bude kasuwanninta ga Zambia da ma sauran sassan nahiyar Afirka baki daya. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan October 15, 2025 Daga Birnin Sin Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji  October 15, 2025 Daga Birnin Sin Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia October 15, 2025
    An fara tantancewar da misalin ƙarfe 12:55 na rana, inda ake sa ran Farfesa Amupitan zai gabatar da tarihinsa da kuma amsa tambayoyin da ‘yan majalisar za su yi masa, kafin yanke shawara kan tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban INEC. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025 Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025
    Cikakkun bayanai za su biyo baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025 Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025
    Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce bai dace a ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, laifin rikicin da jam’iyyar PDP ke fama da shi ba. Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce shugabannin PDP ne suka haddasa matsalolinsu, ba Tinubu ko jam’iyyar APC ba. Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a A cewarsa, jam’iyyar PDP “ta mutu tun tuni,” kuma ba ya cikin waɗanda za su nemi farfaɗo da ita. Ya ƙara da cewa yawancin gwamnonin da suka rage a PDP na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki. “Ba daidai...
    Ministan Harkokin Cikin Gida Ya Yi Watsi Da Shelanta Samun Nasara Da Dantakara Isa Bakari Ya Yi Ministan harkokin cikin gidan kasar Kamaru Paul Atanga Nji ya yi watsi da yadda dan takarar shugabancin kasar Isa Tchiroma Bakari ya shelanta kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, ya kuma yi kira ga shugaban kasar Paul Biya da ya amince da shan kaye. Ministan harkokin cikin gidan na kasar Kamaru ya zargi Issa Bakari da cewa yana da wani shiri na kokarin kona kasar Kamaru ta hanyar taimakon kasashen waje. A makon da ya shude ma dai Atanga Nji ya yi gargadi kar wanda ya fitar da sakamakon zaben, domin yin hakan zai zama daidai da cin amanar kasa....
    Game da siyasar Bayelsa, ya ce bai taɓa taka rawa a matsayin uban gidan Diri ba, sai dai kawai yana ba da shawara idan aka nemi ra’ayinsa. Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa naɗa Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC). “A matsayinsa na Farfesa a fannin shari’a kuma SAN na farko da aka naɗa a wannan matsayi, ya fahimci nauyin da ke kansa. Zan goyi bayan tabbatar da naɗinsa,” in ji Dickson. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02% October 15, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP October 15,...
    Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, ya bayyana Jihar Borno a matsayin jiha mafi juriya a Najeriya, yana jaddada gagarumar nasararta wajen shawo kan ƙalubale da dama tsawon shekaru. Yayin wata ziyarar ban-girma da ya kai wa Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Isa Kadafur, a Maiduguri, Ministan ya yaba wa mutanen jihar bisa jajircewarsu da himmarsu wajen fuskantar matsaloli. Wannan ziyara na daga cikin shirye-shiryen taron Kwamitin Kwamishinonin Yada Labarai na jam’iyyar APC. Ya bayyana cewa abubuwan da suka faru a Borno cikin shekaru goma da suka wuce sun nuna jarumtaka da haƙurin mutanen jihar, waɗanda ke ci gaba da ginawa da tafiya gaba duk da matsalolin da suka fuskanta. Ministan ya jaddada cewa ƙarfin gwiwar mutanen Borno abin alfahari...
    Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya fice daga jam’iyyar PDP. Mai magana da yawun gwamnan, Daniel Alabrah, ne ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook na ainihi, kodayake bai bayyana dalilin ficewar gwamnan daga jam’iyyar ba. Har ila yau, bai bayyana ko Gwamna Diri zai koma APC mai mulki ko kuma hadakar ’yan adawa ta ADC ba. Aminiya ta gano cewa Gwamna Diri yana halartar wani taro da mambobin majalisar zartarwa ta jiha, inda ya bayyana musu wannan bayani. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa, Rt. Hon. Abraham Ingobere, yana cikin mahalarta taron. A cikin sa’o’i kaɗan da suka gabata, Gwamna Diri tare da tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, sun halarci bikin ƙaddamar...
    Iran ta kai hari a wani sansanin sojan Isra’ila na sirri da ke karkashin wata hasumiya a Tel Aviv Yankin Gray, wani dandali ne na bincike, ya bayyana samuwar wani maboyar sirri na sojan Isra’ila da ke karkashin wani hasumiya a Tel Aviv, wanda ake kyautata zaton yana cikin wadanda aka kaiwa hari da makami mai linzami na Iran yayin harin da aka kai ranar 13 ga watan Yuni. Bisa binciken da aka gudanar, dandalin ya gano wurin da wani wurin karkashin kasa da aka fi sani da “Site 81”, wani rukunin jami’an leken asiri na hadin gwiwar sojojin Amurka da Isra’ila da ke karkashin rukunin gidaje na Da Vinci a wata unguwa mai yawan jama’a a tsakiyar birnin Tel...
    Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye. Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na ƙuri’u a rumfunan zaɓe da dama. Sun buƙaci Shugaba Paul Biya, wanda ke neman wa’adin mulki na takwas a zaɓen da ya gaggauta miƙa saƙon taya murna ga Issa Bakary Tchiroma. “Muna kira ga shugaban ƙasa mai barin gado da ya gaggauta taya sabon shugaban ƙasa murna,” in ji ƙungiyar,” in ji wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Anicet Ekane da Djeukam Tchameni, suka fitar a...
    Hukumar da ke shirya gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) ta hukunta Kano Pillars FC da tarar Naira miliyan ₦9.5, tare da rage musu maki uku da ƙwallaye uku, bayan magoya bayansu sun kutsa cikin fili a yayin wasan da suka buga da Shooting Stars a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano. Hakan ya sa NPFL ta rufe filin wasan tare da umartar cewa Pillars za ta ci gaba da buga wasanninta na gida a filin Muhammad Dikko a Katsina. A cewar NPFL, hukuncin ya fito ne bisa dokar C1.1, wadda ke hukunta hare-haren da ake kai wa tawagar baƙi da jami’an wasa. Hukumar ta ce wannan mataki yana nufin tabbatar da tsabtace filayen wasa daga tashin hankali da rashin...
    Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Jamhuriyar Kamaru da ake ci gaba da kirgawa ya nuna jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary, ya samu gagarumin rinjaye a yankunan da a bayan Shugaba Paul Biya ya saba rinjaye. Shugaba Paul Biya mai shekaru 92 yana fuskantar abokan hamayya 11 cikin har da tsofaffin mukarrabansa, da ma tsoffin ministocinsa da ke neman kujerarsa da ya shafe shekara 43 a kai kuma yake namen wa’adi na takswas. Cikinsu har da tsohon Ministan Yawon Bude Ido, Bello Bouba Maigari, da tsohon ministan Ayyuka, Bakary, wanda ya yi murabus a watan Yuli domin shiga takara kuma ya sama mafi shahara bayan doka ta haramta wa madugun adawa Maurice Kamto shiga zaben.. Biya ya ki yin tsokaci...
    A hakila, sha’anin yawon shakatawa na fadada hanyoyin samun kudi ga mutanen Xinjiang.   Alkaluman da hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta Xinjiang ta samar sun shaida cewa, a yayin hutun bikin murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a kwanakin baya, yankin ya karbi baki masu yawon shakatawa sama da miliyan 18, adadin da ya karu da kashi 11.26% idan aka kwatanta da na bara, kudin da bakin suka kashe ya kai fiye da Yuan biliyan 25, kwatankwacin dalar Amurka sama da biliyan 3.5, wanda kuma ya karu da kashi 11.71%. Hakan ya nuna cewa, aikin yawon shakatawa na Xinjiang yana da makoma mai kyau.   A watan Mayu na wannan shekara, an fitar da “Shirin raya...
    An wallafa wasu kundi 2 masu kunshe da ra’ayoyin shugaba Xi Jinping na kasar Sin kan batutuwan da suka shafi mata da yara da kungiyar mata ta kasar, da kuma ra’ayoyinsa kan karfafa zumunci da akidu da al’adun iyali, cikin harsunan Rashanci da Faransanci da Spaniyanci da Larabci, bayan irinsu da aka wallafa cikin harsunan Ingilishi.   Madabba’ar tattara bayanai da fassara ta kwamitin tsakiyar JKS ce ta wallafa kundin, wadanda ake sa ran za su taimakawa masu karatu na kasa da kasa kara fahimtar ra’ayoyin shugaba Xi da dabaru da shawarwarin da Sin ta gabatar game da daukaka daidaiton jinsi da raya dukkan harkokin da suka shafi mata a fadin duniya. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin...
    A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau?   A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai...
      ‘Yan sa’o’i kafin sanarwar da Jam’iyyar ta RN ta yi ne dai, tsohon Firaministansa Edouard Philippe ya ce yana goyon bayan shirya sabon zaben shugaban kasa a gaggauce.   Wannan matsin lamba dai kari ne kan wadda shugaban na Faransa ke fusakanta daga bangaren masu sassaucin ra’ayi, wadanda su kuma bukatarsu ita ce a zabi sabon Firaminista daga cikinsu.   Sai dai a iya cewa akwai ragowar fatan kawo karshen rudanin da siyasar Faransar ta shiga, la’akari da bayanan da suka ce a dazu an shiga tattaunawa tsakanin jagoran jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya Bruno Retailleau da Firaminista Lecournu, kwana guda bayan murabus din da ya yi. Yayin da kuma a gefe guda rahotanni suka ce a gobe...
    Ministan gidaje da raya birane da karkara na kasar Sin Ni Hong, ya ce yanayin sashen samar da gidaje na Sin ya kara inganta tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, yayin aiwatar da manufar raya kasa karo na 14, inda jimillar adadin sayar da sabbin gidaje na kasuwa ya kai fadin sakwaya mita biliyan biyar.   Ni Hong, ya bayyana hakan ne a yau Asabar, yayin wani taron manema labarai. A cewarsa, sama da Sinawa miliyan 110 sun amfana daga babban tsarin gyaran tsofaffin gidaje cikin shekarun biyar. Kazalika, tsofaffin gidaje dake unguwanni sama da 240,000 a sassan biranen Sin, sun mori shirin gyaran fuska cikin wa’adin. Don haka gaba daya, yanayin ingancin muhallin biranen Sin ya kara inganta yadda ya...
    Shugaban kasar Cuba miguiel Diaz –canel yayi tir da matakin da kwamitin dake bada kyautar noble a duk shekara ya dauka na bada kyatutar ta wannan shekarar ta 2025 ga dan adawan kasar venuzela maria corina machado inda ya bayyana shi a matsayin abin ban kunya . Matakin na Diaz canel yana nuna irin yanayin zaman tankiya tsakanin gwamnatocin latin Amurka da kuma kasashen yamma , kuma yana nuna cewa rabuwar kawuna kan wanda aka amince shi a matsyin mai inganci a bangaren dimokuradiya  kuma ya haifar da rashin zaman lafiya a yankin. Yana mai cewa babban abin kunya ne ace kyutar Nobel ta zaman lafiya a mika ta ga wadda ta janyo tsoma bakin sojoji a kasarta, Wannan yana...
    Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta.   A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare.   Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da...
    Ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanya takunkumi kan wasu mutane sama da 50 da hukumomi da jiragen ruwa da ake zargi da hannu a cinikin man fetur da Iran. A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, ofishin kula da kadarorin kasashen waje (OFAC) ta kara matsin lamba kan Iran ta hanyar kakaba mata takunkumi ga mutane sama da 50, kamfanoni da jiragen ruwa masu saukaka sayarwa da jigilar danyen mai da iskar gas daga Iran. A cewar hukumomin Amurka, wadannan hanyoyin sun baiwa Iran damar fitar da mai da kayayyakin da suka kai na biliyoyin daloli. Sabon takunkumin ya shafi kamfanoni uku da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, kamfanoni uku na bogi a Hong Kong, da wata matatar mai a China....
    Majalisar magabata a Najeriya ta amince da nada Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga jihar Kogi a matsayin sabon shugaban hukumar zaben kasar INEC. Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce Shugaba Tinubu ne ya gabatar da sunan Farfesa Amupitan ga majalisar domin neman amincewarta. Tinubu ya shaida wa majalisar cewa Farfesa Amupitan ne mutum na farko daga jihar Kogi da zai rike mukamin, kuma ba dan siyasa ba ne. Nan take kuma duka mambobin majalisar suka amince da shi ba tare da sabani ba. A yanzu shugaba Tinubu zai aika sunansa zuwa majalisar dattawan Nigeria domin amincewarta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Farfesa Amupitan, mai shekara 58, malami ne a Jami’ar Jos...
    ‘Yan majalisar dai sun amince da naɗin, inda Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya.   Dangane da kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara), yanzu Shugaba Tinubu zai aika da sunan Amupitan zuwa Majalisar Dattawa don tantancewa.   Amupitan, mai shekaru 58, daga Ayetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, Farfesa ne a fannin shari’a a Jami’ar Jos, Filato, kuma tsohon ɗalibin jami’ar ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta October 9, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin October 9, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso...
    Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban ƙasar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, a ranar Alhamis. “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya gabatar da Amupitan a matsayin wanda zai cike gurbin Shugaban Hukumar INEC, biyo bayan wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu.”
    Mambobin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i ta Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan da ba Malamai ba (NASU) reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK), sun gudanar da zanga-zangar lumana. Mambobin sun yi zanga-zangar ne a ranar Alhamis kan riƙe wasu haƙƙokinsu da suka zargi gwamnatin tarayya da yi. Zanga-zangar da aka gudanar a cikin harabar jami’ar ta biyo bayan umarnin shugabannin ƙasa na ƙungiyoyin biyu, bayan ƙarewar wa’adin mako guda da ƙarin makonni biyu da suka ba gwamnatin tarayya. Masarautar Nafada ta ƙaddamar da dokar rage tsadar aure Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram – UNICEF Da yake jawabi ga manema labarai yayin zanga-zangar, Mataimakin Shugaban SSANU na Ƙasa shiyyar Arewa maso Yamma, Kwamared Sabo Balarabe Wudil, ya ce...
    Lokacin da mai gabatar da shirin, Seun Okinbaloye, ya tambaye shi ko ya damu saboda yawancin ‘yan ƙabilar Ibo na goyon bayan Obi, Kalu ya cd, “A’a, kawai ban son yin magana a kansa.“Idan kana son na tattauna a kan Peter Obi, to ka gayyace mu duka mu biyun mu zauna a tattauna ta awa biyu; kai za ka zauna a tsakiya, shi a gefe ɗaya, ni kuma a ɗaya gefen. Sai mu tattauna.”“Peter Obi ba jagorana ba ne. Ni ne ɗan siyasa mafi shahara daga yankin Kudu maso Gabas. Na taɓa lashe jihohi biyu a ƙarƙashin jam’iyyar PPA, kuma na taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa.“Kuri’u na miliyan 4.9 na samu a shekarar 2007 har yanzu suna nan. Jam’iyyata ta...
    ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025
    ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025
    Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta. Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara. ‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’ Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen. “Mun samu kiran...
    Ya buƙaci jama’a suke bambanta “gaskiya da siyasa.”ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025
     Wannan sanarwar ta baya bayan nan da kasar Sin ta yi, ya samu yabo sosai, musammam daga sakatare janar na MDD, yana jaddada cewa, shirin na Sin na da muhimmanci matuka ga tunkarar sauyin yanayi. Su ma kafafen yada labarai na kasa da kasa da manyan jami’an hukumomi da kasashe da dama, sun yaba wa shirin, wanda ya nuna cewa, ana kara ammana da irin rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin da suka shafi duniya. Ba alkawari da gabatar da shirin kadai take yi ba, ta kasance mai aiwatar da su a aikace kuma ana ganin nasarorin da take samu a zahiri. Zuwa yanzu, babu wata kasa da ta bayar da gudunmuwa a wannan bangare kamar kasar Sin, kuma...
    Kafafen watsa labarun HKI sun nakalto cewa kamfanin jirgin saman kasar Oman, wato “Oman Air” ya cire sunan Isra’ila daga cikin taswirarsa yam aye gurbinta da Falasdinu, domin nunawa domin abinda yake faruwa.  Tashar talbijin din “almayadin’ ce ta nakalto labarin daga kafafen watsa labarun HKI akan matakin na kasar Oman. Ana ganin matakin na Oman a matsayin mayar da martani akan kisan kiyashin da HKI take tafkawa akan al’ummar Falasdinu, musamman a Gaza. A baya ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu, domin kawo karshen laifukan da HKI take tafkawa akan al’ummar Falasdinu, da kuma buke kafar da za a shigar da kayan abinci...
    Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) mai barin gado ya mika ragamar shugabancin hukumar a hukumance ga Misis May Agbamuche-Mbu, wacce za ta zama shugabar riko.Taron ya gudana ne a ranar Talata yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kwamishinonin zabe a hedikwatar INEC da ke Abuja.Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta ArewaMajalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A NijeriyaAgbamuche-Mbu, wacce itace kwamishina mafi dadewa a hukumar zabe ta kasa INEC, za ta ci gaba da kula da harkokin hukumar zabe har sai an nada sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta.Da yake sanar da ajiye aikin, Farfesa...
    ”Dan wasan gaban Bayern Munich Harry Kane ya bayyana cewar zamansa a Bayern Munich ya bude wani sabon Babi a rayuwarsa don haka a shirye yake ya bude tattaunawa da Bayern Munich kan yiwuwar saka hannu akan sabon kwantaragi, Kane ya shafe rabin shekarun kwantiraginsa a Bayern Munich, Kane ya saka hannu akan shekaru hudu da Bayern Munich wadda ta dauko shi daga Tottenham Hotspur kan fan miliyan 86.4 a shekarar 2023.Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin MasarautuTsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan BindigaDan wasan mai shekaru 32, ya zura kwallaye 103 a wasanni 106 da ya buga wa kungiyar...
    Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa.   Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph na National Accord da kuri’u 9 a matsayin shugaban kungiyar.   Ya kuma bayyana cewa Mista Chris Nyamtu na gidan rediyon Najeriya ne ya yi nasara da kuri’u 21 yayin da Augustine Kuza na jaridar Pilot na Najeriya ya samu kuri’u 9 a matsayin Sakatare.   Mista Abel Daniel na jaridar Guardian a matsayin mataimakin shugaba Awayi Kuje na NAN a matsayin Mataimakin Sakatare, Michael...
    A wani bangare na kudirinta na bunkasa tattalin arzikin mata, gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na shirya tarurrukan horaswa kan kula da tsaftar madara, da shirya kayayyaki, da dabarun kiyayewa ga mata masu sayar da madara ko nono a fadin jihar.   Kwamishiniyar harkokin mata da yara da masu bukatu ta musamman Ambasada Amina Abdullahi Sani ta bayyana hakan a wata ziyarar aiki da ta kai kasuwar masu sayar da madarar mata (Nono Sellers) dake kan titin Zaria a Kano.   A cewar kwamishinan, ziyarar na da nufin tantance yanayin da kasuwar ke ciki da kuma lalubo hanyoyin da za a bi don inganta yanayin aiki da kuma sa’o’in na mata masu sana’ar sayar da kayayyaki a can.  ...
    A yayin Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, Uche Nnaji, ke fuskantar matsin lamba bayan ya amsa a gaban kotu cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba, zargin sa da amfani da takardun bogi da kafar PREMIUM TIMES ta bankaɗo ya ƙara ƙarfi. Fadar Shugaban Ƙasa ta ce za ta jira hukuncin kotu kafin ta ɗauki mataki kan batun Nnaji. Wannan ya sanya Mista Nnaji cikin jerin wasu ministoci da suka fuskanci irin wannan tuhuma: – Uche Nnaji Uche Nnaji, wanda Shugaba Bola Tinubu ya nada a watan Yuli 2023, ya gabatar da takardar digiri da kuma takardar kammala aikin NYSC a lokacin tantancewa. Amma jami’ar UNN da hukumar NYSC sun ce ba...
    Wani saksmkon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar dimokuradiyya ta Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Isra’ilawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin Gaza, tare da bayyana hadarin da fursunoni ke fuskanta. Wannan adadi na kashi 66% ya karu da kashi 13% a kan sakamakon da aka fitar a shekara guda da ta gabata lokacin da aka yi musu tambaya iri ɗaya. Sakamakon  ya kuma nuna cewa kashi 45% na Isra’ilawa sun yi imanin cewa ya kamata Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yi murabus nan da nan kafin karshen yakin, tare da dora masa alhakin abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Sakamakon ya nuna...
    Tags: KwaraNPFL ShareTweetSendShare Rabilu Sanusi Bena Related Wasanni Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar 5 hours ago Wasanni Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or 2 days ago Wasanni Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya 2 days ago
      Ya kara da cewa yan shekarun da suka gabata, an yi shakku kan dorewar wasan Hockey a Nijeriya, amma yanzu tawagarmu ta mata ita ce ta zo matsayi na 3 a Afirka, yayin da tawagar maza ke matsayi na 4, wadannan nasarorin sun nuna irin yadda muka himmatu wajen ganin mun kara inganta wannan wasa a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwarzuwar gasr Big Brother Naija (BBNaija) ta wannan shekara, Imisi Eniola Ayanwalwe, ta ce ba ta san yadda za ta kashe Naira miliyan 150 da ta lashe a gasar ba. Imisi Eniola Ayanwale ce ta zama gwarzuwar BBNaija da aka kammala a daren Lahadi ne bayan kwanaki 70 ana fafatawa mai cike da ce-ce-ku-ce da nishaɗi. An sanar da sakamakon tare da karrama ta da kyaututtuka ne a babban bikin ƙarshe da Ebuka Obi-Uchendu ya gabatar, inda Imisi ta doke abokiyar takararta Dede a karshe. Ta tafi da tsabar kuɗi Naira miliyan 80 a matsayin wani ɓangare na kayatattun Naira miliyan 150 da ta lashe a matsayin gwarzuwar BBNaija karo na 10. A bana, masu shirya gasar sun canja tsarin...
    Har ila yau, ya roƙi jama’a da su yi watsi da wannan rahoton ƙaryar kuma su ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen nasarar ayyukan Soji. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ana ta rade-radin an baki sarauta, shin mene ne gaskiyar maganar? Alhamdulillah, maganar an bawa Zahra’u sarauta ba karya ba ne, hakkun haka ne an ba ni sarauta.   Mutane za su so su ji, shin daman Haj. Zahra’u ‘yar Ghana ce, tana da sarauta a Ghana? A’a! Ni ba ‘yar Ghana ba ce, ba abin da na hada da Ghana, sai dai so da yarda, saboda ma’abota kallon finafinan hausa ne. Ni kuma ina cikin wannan masana’anta ta finafinan hausa, musamman Dadin Kowa na Arewa24. Alhamdulillah Arewa24 ta sa sunanmu ya tafi a duniya. Ta yi mana riga ta yi mana wando babu abin da ba ta yi mana ba, domin dalilin fuskanmu da ta tafi ake kaunar mu...
    Turkiyya ta mayar da martani ga shugaban Amurka cewa: Ba za ta daina sayen iskar gas daga kasar Rasha ba Ministan makamashi da albarkatun kasa na kasar Turkiyya Alparslan Bayraktar ya tabbatar a wata hira da yayi da gidan talabijin a jiya alhamis cewa: Kasarsa ba ta da niyyar yin watsi da sayen iskar gas da take daga Rasha. “Ministan a wata zantawa da tashar CNN Turk ya bayyana cewa: Game da Turkiyya ba za ta iya ce wa ‘yan kasarta ku yi hakuri, iskar gas ta kare ba. Ya kara da cewa: “An tabbatar da tsaron iskar gas tana tabbata ne ta  hanyar yin amfani tilas da wadannan hanyoyin, ba tare da nuna bambanci ba a lokacin hunturu mai...
    Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da yanayin ruwa da kasar da ke cikinsu ya kai kashi 73 cikin dari. Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, a yayin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, an kiyaye kyautata yanayin zaizayewar kasa a kasar Sin, kuma an cimma burin rage fadin gonakin da suka gamu da matsalar, da kuma rage illar da ruwa da iska suka haddasa wa gonaki....
    Sarah Mullally ta zama sabuwar Shugabar Cocin Ingila, wato Archbishop ta Canterbury, inda ta kasance mace ta farko da za ta jagoranci Cocin Ingila inda wannan muƙamin ya samo asali tun zamanin Daular Romawa da kuma al’ummar Anglican na duniya. Sarki Charles III ya amince da naɗin Mullaly bayan kwamitin da aka dora wa alhakin nemo wanda zai maye gurbin Justin Welby, wanda ya yi murabus a farkon wannan shekarar saboda wani zargi na cin zarafi, kamar yadda gwamnatin Birtaniya ta sanar a ranar Jumma’a. Cocin Ingila ita ce ta haifi ɗarikar Anglican a duniya. Mullally, mai shekaru 63, ta zama Archbishop ta Canterbury ta 106. A cikin wata sanarwa, tsohuwar ma’aikaciyar jinya ta bayyana cewa ta fahimci “babban nauyi”...
    Wannan al’amari ya nuna yadda ake samun ƙarin rashin jituwa tsakanin shugabancin kamfanin da ƙungiyoyin ƙwadago, duk da cewa matatar ana ganin ta zama muhimmin ginshiƙi wajen cikar burin Nijeriya na cin gashin kai a fannin makamashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Alhamis, kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, layin dogo na kasar Sin ya gudanar da balaguron fasinjoji miliyan 23.13 a jiya Laraba, wato ranar farko ta hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na tsawon kwanaki 8. A cewar kamfanin sufurin jiragen kasan, wannan adadi ya nuna wani sabon tarihi na yawan balaguro da aka samu a rana daya. Kamfanin sufurin jiragen kasan ya yi kiyasin cewa, za a yi tafiye-tafiye miliyan 19.3 a ranar Alhamis, tare da karin jiragen kasa 1,409 da aka samar. Yayin da bikin tsakiyar kaka ya fado lokaci guda tare da ranar kafuwar PRC a wannan shekarar, ana sa ran hutun da ake...
    Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce zai kori dukkanin jami’an diflomasiyar Isra’ila daga ƙasarsa a matsayin martani ga kama jiragen ruwa masu ɗauke da agaji zuwa Gaza. Ya kuma ya bayyana cewa an yi garkuwa da yan Colombia guda biyu. Petro babban mai caccakar yaƙin Isra’ila a Gaza, ya zargi Isra’ila da sake saɓa dokokin ƙasa da kasa inda ya buƙaci sakin su cikin gaggawa. Italiya ta kira kutsen jiragen ruwan da Isra’ila ta yi a matsayin fashin teku da kuma ta’addanci. An dai yi ƙokarin shigar da kayan agaji ne ta hanyar teku domin kaucewa shingen Isra’ila a yankin
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Ismail Falgore, ya mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai.   A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, shugaban majalisar ya bayyana tafiyar Najeriya bayan samun ‘yancin kai a matsayin wanda ke cike da kalubale da dama, yana mai cewa idan aka yi hangen nesa da tsare-tsare, makoma mai haske tana nan kusa.   Ya lura cewa duk da matsaloli, Najeriya a yau tana tsaye a matsayin kasa mai mutane sama da miliyan 230, galibi matasa da kuzarin da ke da karfi na musamman da kasashe da yawa ba su da su.  ...
    Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai.   Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa.   Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da...
    Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago na daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar Marigayi Kyaftin Hassan Mohammed Baro, Kwamishinan dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja.   Sallar jana’izar wadda aka gudanar a kusa da gidan marigayin da ke Minna ta samu halartar babban daraktan kula da harkokin addini Malam Umar Faruk Abdullahi wanda ya samu halartar jama’a da dama da suka hada da mai martaba Sarkin Agaie Alh Yusuf Nuhu.   Gwamnan ya kuma kasance cikin masu jajantawa a makabartar Musulmi ta Kpakungu inda aka yi jana’izar marigayi Captain Baro tare da babban limamin Minna, Malam Jibril Isah ya yi addu’ar Allah ya jikansa.   Daga karshe Umar Bago ya jagoranci tawagar jihar zuwa gidan...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, ta doke Barcelona a wasan mako na 2 na gasar Zakarun Turai a wasan da suka buga a filin wasa na Luis Companys. Ferran Torres ne ya fara jefa ƙwallon a ragar PSG a minti na 19 da fara wasan, amma gab da tafiya hutun rabin lokaci Senny Mayulu ya farkewa baƙin ƙwallonsu, yayin da Goncalo Ramos ya ci ƙwallon ƙarshe kuma wacce ta bai wa PSG nasara a mintin ƙarshe na wasan. Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP, Sun Kama Wasu Da Miyagun Ƙwayoyi Li Qiang Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Sabon Firaministan Algeria Da wannan nasarar da PSG ta samu ya sa ta koma matsayi na 3 a teburin gasar Zakarun Turai yayin...
    A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba.   An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken...
    A yan kwanaki kin nan kasashen duniya sun fuskanci wani lamari mai jan hankali sosai, wanda ya jaddada hakkin falasdinu na kafa kasarsa mai cin gashin kai,  hakika wannan lamari ya kai kololuwasa inda ya kai ga ranar litinin da ta gabata aka kira wani taro a gegen taron majalisar dinkin duniya karo na 80 domin bayyana nuna amincewa da warware rikicin falasdinu na kafa kasashen biyu masu cin gashin kansu, Akwai abubuwa guda buyi masu gayar muhimmancin da suka sanya aka gudanar da taron kafa daula biyu, na farko hakika yazo a yan kwanaki kadan sanar da shimfida taswirar hanya na kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai bisa  iyakoyin da aka cimma a wata yuni shekara ta 67...
    Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Pakistan sun bayyana cewa sun yi gwajin makami mai linzami na fatah 4 da aka kara inganta shi,  wanda zai iya kai hari mai nisan kilomita 750 ba tare da wani kuskure ba, wanda ya kara inganta karfin makamai masu linzami na kasar. Babbar nasarar da aka samu wajen gwajin makamai mai linzami da aka kara inganta shi acikin gida na fatah 4,wanda aka karfafa shi da wani tsari na zamani,  makamin zai iya kaucewa harin makami mai linzami na makiya ta hanyar tsarin rungumar kasa yayin da yake kai hari, Wannan wani bangare ne na karfin sojin kasar kuma da sannu za su kara inganta karfin makami mai linzami na fatah 4,...
    Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane. Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya.   Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli...
    A yau Talata ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wani kundi mai kunshe da matsayin kasar dangane da kudurin MDD mai lamba 2758. Kundin ya bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, da babban rinjaye taron MDD na 26 ya zartar da kuduri mai lamba 2758, wanda a cikinsa aka fayyace mayar da dukkanin hakkoki ga janhuriyar jama’ar kasar Sin, da amincewa da wakilan janhuriyar jama’ar kasar Sin a matsayin wakilan kasar Sin kadai a hukumomin MDD. Wannan kundi ya kuma fayyace komai dalla-dalla, tare da warware batun wakilcin Sin, ciki har da batun yankin Taiwan, a dandalin MDD a mahanga ta siyasa, da shari’a, da matakan aiwatarwa. Kuma tabbas halasci, da inganci, da...
    Wata kotu a Jihar Florida da ke ƙasar Amurka ta aike da wani mutum Craig Vogt mai shekaru 61 gidan waƙafi, bayan samunsa da laifin yanka tsuntsayen Dawisu guda biyu, sannan ya yi dabge da naman su. Hukumomin Hudson, wani yanki da ke Florida, sun cafke mutumin ne bayan an samu rahoton abin da ya aikata, wanda ya ta da hankalin maƙwabta da ya shaida musu cewa ya yanka tsuntsayen kuma ya soya har ya ɗebi dabgen. An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin ya amince da laifinsa, yana mai cewa ya aikata hakan ne saboda ɓacin ran...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa  Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai bayyana cewa a matsayin babban rashi a ƙasar da kuma fagen aikin jarida. ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa, marigayiyar ta rasu ne bayan wani farmaki da ’yan fashi suka kai gidanta da ke Katampe a Abuja, a ranar Litinin da ta gabata. Tinubu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Amurka ta kawo cikas ga yarjejeniya tsakanin Iran da Turai game da batun yin watsi da dawo da takunkumi kan Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: An cimma yarjejeniya da kasashen turai dangane da yadda za’a yi watsi da batun sake dawo da takunkumi kan Iran, amma bangaren Amurka ya kawo cikas ga wannan yarjejeniya. A lokacin da ya iso filin jirgin saman Mehrabad na Iran daga birnin New York, shugaba Pezeshkian ya yi tsokaci kan ganawarsa da wasu shugabannin kasashen Turai da suka yi da ba a taba gani ba, yana mai cewa, “A birnin New York, sun tattauna da Turawa kan batutuwan da suka jibanci lamarin makamashin nukiliyar Iran,...
    Jami’ar Bayero Kano (BUK) da ke Kano ta sanar da korar ɗalibai 57 saboda kama su da laifuka masu nasaba da maguɗin jarrabawa. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da darektan sashen kula da harkokin jarrabawa na jami’ar, Malam Aminu Wada Kurawa ya fitar. Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki ‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuros Riba Sanarwar ta ce an dakatar da wasu ƙarin mutum 8 da aka kama da laifuka masu nasaba da hakan tare da wanke ƙarin ɗalibai biyu daga zargin. Jami’ar ta ce bincike ya tabbatar da cewa ɗaliban da aka kora sun aikata laifuka daban-daban da suka shafi karya ƙa’idojin jarrabawa. Cikin wadanda...
    Firaministan Nijar Mahaman Lamine Zein ya yi Allah wadai da yadda kasashen ketare ke da hannu wajen tada zaune tsaye a yankin Sahel. Lamine Zein, ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar da a zauren babban taron MDD karo na 80 dake gudana a birnin New York. Nijar ta kuma yi Allah wadai da kisan kiyashin Isra’ila a Gaza, da kuma hare haren Isra’ilar kan Iran da Qatar, da kuma yadda ake nuna halin ko in kula game da rikicin Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo da Sudan dama yankin Sahel tare da hadin bakin wasu manyan kasashen yamma a nahiyar Afrika. Fira ministan na Nijar, Ya kuma kara da cewa gwamnatin Nijar da takwarorinta na Burkina da Mali, a sun sha...
    Maude dan shekara 40, kwararren lauya ne, kuma haziki wanda ya kammala karatun digiri a fannin shari’a daga babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.   Shi mamba ne a kungiyar lauyoyin Nijeriya da kuma a Cibiyar Masu sasantawa ta Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da yammacin yau Asabar ne manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa Real Madrid da takwararta Athletico Madrid suka fafata wasan mako na 7 a gasar Laliga ta bana a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid. Normand na Athletico ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Madrid kafin Mbappe ya farke a minti na 25, a minti na 36 Arder Guler ya sake jefa ƙwallo a ragar Athletico kafin Sorloth ya farke ƙwallon dab da tafiya hutun rabin lokaci. Tawagar Gwamnatin Tsakiya Na Ci Gaba Da Ziyartar Jami’ai Da Mazauna Yankuna Da Dama Na Jihar Xinjiang Masana Sun Dora Alhakin Rashin Cika Alkawuran ‘Yan Siyasa Kan Jam’iyyu Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Julian Alvarez ya ci ƙwallaye biyu a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an ’yan sanda a Jihar Ondo sun kuɓutar da wata yarinya ’yar shekara huɗu da ta ɓace tare da gano wasu masu fataucin yara da ke gudanar da ayyukan su a yankunan Jihohin Ondo, Delta da Anambra. An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Sunday Kingsley da ke yankin Alagbaka Extension a garin Akure, ya ruwaito cewa ’yarsa Jesinta, ta ɓace ne a lokacin da take tare da mahaifiyarta Sunday Happiness. Gwamnatin Kebbi ta sake jaddada goyon bayanta ga hukumomin tsaro Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Olusola Ayanlade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka sanarwa manema labarai a Akure ranar...
    Sai kuma fannin fadada dazuzzuka da zai karu zuwa sama da kyubik mita biliyan 24, da mayar da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi kan gaba, cikin jimillar ababen hawa da kasar za ta rika sayarwa, da fadada kasuwar carbon ta kasar Sin, ta yadda za ta game dukkanin manyan sassan fitar da hayakin carbon, tare da kafa al’umma mai ingancin rayuwa yayin da ake tunkarar sauyin yanayi. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wani samame na kwanaki hudu na hadin gwiwa na yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula a kan tituna, rundunar hadin guiwa mai wanzar da zaman lafiya da farfado da matasa ta jihar Kano, ta kama wasu mutane 78 da ake zargi a manyan wuraren da ke jihar.     A wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA a Kano Sadiq Mohammad Maigatari ya fitar, ya ce rundunar ta yi aiki tare da hadin gwiwar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya.     Wannan farmakin dai ya shafi fitattun wuraren da ake aikata miyagun laifuka da suka hada da Mariri Yan’itace, Fagge, Badawa,...
    Da yake magana a gaban babban zauren majalisar dinkin duniya Yarima mai jiran gado na kasar Kuwait shaikh sabah khalid al-hamad Al-sabah ya bayyana yanayin da ake ciki a yankin gaza a matsayin babban bala’I, yace alumma faladinu da basu da wani mai basu kariya suna fuskantar wahalhalu mafi muni a tarihi. Har ila yau  ya kara da cewa abin da ke faruwa a Gaza kisan kare dangi ne,da kuma share kabilu, don haka wannan ba zai tafi da yin shiru ba, kana ya yi tir da harin da HKI takai kan kasar Qatar kuma yayi barazanar cewa kai hari kan daya daga cikin mambobin kungiyar hadin kan kasashen larabawa, kamar kai hari ne akan dukkansu baki daya, Yarima yayi...
    A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa da ya yi hobbasar gina Xinjiang na zamani mai ra’ayin gurguzu da ke kunshe da hadin kai, da kwanciyar hankali, da samun wadata, da arziki mai albarka, da raya al’adu da kyautata muhallin halittu, inda jama’a za su ci gaba da rayuwa da aiki cikin zaman lafiya da samun wadata. Yayin da yake sauraren rahoton ayyukan kwamitin jam’iyyar JKS a yankin Xinjiang da gwamnatin yankin a yau 24 ga wata, shugaba Xi ya jaddada cewa, wajibi ne a kafa tubalin samar da albarkatu da masana’antu, da yin nazari sosai a game da turbar samar da ci gaba mai inganci da ta dace...
    Yayin da ake cika shekaru 70 da kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa a bana, CGTN ta gudanar da wani bincike na kuri’ar jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,446 daga kasashe 38. Sakamakon binciken ya nuna cewa masu bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da nasarorin da aka samu a ci gaban tattalin arziki da zamantakewar yankin na Xinjiang. An amince sosai da cewa, tsarin gudanar da mulkin Xinjiang da kasar Sin ta yi amfani da shi ya gano hanyar da ta dace wajen daidaita ci gaba da bangaren tsaro a yankunan kan iyaka, da kara kaimi ga amfani da zamanantarwar kasar Sin a yankin Xinjiang, da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce a matsayin Sin na babbar kasa mai tasowa dake sauke nauyin dake wuyanta, ba za ta nemi wani sabon matsayi na musamman, ko fifiko yayin tattaunawar cimma matsaya ta yanzu, da ma ta nan gaba, dangane da harkokin kungiyar cinikayya ta duniya WTO. Li, ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manyan jami’ai dangane da shawarar nan ta tsarin shugabanci da Sin ta gabatar, a gefen babban taron MDD karo na 80 dake gudana yanzu haka. A yau Laraba, ma’aikatar cinikayya ta Sin ta kira taron manema labarai, inda mataimakin ministan cinikayya na Sin Li Chenggang, ya bayyana wannan muhimmiyar matsaya ta Sin, a matsayin alkawari dake mayar da hankali ga yanayi da...
    Babban magatakardar malajisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Batun sake kakabawa Iran takunkumi yana nuni da gajiyawar kasashen turai. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din al’mayadin’ta yi hira da shi, ya kara da cewa, matakin da kasashe uku na Faransa, Birtaniya da Jamus, su ka dauka akan batun sake kakabawa Iran takunkumi, yana sake yin  nuni ne da tsohuwar gabar da kasashen turai da Amurka suke da ita akan al’ummar Iran. Haka nan kuma ya ce wannan tsohuwar gaba ta yi tasiri mai girma a cikin siyasar mulkin mallaka ta kasashen turai da yadda suke son Dannen sauran kasashe. Dr. Ali Larijani ya kuma ce, wanann irin kiyayya da siyasa tana cin karo...
    Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
    A ranar Alhamis 25 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wani babban taro a birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa, domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar yankin. An shirya fara bikin da shugaba Xi zai halarta da karfe 10:30 na safiyar Alhamis, kuma babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da dandalin shafin intanet na kamfanin dillancin labarai na kasar Sin (Xinhuanet) za su watsa shi kai-tsaye. (Abdulrazaq Yahuza Jere)     Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, tambayoyi a kan harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Jihar Kebbi. An gudanar da tambayoyin ne a ofishin hukumar na Birnin Kebbi a ranar Litinin, inda Malami ya bayyana cewa an yi masa tambayoyin cikin ƙwarewa da mutuntawa. A ranar 1 ga Satumba, 2025 ne aka kai wa ayarin motocin da ke rakiyar Malami hari a Birnin Kebbi, bayan ya dawo daga gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Babban Limamin Masallacin Dakta Bello Haliru Jumu’a. Shaidu sun bayyana cewa an lalata motocin rakiyarsa kusan guda 10, sannan da dama daga cikin magoya bayansa sun jikkata. Burkina Faso, Mali da Nijar...
    Rahotanni sun bayyana cewa kimanin kaso 8% na mambobin majalisar dinkin diniya ne suka sanar da amincewarsu da kasar falasdinu, a daidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da kisan kare dangi a Gaza kuma take kara fadada  mamaye yankuna  a gabar yammacin kogin jodan. Kasaashen faransa, luxambourg , malta da manako ne suka sanar da amincewa da yankin falasdinu a matsayin kasar a wajen taron babban zauren majalisar dinkin duniya,  prime ministan kasar kanada marka caney ya fadi cewa amincewar tana da muhimmanci sosai, kana yayi gargadin cewa an shafe batun yancin cin gashin kai ga yankin falasdinu. Sai dai duk da amincewa da yankin na falasdinu a matsayin kasa, amma ta’addancin da Isra’ila ke yi a yankin gaza...
    Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na  bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
    Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na  bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?. To, sai na ji ban ji daɗi ba a lokacin, dan akwai gidajen TƁ da suka karɓa suke haskawa, nayi sauri na hana a haska ɗin. Sai kuma wani...
      A cewar Atiku, wannan kalmomi (ƙabilanci da yanki) an tanade su ne don raba kan jama’a da nufin cimma burinsu na siyasa ta hanyar roƙon ’yan ƙabilarsu da kada su zaɓi wani ɗan takara wanda ya fito daga wata ƙabila’ maimakon tantance shi da kyawawan halayensa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa ta gayyata domin halartar taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah wanda za yi a ranar 27 ga watan nan na Satumba. Tunawa da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah da sauran wadanda su ka yi shahada a lokacin, kamar su Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin, zai kasance a wani gagarumin taro a birnin Beirut da kuma sauran garuruwan Lebanon  a ranar 27 ga watan Satumba da misalin karfe: 4;30. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Hamas...
    Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Matatar Man Fetur na Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa tun bayan fara samar da man fetur a shekara guda da ta gabata, matsalar dogon layin man fetur da ta shafe shekara 50 ana fama da ita ta zama tarihi. A lokacin wani taron bita da aka gudanar don murnar cika shekara ɗaya tun bayan ƙaddamar da samar da man fetur daga masana’antar dake samar da ganga 650,000 a kowace rana, Dangote ya jaddada cewa Ƴan Nijeriya sun sha fama da dogon layin mai tun daga 1975, amma wannan matsala ta fara zuwa karshe tun lokacin da masana’antar ta fara aiki a ranar 3 ga Satumba, 2024. Dangote ya yi nuni da kalubale...