Togo: An Yi Kiran Sake Yin Wata Sabuwar Zanga-zanagr Kin Jinin Gwamnati
Published: 6th, July 2025 GMT
Kungiyoyi farar da jam’iyyun adawar siyasa a kasar Togo, sun sake yin kira da a gudanar da Zanga-zanga a ranar 16 da 17 ga watan nan na Yuli da ake ciki.
Masu Zanga-zangar dai suna son nuna kin amincewa ne da siyasar hukumar kasar da suke bayyanawa da ta kama-karya, haka nan kuma kashe wasu mutane da aka yi a Zanga-zangar da ta gabata.
Bugu da kari, kiran a yi zanga-zangar dai ya zo ne bayan kama wasu ‘yan hamayyar siyasa da aka yi da kuam kara kudin wutar lantarki, da amince da sabon tsarin mulki da ya kara bai wa shugaban kasar Faure Gnassingbe karfin iko.
Wasu fitattun masu fafutuka a kasar, sun watsa sanarwa a shafukan sada zumunta da a cikin suke yin kiran mutane su fito domin yin Zanga-zangar ta wannan watan na Yuli.
Zanga-zangar karshe da aka yi a kasar, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 kamar yadda majiyar masu fafutukar ta ambata, sai dai kuma mahukuntan kasar sun ce, mutane biyu ne kadai su ka rasa rayukansu, kuma nustewa su ka yi a ruwa.
Har ila yau majiyar ‘yan hamayyar ta ce, an kame mutane da adadinsu ya kai 60 a yayin waccan Zanga-zangar.
A ranar 17 ga watan Yuli ne ake sa ran yin zaben kananan hukumomi, da jam’iyyun hamayya suke yin kira da a dage zaben zuwa wani lokaci a can gaba, har yanyin siyasar kasar ya bayar da dama.
A gefe daya, jam’iyyar da take Mulki a kasar ta dage taron da ta shirya yi a wannan Asabar din mai zuwa domin nuna goyon bayanta ga shugaban kasa, ba tare da bayyana dalilin yin hakan ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakato.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta?
Yan Najeriya da dama na ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan sabon hadakar ‘yan siyasa zuwa sabuwar jami’yyar ADC.
A yayin da wasu ke ganin wannan hadaka za ta cire musu kitse daga wuta, wasu kuwa gani suke yi duk kanwar ja ce.
A ranar laraban nan ne dai gaggan ‘yan siyasa daga jamiyyu daban daban suka hadu don dinkewa wuri daya da niyyar kalubalantar jamiyya mai mulki ta APC, a cewar su za su ceto Najeriya daga halin da jamiyyar ta jefa su a ciki.
NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke HaifarwaShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan ko sabuwar hadakar jamiyyar ADC za ta fidda ‘yan Najeriya daga matsalar da suka ce suna ciki?
Domin sauke shirin, latsa nan