Aminiya:
2025-10-16@14:41:27 GMT

Za a kafa kamfanin ƙera kayan sola a Kano

Published: 16th, October 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za a fara ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki daga hasken ranar a jihar.

Hakan a cewar gwamnatin ya biyo bayan samun masu zuba jari a fannin na makamashi, bayan rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanoni biyu da suka shahara a fannin, wato Tricell Solar Solutions da IRS Green Energy.

.

’Yan sanda sun kama gungun masu fashi a kan hanyar Katsina zuwa Kano Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose

An kulla yarjejeniyar ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA) domin bayar da shawarwari na fasaha da daidaita ayyuka, a yayin taron Sabunta Makamashi na Najeria (NERIF) na 2025 da aka gudanar a ranar Talata a birnin Abuja, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana.

Ya ce shugaban hukumar Zuba Jari ta jihar (Kan-Invest), Naziru Halliru ne ya jagoranci ƙulla yarjejeniyar a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sansusi ya ce ƙulla yarjejeniyar na cikin manyan matakai da gwamnatin ke ɗauka domin faɗaɗa samar da makamashi mai tsafta da araha, bunƙasa masana’antu a cikin gida, da samar da ayyukan yi ga al’ummar jihar.

Sanarwar ta kuma ce a karkashin wannan tsarin, kamfanin IRS Green Energy zai gina masana’antar kera kayan amfani da hasken rana da ke da ƙarfin samar da 600MW a shekara, yayin da Tricell Solar Solutions zai kafa wata da ke da ƙarfin 500MW, lamarin da ya ce zai mayar da Kano cibiyar samar da sabon makamashi a yankin.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Kano Na Aikin Gyaran Cibiyoyin Lafiya Da Za Su Yi Gogayya Da Na Ƙasashen Duniya

Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya kai ziyarar ba-zata ta duba aiki a Asibitin karbar Haihuwa na Imamu Wali, na Marmara, da kuma Asibitin Sabon Bakin Zuwo.

Ya kai ziyarar ce domin tabbar bin umarnin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na wucin gadi wajen sauya wuraren gudanar da ayyukan karbar haihuwa da na yara zuwa wasu cibiyoyi daban.

A karkashin wannan umarni, an mayar da sashen haihuwa na Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase zuwa Asibitin Haihuwa na Imamu Wali, yayin da aka mayar da ayyukan yara kyauta da ake yi a Asibitin Yara na Hasiya Bayero zuwa Asibitin Haihuwa na Marmara.

Wadannan canje-canjen sun biyo bayan ci gaba da gyare-gyare da sabunta wadannan asibitoci, wani muhimmin bangare na hangen nesa na Gwamna Yusuf wajen inganta cibiyoyin lafiya a Kano zuwa matakin kasashen duniya da suka ci gaba.

Domin tabbatar da ci gaba da bayar da ayyuka ba tare da tangarda ba, ma’aikatan sassan da abin ya shafa suma an tura su zuwa sabbin wuraren da aka kebe musu.

Yayin ziyarar, Dakta Nagoda tare da daraktoci da ma’aikatan hukumar, ya jaddada muhimmancin bin umarnin gwamnati yadda ya kamata, tare da yabawa shugabanci da ma’aikatan asibitocin da aka ziyarta saboda hadin kai da jajircewarsu.

Ya kara tabbatar da kudirin hukumar wajen tabbatar da cewa bayar da ayyukan lafiya a Jihar Kano zai ci gaba da kasancewa cikin sauki, da inganci, tare da mayar da hankali kan marasa lafiya, duk da gyare-gyaren da ake yi.

 

Daga Khadijah Aliyu

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, Isra’ila ta kashe Falasdinawa 3 a Gaza
  • Hukumar Kula Da GIdajen Gyaran Hali A Zamfara Ta Neman Shigarda Fursunoni Tsarin Inshorar Lafiya Na NHIS
  • An Bukaci Manoman Kano Su Shiga Baje Kolin Kayan Noma Na Kasa
  • Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi
  • Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF
  • Jihar Kano Na Aikin Gyaran Cibiyoyin Lafiya Da Za Su Yi Gogayya Da Na Ƙasashen Duniya
  • Kudurorin Kafa Hukumomi 3 Sun Tsallake Karatu Na 2 A Majalisar Dokokin Jihar Jigawa
  • Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya
  • Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph