Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da lafiyar mutanen Mafa, mahaifar sa.

Gwamnan dai a wasu ziyarce-ziyarcen da ya kai har sau biyu, ya ware ta, ya kuma yaba wa sadaukarwar da ta yi, tare da yaba mata kan yadda ta tsaya tare da jama’arsa duk kuwa it aba ‘yar asalin yankin ba ne.

Kyautar kwazo da rikon amana da ta samu ya zo ne a lokacin da Gwamna Zulum, wanda ya yi fice wajen bayar da lada ga ƙwazo, ya haɗa da Mrs Duaka a cikin malamai 72 da ma’aikatan lafiya da suka samu gidajen kwana a wani biki da aka ƙaddamar a garin Mafa.

Yayin gabatar da makullan, gwamnan ya kuma sanar da ɗaukar aiki kai tsaye ga ɗanta Anthony, wanda ya kammala karatun Harkokin Banki, a Jami’ar Kashim Ibrahim ta jihar.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa Mrs Duaka ta shafe sama da shekaru ashirin tana aiki a cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Mafa, kuma ba ta bar garin ba, ko da lokacin da ake fama da rikicin Boko Haram. Da yake ƙarin godiya, gwamnan ya bayyana cewa ta yi aiki a Mafa sama da shekaru 24 ba tare da barin garin ba na tsawon wata guda. A lokacin rikicin, lokacin da mafi yawan mutane suka gudu, ta zauna tana kula da al’ummar garin ciki har da mahaifiyarsa.

Mrs Duaka na da aure da ‘ya’ya 4.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello October 25, 2025 Tattalin Arziki Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria October 25, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Shekarar 2025

এছাড়াও পড়ুন:

Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Wani  Hatsari a Neja

Wani jirgin Sojin saman Najeriya ya yi haɗari jim kaɗan bayan tashi daga sansanin Sojin ƙasar da ke Kainji a jihar Neja, sakamakon tangarɗar inji.

Kakakin rundunar sojin saman na Najeriya Ehimen Ejodame lokacin da yake tabbatar da faruwar haɗarin ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa sanadiyyar wannan haɗari, sai dai fasinjan da ke cikin jirgin yanzu haka suna karɓar kulawar gaggawa a asibiti.

Tuni dai aka jiyo hafson sojin saman Najeriyar Air Marshal Sunday Aneke, na yabawa matuƙan jirgin wanda ya bayyana da jajirtattu, da ya ce ƙwarewa da jarumtarsu ce ta tseretar da asarar rayuka a haɗarin.

Jiragen sojin Najeriya a lokuta da dama na gamuwa da haɗari wanda ke kaiwa ga asarar ɗimbin rayuka kama daga na sojojin da kuma fararen hula, dai dai lokacin da ƙasar ke buƙatar agajin sojojin na sama wajen yaƙi da matsalolin tsaron da suka dabaibaye ƙasar.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Wani  Hatsari a Neja