ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD October 25, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15 October 25, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC October 25, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia, Mohammed Haliru Arabo, na tsawon wata uku, kan rikicin shugabanci.

Shugaban Majalisar, Danladi Jatau, ne ya sanar da hakan a ranar Talata a Lafia, bayan Shugaban Kwamitin Majalisar kan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Musa Ibrahim Abubakar, ya gabatar da korafi kan rikicin mulki da ke faruwa a karamar hukumar.

Jatau ya ce matakin ya zama dole domin ba da damar gudanar da bincike kan yadda ake tafiyar da mulkin karamar hukumar, wanda ya ce yana shafar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Ya bayyana cewa dakatarwar ta yi daidai da sashe na 7 da na 128 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima, wanda ya ba majalisa ikon sanya ido kan harkokin mulki.

Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashenta Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato

A cewarsa: “Domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Lafia, dole ne mu gudanar da bincike kan abin da ke faruwa. Bisa ikon da kundin tsarin mulki ya ba mu, shugaban karamar hukumar Lafia ya dakata na tsawon wata uku. Za a ci gaba da gudanar da harkokin karamar hukumar har sai an kammala bincike.”

Kwamitin harkokin kananan hukumomi da masarautu ya samu umarni da ya gudanar da binciken cikin wannan lokaci. A yayin dakatarwar, mataimakin shugaban karamar hukumar, Uba Arikya, zai rike ragamar mulki.

Tun da farko, Musa Ibrahim Abubakar ya gabatar da kudiri a matsayin gaggawa, inda ya nuna damuwa kan yadda aka dakatar da shugaban karamar hukumar na tsawon wata shida ba tare da bin ka’ida ba. Ya ce hakan ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma yana haifar da rashin tabbas a siyasar yankin.

Ya jaddada bukatar majalisar jihar ta shiga tsakani domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin kudi da mulkin karamar hukumar.

Kwamitin ya kuma bukaci majalisar ta yi nazari sosai kan lamarin domin kawo karshen rashin tabbas da rikicin da ya kunno kai a Lafia.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yaba Ma Iyaye Bisa Goyon Bayansu ga Shirin Rigakafin Shan Inna a Karamar Hukumar Ringim
  • Za a Yi wa Yara 194,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Karamar Hukumar Birnin Kudu
  • An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia
  • Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashenta
  • Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba
  • Majid Majidi Na Iran Ya Sami Kyauyar Girmamawa Daga Cibiyar Fina-finai Na “Eurasia Dake Kasar Rasha
  • Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa
  • Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
  • Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya
  • Iran Ta Zama Zakaran  Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21