2025-12-11@08:13:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2888

«yankin Yammacin Kogin Jordan»:

    Jakadan kasar iran na din din din a majalisar dinkin duniya Amir saeid iravani ya jaddada matsayin Tehran na ganin ta hana kisan kare dangi, kuma tayi tir da kisan kare dangi da HKI ta yi a yankin Gaza, kuma ya fadi hakan ne a wajen taron koli karo na 10 na majalisar dinkin duniya kan  ranar tunawa da wadanda kisan kiyashi ya shafa a duniya. Iran tayi amfani da wannan babban taron wajen nunawa majalisar dinkin duniya gazawarta wajen kasa dakatar da kisan kare dangi kan alummar falasdinu a gaza, don haka tayi kira ga kasashen dake mambobi a majalisar dinkin duniya da su dauki mataken da suka dace wajen aiki da doka don sauke nauyin da ya rata...
    Jami’ai sun ce mutane sama da dubu 500 ne kawo yanzu aka tursasawa barin muhallansu a Thailand da kuma Cambodia a yayin da rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari. Rundunar sojin Thailand ta ce Cambodia ta harba mata dubban makaman roka tun bayan da suka soma rikici da juna. Dubban mutane ne suke guduwa domin tserewa lugudan makaman roka da ake harbawa daga Cambodia. Kazalika Thailand ma na ci gaba da kai wa Cambodia hare-hare ta sama. Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana kyautata tsammanin zai gana da  shugabannin kasashen biyu ta wayar tarho, wanda ya matsa musu lamba aka cimma kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yulin da ya gabata. To sai dai ministan...
    Taron kasa da kasa na musamman wanda aka gudanar a wata Jami’a a nan Tehran dangane da nasarar da JMI ta samu kan HKI da Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan yulin da ya gabata ya jawo hankalin kasashen duniya da dama, sannan ya sauya yadda ake daukar HKI a yankin, musaman a matsayin kasa wacce ta fi ko wace kasa karfi soji a yankin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa masu halattan taron sun bayyana muhimmancin wannan nasarar karkashin jagorancin Jagoran Juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae a matsayin babban sauyi a yankin gabas ta tsakiya da kuma duniya gaba daya. Labarin ya bayyana cewa yan siyasa da sauran mahalatta taron...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan kare dangi ga Najeriya. Ko wannan ziyarar da tawagar Amurka ta kawo zai kawo karshen matsalar tsaron da Najeriya ke ciki? NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Jaridar Daily Trust da gidan talabijin na Trust TV, dukkansu mallakar kamfanin Media Trust, a bana ma sun sake yin fice bayan ’yan jaridansu suka lashe kyautar binciken kwakwaf ta Wole Soyinka ta bana. ’Yan jaridar na Daily Trust da Trust TV, Afeez Hanafi da Muslim Muhammad Yusuf, sun lashe gasar ne a matsayin zakaru a rukunin rahoton jarida da kuma na talabijin mafi daraja a bana a Najeriya. Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato Hanafi ya lashe rukuni na rubutu bisa labarinsa mai taken: “Bincike: Dan jarida ya samu ayyuka biyu da takardun bogi na Oluwole.” Wanda ya zo na biyu...
    Kananan yara sama da 93,200 ne ake sa ran yiwa allurar rigakafin cutar shan Inna da ake gudanarwa a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Kazalika, kananan yara sama da 53,800 ne ake sa ran digawa sinadarin vitamin A a yankin. Shugaban hukumar lafiya matakin farko na yankin Aminu Abubakar Kwandiko ya yaba da yadda iyaye ke bada hadin kai da goyan baya ga shirin. Ya kuma ja hankalin ma’aikatan rigakafin da su sanya kishi da kwazo wajen samun nasarar aikin. A sakon da ya aike da shi a taron tattara bayanan aikin rigakafi na yankin, Shugaban Karamar Hukumar, Mallam Badamasi Garba Dabi ya jaddada kudirin Karamar Hukumar na ci gaba da bada gudunmuwa wajen samun nasarar shirin rigakafin.  ...
    Kungiyar ‘yan jarida marar iyaka ta RSF, ta fitar da rahoton na shekara shekara wanda a cikinsa ta bayyana cewa, ‘yan jarida 67 suka rasa rayukansu a lokacin da suke bakin aiki ko kuma sakamakon aikinsu a duk duniya, Saidai a cewar rahoton kusan rabinsu sun mutu a Zirin Gaza, “a lokacin da sojojin Isra’ila suka bude musu wuta. A cewar rahoton na 2025, “Yawan ‘yan jarida da aka kashe (daga 1 ga Disamba, 2024, zuwa 1 ga Disamba, 2025) ya sake karuwa, saboda laifukan da sojoji masu dauke da makamai na yau da kullun da kuma laifukan da aka tsara.” Kungiyar ta kuma bayar da rahoton ‘yan jarida 135 da suka ɓace, wasu fiye da shekaru 30, da kuma...
    Ana taro kan yadda manzon Allah mohammad dan Abdullahi (a) ya zauna da wadanda ba musulmi ba a rayuwarsa a Madina. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto hukuma mai kula da al-adu da kuma al-amuran addinin Musulunci a nan Iran tana cewa ana gudanar da wannan taron ne a dai dai lokacinda aka fara bukukuwan cika shekaru 1500 na hijirar manzon Allah (s). Labarin ya kara da cewa an sabi baki wadanda suka gabatar da jawabi masu muhimmanci daga kasashen Iran, Lebanon da kuma Masar. Ahmad Mobaleghi na mamba a kwamitin al-amuran addini na hukumar ya kawo ayoyin al-kur’ani wadanda suka yi mgana kan yadda manzon Allah yayi mu’amala da yahudawan da ya samu a Madina, kuma...
    Kakakin rundunar sama ta tarayyar Najeriya, wato ‘Nagerian Air Force’ Ehiment Ejodame ya bayyana cewa jirgin wani jirgin saman rundunar dauke da mutane 11 ya yi saukan gaggawa a kasar Burkina Faso a ranr litinin da ya gabata. Jiridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Ejodame yana fadar haka a yau Talata ya kuma kara da cewa kungiyar kasashen AES sun tilastawa jirgin sauka a Bobo Dioulasso na Burkina Faso bayan zargin cewa jirgin ya keta hurumin sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba. A halin yanzu dai ana saran za’a warware matsalar da ke tsakanin kasashen biyu sannan jirgin zai kama hanyarsa zuwa kasar Portigal kamar yadda aka tsara. Labarin ya kara da cewa, jirgin ya tashi daga...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna cin wasu tsirrai, ganye, ko ababen da ke dauke da sinadarai masu haɗari, waɗanda daga baya suke taruwa a jikinsu har su zama guba ga mutum idan aka ci su.   Wasu lokuta ma waɗannan gubobi ba daga abincin dabbar suke fitowa ba, sai dai daga sinadarai da ake amfani da su wajen kiwon su kamar magungunan kiwo, sinadaran rigakafi, ko ma gurɓatattun ruwa da...
    Daga Nasir Malali An kashe ’yan bindiga guda goma sha takwas a wani samame da Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta kai a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto. A wata hira ta wayar tarho, wani shaida daga yankin, Malam Aminu Muhammad, ya shaida wa Rediyon Najeriya a Sokoto cewa, nasarar samamen ta fara ne bayan rundunar ta samu bayanin cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako a kan hanyar Tarah zuwa Karawa a Sabon Birni. Sojojin sun garzaya cikin gaggawa bayan jin harbe-harbe, inda suka kusan awa guda suna musayar wuta da maharan. Shaidan gani da idon ya ce sojojin sun ...
    Wakiliyar musamman ta majalisar dinkin duniya kan yankin falasdinu da aka mamaye  Francesca Albanese ya bayyana irin halin da ake ciki a yankunan falasdinu da isra’ila ta mamaye a matsayin babban bala’I, ta ce kuma shi ne kisan kare dangi na farko da ya tada hankali duniya sosai. Da take bayani wajen rufe taron da aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a jiya lahadi ta bayyana cewa kusan komai ya lalace a yankin, wanda hakan ke nuna kusan rushewar harkokin siyasa da tarbiyar alumma, Wannan ba shi ne kisan kare dangi na farko a tarihin dan Adam ba, wannan shi ne kusan karo na 3 na kisan kare dangi idan bai zama na 4 ko na 5 ba...
    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan kubutar da yan makaranta 100 daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka sace a wata makaranta a jihar Naija a cikin watan Nuwamban da ya gabatata. Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa jami’an tsaron kasar sun sami nasarar kubutar da yan makaranta har 100 daga cikin wadanda yan ta’adda suka sacesu a wata makarantar cocin Khatolica a cikin jihar Naija. Kafin haka an ce yara kimani 50 sun tsere daga hannun yan ta’addan bayan an sacesu. Tashar talabijin ta ‘Chennel TV ‘ ta bada labarin cewa sakin yan makarantan, amma bata nuna hotunansu ba kuma bata yi wani karin bayani ba. Sannan kungiyar kiristoci ta Najeriya...
    Daga Bello Wakili Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa Abidjan na kasar Côte d’Ivoire, domin wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen rantsar da Shugaban Alassane Ouattara a wa’adinsa na hudu. Za a rantsar da Shugaban ne a yau Litinin, 8 ga watan Disamban 2025, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abidjan, wanda shugabanni daga kasashen Afrika da sauran manyan baki daga sauran kasashen duniya za su halarta. Shugaba Ouattara ya sake lashe zabe ne a ranar 25 ga watan Oktoban 2025, inda ya sake samu wani sabon wa’adi na jagorantar kasar. Sake Rantsar da shi na nuna da ci gaban da dimokuradiyya a kasar ta Côte d’Ivoire da kuma kyakkyawar dangantakarta da Najeriya. A cewar Fadar Shugaban...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan.   Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadannan ‘yansanda, akwai batun samar da kayan aiki da horo da sauran abubuwa da ake bukata don gudanar da dawainiyar ‘yansandan. NAJERIYA A YAU: Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin...
    Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi wa kasar Najeriya alkawalin taimaka ma ta domin ta fuskanci matsalolin tsaro, musamman ma dai ta’addanci a arewacin kasar. Shugaban kasar Faransan ya ce, takwaransa na Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bukaci taimako domin fuskantar matsalar tsaro a arewacin kasar. Macron ya rubuta a shafinsa na X cewa; Saboda bukatar da ya gabatar ta taimako, za mu bunkasa yadda muke aiki da gwamnati da kuma taimakawa ‘yan kasa da su ka cutu. Muna kuma yin kira ga dukkanin kawayenmu da su bayar da nasu taimakon. Sai dai shugaban kasar ta Faransa bai bayyana yadda taimakon zai kasance ba. Makwanni kadan da su ka gabata ne dai shugaban kasar Amurka ya yi wa Najeriya...
    Fitacce mai shirya fina-finai dan kasar Iran Majid Majidi ya sami kyauta ta musamman a wurin bikin fina-finai na Eurasia, saboda gagarumar rawar da yake takawa a fagen shiryafina-finai da su ka shahada a duniya. A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka bude bikin a birnin Moscow wanda ya sami halartar ministan al’adu na kasar Rasha, Olga Lyubimova, mataimakin shugaban kasar Rasha, Vladmir Medinsky sai kuma jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a Rasha Kazem Jalali. Shugaban Tsangayar FIna-finai ta Eurasia,  Nikita Mikhalov ya jinjina wa Majid Majidi saboda fina-finan da ya yi da hakan ya sa aka ba shi kyauta ta musamma da ita ce lambar yabo ta “ Dimond Butterfly”. A jawabin da ya gabatar, Majid Majidi...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, bayan wasu sojoji sun bayyana hamɓarar da Gwamnatin Shugaba Patrice Talon. Gungun sojojin, sun bayyana cewa ta rushe gwamnati tare da dakatar da kundin tsarin mulki, da rufe iyakokin ƙasar. An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sun kuma ayyana Laftanar Kanar Tigri Pascal a matsayin Shugaban gwamnatin soja. Daga baya gwamnatin Benin ta sanar da cewa sojojin ba su yi nasarar yin juyin mulkin ba. Rahotanni sun nuna cewa jiragen yaƙin Najeriya sun shiga ƙasar domin kare dimokuraɗiyya, duk da cewa babu cikakkun bayanai ba....
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.” Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da...
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.” Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da...
    Wani jirgin Sojin saman Najeriya ya yi haɗari jim kaɗan bayan tashi daga sansanin Sojin ƙasar da ke Kainji a jihar Neja, sakamakon tangarɗar inji. Kakakin rundunar sojin saman na Najeriya Ehimen Ejodame lokacin da yake tabbatar da faruwar haɗarin ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa sanadiyyar wannan haɗari, sai dai fasinjan da ke cikin jirgin yanzu haka suna karɓar kulawar gaggawa a asibiti. Tuni dai aka jiyo hafson sojin saman Najeriyar Air Marshal Sunday Aneke, na yabawa matuƙan jirgin wanda ya bayyana da jajirtattu, da ya ce ƙwarewa da jarumtarsu ce ta tseretar da asarar rayuka a haɗarin. Jiragen sojin Najeriya a lokuta da dama na gamuwa da haɗari wanda ke kaiwa ga asarar ɗimbin...
    Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa. Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, kuma suka tafi da shi hedikwatarsu da ke Bompai. Kwamashinan ya siffanta kamen da “abin damuwa sosai” wanda “ya yi kama da yanayin aikin soja”. Ya yi iƙirarin cewa dakaru kusan 40 ne ɗauke da makamai suka je kama Muhuyi. “Kwamashinan ya nuna cewa akwai yiwuwar lamarin yana da alaƙa da binciken da ake yi wa wasu manyan ‘yansiyasa,” in...
    ’Yan sanda sun kama tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimin Gado. Rahotanni sun nuna cewar wasu ’yan sanda ɗauke makamai ne suka kama shi a ofishinsa da ke Kano, bayan tafka jayayya a ranar Juma’a. Cikakken jadawalin rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026 Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum Waɗanda lamarin ya faru a kan idonsu, sun  ce manyan motocin ’yan sanda cike da jami’an da ke ɗauke da makamai ne suka dira ofishinsa da ke kan titin zuwa Zariya. Sun gargaɗi mutane da kada kowa ya kusanci ofishin, inda suka yi barazanar buɗe wa duk wanda ya yi yunƙurin tsoma baki a lamarin wuta....
    Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta a gaban sanatoci a jiya Alhamis. Kafin haka shugaban ya gabatar da sunayen wasu yan siyasa 3 don nadasu jakadu. A cikin wasikar shugaban yace mutane 34 daga cikinsu kwararrun jakadune, sannan sauran 31 yan siyasa ne. Daga cikin wadanda shugaba yanada har da tsohon shugaban hukumar zabena kasar (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu) sauran sun hada tsoffin gwamnonin jihohin. Enugu, Abia, tsohon mataimakin gwamnan...
    Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka za ta hana ’yan Najeriyar da ake zargi da yi wa Kiristoci kisan kiyashi biza Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa Ya ce ana zargin matashin ne mai shekaru 17 da aka fi sani da Amir, wanda makanike ne da kashe matar ta hanyar daba mata wuka. Wani makwabcin wajen ya shaida cewa ana zargin matashin ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell? ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa. NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro Ko yaya...
    Dan wasan taekwando na kasar iran  Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya  da ake gudanarwa a birnin Nairobi na kasar kenya , kuma ita ce lambar yabonsa na biyu a cikin kwanaki 35, Gasar tana gudana ne a filin wasa na moi international sport center dake kasar kenya kimanin yan wasa 452 da suka fito daga kasashen duniya 75 ne ke halartar gasar, kuma iran ta shiga gasar da yan wasa guda 16 da suka hada da mata 6 da kuma maza 8 da za su yi tasu karawar acikin kwanaki 4. Zandi da ya samu lambar yabo ta zinairiya a baya –bayan nan ya nuna gwaninta da ya cancanci...
    Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa. Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa. Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Ya gode wa Shugaban Ƙasa saboda zaɓarsa da ya yi a matsayin minista, sannan ya gode wa ’yan Najeriya saboda amincewa da suka yi da shi. Ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan. Ya ce: “Da na ga irin martanin...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da kwamishinoni biyu na hukumar, tare da sabbin manyan  sakatarori guda biyar da aka nada a gwamnatin tarayya. Daga nan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Bayan karanta takardar tarihin rayuwarsu, manyan sakatarorin biyar Abdulkarim Ibrahim, Dr John Ezeamama, Dr Abdul-Sule Garba, Dr Isiaku Mohammed da Dr Ukaire Chigbowu, sun dauki rantsuwar kama aiki, sannan suka sanya hannu a kundin rantsuwa. An kuma rantsar da Dr Aminu Yusuf, wanda shugaban kasa ya nada a matsayin Shugaban NPC a ranar 9 ga Oktoba, da kwamishinoni biyu ciki har da Dr Tonga Betara daga Jihar. NPC ita ce...
    Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, a zamanta na yau Laraba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga ofishin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele. Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro Sanarwar ta ce majalisar ta karɓi buƙatar Shugaban Ƙasa Tinubu na tabbatar da wanda aka naɗa Ministan Tsaro. Sanarwar ta ƙara da cewa za a karanta wasikar a gaban majalisar a ranar Laraba, sannan kuma za a ci gaba da tantance wanda aka naɗa nan take. Opeyemi ya bayyana cewa majalisar ba za...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa majalisar.   Wannan naɗin ya zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman hare-haren ’yan bindiga, da ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci a yankuna daban-daban. Ko wadanne irin kalubale ne ke gaban sabon ministan tsaron yayin da yake shirin kama aiki a ma’aikatar tsaro bayan majalisa ta tabbatar da shi? NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ne ya bayyana cewa; Yadda al’ummar Iran suke goyon bayan tsarin musulunci shi ne abinda ya          hana abokan gaba cimma mummunar manufarsu akan kasar. Shugaban na kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama ranar “Mutane Masu Bukata Ta Musamman” ta duniya ya bayyana cewa a yayin kallafaffen yaki na shekaru takwas tsakanin 1980-1988, dukkanin duniya ta kasance a bayan ‘yan Ba’asiyya da zummar kawo karshen jamhuriyar musulunci,amma goyon bayan da al’ummar Iran suke bai wa tsarin musulunci goyon baya, hakan ba ta faru ba. Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; “Yan Sahayoniya da Amurka sun kawo wa Iran hari da yakin kwanaki 12 a karkashin wannan irin tunanin...
    A yau Talata ne mai bai wa shugaban kasar ta Nigeria, shawara akan watsa labaru Bayo Onanuaga ya sanar da Nadin na Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin wanda zai maye gurbin Alhaji Muhammad Badru Abubakar da ya yi murabus a jiya Litinin. Janar Musa ya rike mukamai masu yawa na soja gabanin Nadin nasa a yau. Daga cikin mukamin shugaban bangaren tsaro na soja a tsakanin 2023 zuwa oktoba 2025.  Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.   An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, wanda hakan ke sa magani ya yi wahala kuma ya rage yiwuwar ceto rayuwar wanda ya kamu da shi. NAJERIYA A YAU: Halayen Da Ambasadoji Ya Kamata Su Mallaka Kafin Tura Su Wasu Kasashe DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? Wannan...
    An kashe wani ɗan sanda a wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai gidan Babban Jami’in Ɗan Sanda (DPO) mai kula Babba Ofishin ’Yan Sanda da ke Aujara a Ƙaramar Hukumar Jahun ta a Jihar Jigawa.   Da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, ranar 25 ga Nuwamba, 2025, ne wasu ’yan bindiga suka kai farmaki gidan DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan. Sanarwar rundunar ’yan sanda ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa jami’an tsaro da ke gadin gidan sun yi ƙoƙarin dakile harin, inda aka samu musayar wuta. A yayin arangamar, biyu daga cikin jami’an sun samu munanan raunuka, aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa. Tinubu ya gana da Janar Christopher Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus...
    Anicen Ekane dan adawa na jam’iyyar African Movement for New Independence yana daga cikin fitattun yan  siyasa a kasar Kamaru, kuma yana goyon bayan Issa Chiroma a zaben shugaba kasa wanda aka gudanar a kasar a cikin watan Octoban da ya gabata. Issa Chiroma dai ya shelanta cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a cikin watan Octoban da ya gabata. Jami’an tsaro sun yi dirar mikiya kan masu goyon bayan Chiroma, kuma sun kashe mutane da dama sun kuma kama wasu Anicen Ekaney ana daga cikin wadan da aka kama a birnin Duala a ranar 24 ga watan Octoba. Kuma Ekane ya zargi jami’an tsaro da kwace maganin Oxigen dinsa, wanda ya jefa rayuwarsa cikin hatsari,...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace tuna shakarar 2012, waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  ’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru. Rediyon Najeriya ya ruwaito  cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda, kuma ya faru ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin tarayya ta samu ’yantar da mambobin Cocin Christ Apostolic Church (CAC) 38 da aka yi garkuwa da su a yankin. Majiyar da ta yi magana da Rediyon Najeriya ta ce ’yan bindigar sun farmaki Aasaru ne a wani daji da ke kan hanyar Koro. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto da matarsa da mabiyansa a yayin da suke tsaka da ibada a coci da ke a  Jihar Kogi. Wani ganau da ke cikin cocin a lokacin da aka kai harin, Adegboyega Ogun, ya ce misalin ƙarfe 9.30 na safe ’yan bindigar suka kai harin suna bude wuta. “Mutane sun qarshe ta ko’ina, har da faston, wanda aka fi sani da Baba Orlando da matarsa da wasu masu ibada duk an yi garkuwa da su. Gaskiya harin ya yi muni, dukkanmu tserewa muka yi daga cocin.” Sace masu ibadar a ranar Lahadi a Cocin Cherubim and Seraphim ya auku ne bayan a kwanan nan Gwamna Usman Ododo, ya koka da cewa wasu  manyan...
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya iso birnin Tehran a jiya lahadi kuma  ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar iran Abbas Araqchi. Ziyarar tasa ana saran za ta kara fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ganin cewa dukkan kasashen biyu suna taka rawa a batutun da suka shafi yanki dama duniya baki daya. Bugu da kari bayan ganawarsa da Araqchi da musayar ra’ayoyi kan batutuwa daban daban, zai gana da sauran manyan jami’an gwammnatin kasar, da ake saran za su tattauna kan alakar dake tsakaninsu da kuma irin ci gaban da aka samu a yankin da dai sauran batutuwa na kasa da kasa. Ana sa bangaren shugaban kasar iran Masud pezeshkiyan a lokacin ganawarsa...
    A wani bangare na huldar duplomasiya tsakanin iran da saudiya , mataimakin ministan harkokin wajen kasar saudiya Saud bin mohammad Al-sati ya gana da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a nan birnin tehran inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafin alakokin dake tsakani da kuma ci gaban yankin. Ganawar wani bangare ne na kokarin da kasashen biyu ke yi na kara karfafa dangantakar dake tsakaninsu da kuma ci gaba da tattaunawa kan batutuwa masu tsauri, saudiya da iran sun kara fifita huldar diplomasiya domin shawo kan rikicin da ake ciki a yankin da kuma samar da damarmakin yin aiki tare. Ganawar tasu ta zo ne adaidai lokacin da ake cikin mawuyacin halin a yankin  da suka hada...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa.   Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen jakadu da yake sa ran majalisar kasa ta tantance ne dai batun ke ta shan suka daga manazarta kan sunayen da ya fitar. Ko wadanne irin halaye ya kamata jakada ya mallaka a yayin da za a tura shi a matsayin wakili a wata kasa? NAJERIYA A YAU:Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini DAGA LARABA:...
    Hukumar Agaji ta MDD ta sanar da cewa, kasar Somaliya ta shiga cikin wani mawuyacin yanaki saboda fari, da yanki mai yawa na kasar ya bushe bayan da aka dauki shekaru hudu a jere babu ruwan sama. Hukumar ta MDD ta kuma ce, da akwai miliyoyin mutanen kasar da suke fuskantar yunwa mai tsanani, yayin da wasu kuma suke ficewa daga garuruwan nasu. A can kasar ta Somalia, gwamnati ta shelanta shiga ” halin- ko- ta- kwana’ saboda farin, tare da yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kai dauki na gaggawa,musamman a yankunan Arewa da Kudancin kasa da kuma tsakiya.” Yankin Portland ne ya fi cutuwa daga fari, inda gwamantin Somaliya ta yi kiyasin cewa da akwai...
    ’Yan bindiga sun shiga garin Chaco da ke Ƙaramar Hukumar Wurno a Jihar Sakkwato, inda suka sace amarya da ƙawayenta guda 14. Yayin da mutane ke tsaka shagalin bikin auren, sai ’yan bindigar suka afka musu tare da tarwatsa komai. Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano Sun shigo garin a ƙafa, inda suka wuce kai-tsaye zuwa gidansu amaryar ba tare da sun taɓa kowa ba. Wani daga cikin iyayen ƙawayen amaryar ya shaida wa Aminiya cewa ba a tantance adadin waɗanda aka sace ba, amma wasu na cewa 15 ne, wasu kuma na cewa 13, amma amaryar da ’yarsa na cikin waɗanda aka...
    ’Yan bindiga sun harbe wata tsohuwa har lahira a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Yankamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano. Sun kai harin ne a daren ranar Asabar, a lokacin da mutanen ƙauyen ke kwance. Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32 Yayin kai harin, ’yan bindigar sun kuma sace aƙalla mutum uku. Yankamaye, wani ƙaramin ƙauyen manoma ne, ’yan bindiga da ke tserewa daga maƙwabtan jihohin Kano ne suka fara kai musu hare-hare. Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’ai domin bin diddigin maharan. Mazauna ƙauyen sun ce ’yan...
    Cinikin kasashen waje na kasar Iran a cikin watanni takwas na farko na bana ya kai tan 131,540, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 76.5. kwatankwacin tagomashi na kashi 1.53% idan aka kwatanta da bara warhaka. Bayanin da aka samu daga hukumar kwastam ta Iran ya ce: “A wannan lokacin, an fitar da tan 105,231,000 na kayayyaki daban-daban, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 37, zuwa kasashe daban-daban. Wannan adadi yana wakiltar karuwar kashi 1.17% idan aka kwatanta da wannan lokacin a shekarar da ta gabata. A daya bangaren kuma ” Iran ta kara fitar da kayayyaki zuwa ga Kungiyar Tattalin Arziki ta Eurasia (EAEU), kimanin shekaru biyu bayan yarjejeniyar cinikayyar ‘yanci da aka sanya wa hannu tsakanin Tehran da...
    Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar najeriya Bola Ahmad tunubu ya mika sunayen mutane 32 ciki har da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mahamud yakubu da tsohon ministan sufurin jiragen sama femi kayode ga majalisar dokokin kasar domin a tantancesu kwanaki bayan tura sunayen mutane 3 a fara da su. Mai magana da yawun shugaban kasar bayo Onanuga shi ne ya fitar da sanarwa, a cikin wasu wasiku ma banbanta da shugaban kasar ya turawa shugaban majalisa Godswill Akpabiyo ya bukaci majalisar ta amince da sunaye 15 a matsayin jakadun aiki da kuma wasu 17 da bana aiki ba, Akwai mata guda 4 daga cikin sunayen a matsayin jakadu na aiki da kuma wasu guda 6 a matsayin jakadu...
    Cibiyar HANs Centre for Social Justice and Development tare da Kanady Academy, sun kammala horon kwana uku domin koya wa yara marasa galihu da matasa mata sana’o’in dogaro da kai a Jihar Gombe. Shugabar HANs, Barista Hannatu Dauda Simon, ta ce an shirya horon ne domin ƙarfafa gwiwar mahalarta, tare da koya musu yadda za su iya rayuwa ba tare da dogaro da wasu ba. Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali Ta ce halin tattalin arziƙin ƙasar nan ya ƙara nuna muhimmancin sana’ar hannu ga matasa. Ta bayyana cewa matasa mata 100, ciki har da ɗaliban Kanady Academy ne, suka halarci horon. Masu horarwa daga...
    A baya, samun fara da yawa a shekara abin tsoro ne ga kowa, dalilin ɗab’arta ta lalata amfanin gona, sai dai a yanzu ta zamo hanyar samun abincin mutanen da dama, musamman ma mata a Jihar Kano. Duk da cewa a baya ma akwai tsirarun mutane da ke cin fara dace kuma halaccin cin ta a Musulunce, masu ƙyamar ta sun fi yawa, har ma wasu ke ganin masu cin ta za su iya cin kyankyaso. Sai dai a yanzu wannan ɗabi’a ta kusa zama tarihi, saboda fara ta zamo abincin taɓaka-lashe ba ga mata kaɗai ba da aka saba gani a baya, har ma da maza da masu kuɗi, inda ake mata mazubi na musamman da tsarabe-tsarabe, har...
    A baya, samun fara da yawa a shekara abin tsoro ne ga kowa, dalilin ɗab’arta ta lalata amfanin gona, sai dai a yanzu ta zamo hanyar samun abincin mutanen da dama, musamman ma mata a Jihar Kano. Duk da cewa a baya ma akwai tsirarun mutane da ke cin fara dace kuma halaccin cin ta a Musulunce, masu ƙyamar ta sun fi yawa, har ma wasu ke ganin masu cin ta za su iya cin kyankyaso. Sai dai a yanzu wannan ɗabi’a ta kusa zama tarihi, saboda fara ta zamo abincin taɓaka-lashe ba ga mata kaɗai ba da aka saba gani a baya, har ma da maza da masu kuɗi, inda ake mata mazubi na musamman da tsarabe-tsarabe, har...
    Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sake bayar da wani dauki a Kasuwar hada-hadar musayar kudade, da nufin samar da sauki wajen samun kudade a cikin kasar. Hakan ya sanya Bankin, ya sayar da dala miliyan hamsin, ga dilolin da aka yarjewa yin hada-hadar musayar kudade a cikin kasar. Kazalika, Bankin ya yi hakan ne, domin samar da daidaito, wajen yin hada-hadar musayar kudaden Naira dai, ta fara fuskantar tarnaki ne, biyo bayan samun raguwarta a kasuwar hada-hadar musayar kudade, inda kuma bukatar dalar, ya kara karuwa. Tun bayan da Naira ta samu farfadowa, Bankin na CBN, ya samu sauki kan hada-hadar musayar kudaden da aka yi. Sai dai, Bankin na CBN ya tura dala miliyan hamsin musamman domin dillalen da...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasar Yamen ta yi tir da matakin da kasashen birtaniya da Amurka suka dauka na sukar hukumcin kisa da aka yanke wa wasu yan leken asiri bayan kama su da laifi, tace bata amince da wannan mataki ba kuma tsoma baki ne a harkokin cikin gidanta. Ma’aikatar harkokin wajen kasar yamen ta bayyana cewa ma’aikatar sharia ta kasar tana da cikakken yanci kuma tuni ta yanke hukumcin kisa kan wadanda aka kama da yi wa kasashen waje leken asiri a kasar Haka zalika ta ce duk wata kasa da tace za ta dauki mataki kan wannan hukumci Amurka ce ko birntaniya to za ta dauke shi matsayin shiga shugalarta ne, kuma ba za ta amince da...
    Jagoran juyin musulunci na kar iran Ayatullah sayyid Ali Khamna’i ya bayyana cewa kasar Amurka bata ji da dadi ba a yakin kwanaki 12 da ta kaddamar a kan kasar iran a watan yuni, duk da amafani da ta yi da manyan makaman yaki na zamani da suka hada da jiragen yaki da kuma makaman kariya . Har ila yau jagoran yace Amurka da isra’ila sun sha kashi a yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan kasar iran, sun kai harin ne don su ci blus, sai suka koma da borin kunya, basu iya tabuka komai ba, wannan babban shan kashi ne a garesu, Yace wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnatin sahyuniya ta shirya yakin shekaru 20, ta shirya tunzura...
    Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce Najeriya na iya ajiye biliyoyin naira a duk shekara idan aka rungumi tsarin majalisa ta wucin gadi. Yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, Ndume ya ce kuɗin da ake kashewa wajen kula da Majalisar Dokoki a tsarin zama kodayaushe ba zai dore ba, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke fama da matsalolin kuɗi da tsaro. An janye ’yan sanda 11,566 daga yi wa manyan mutane rakiya – Egbetokun An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra “Kudin gudanar da gwamnati ya yi yawa sosai. Idan ’yan majalisa suka zauna na wucin gadi, gwamnati za ta ajiye biliyoyi,” in ji shi. Ya ce...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci, masanin tafsiri, kuma jagoran darikar Tijjaniyya, shahararre ne saboda iliminsa mai zurfi da tasirin da ya yi a fagen addini da tarbiyya a Najeriya da ma ƙasashen Yammacin Afirka.   Sheikh Dahiru Bauci ya shafe sama da shekaru saba’in yana koyar da ilimi, ya gudanar da tarukan tafsiri a duk shekara, ya gina makarantu, ya kafa cibiyoyi, kuma ya ba da ilimi ga dubban almajirai hanyoyin da suka taimaka wajen yaɗa ilimin addini cikin lumana da biyayya ga Allah Madaukakin Sarki. Rayuwarsa ta kasance tsantsa ta tsoron Allah, tawali’u, da ayyukan alheri. NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar...
    Daga Sani Sulaiman   Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu. Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta. Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan...
    Daya daga cikin ‘ya’yan babban malamin addinin musulunci a Najeriya Sayyid Ali Dhahiru Usman Bauchi ne ya tabbatar wa da jaridar “Daily Trust” rasuwar malamin. Sayyadi Ali ya furta cewa: ” Tabbas Shehi ya koma ga mahaliccinsa, mu duka daga Allah muke, kuma zuwa gare shi za mu koma.” Haka nan kuma ya kara da cewa, Lokaci ya yi da shehun malamin zai huta,kuma mun gode wa Allah da ya yi mana komai, ya tsawaita rayuwar shehi har zuwa wannan lokacin. Shi dai Shehu Dhariu Usman Bauchi an haife shi ne a 29 ga watan Yuni na 1927, ya kuma rasu yana dan shekaru 97 a wannan Alhamis din 27/ ga watan Nuwamba 2025. Gabanin rasuwarsa ya kasance daya daga...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya. Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Jama’ar yankin ne suka kira rundunar cewar fasinjojin wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai launin baƙi sun jefar da wata jaka, sannan suka tsere. Da jami’an rundunar suka isa, sun tarar da jakar da aka jefar. Bayan gudanar da bincike, sun gano harsasai 210 na ɗangon 7.56mm. DPO ɗin yankin ya sanar da sauran jami’an rundunar da ke kan hanyar...
    Bayan an zabi kasar Iran a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na hukumar yaki da makaman guba ta duniya, wato ‘ the Chemical Weapons Convention (CWC)’ da kuriun jimillar yan majalisar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata yi amfani da damar da ta samu na bin hakkin mutanen kasar Iran dangane da makaman guba wadanda Sadam Husain ya yi amfani da su a kan mutanen kasar a yakin shekaru 8 (1980-88). Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a taron CWC a birnin Hague a ranar Talatan da ta gabata. Ya kuma kara da cewa Iran zata bukaci a hukunta kasashen da suka taimakawa Sadam Husain a wajen...
    Wata cibiyar bincike mai suna “Frensic Architecture’ ta bada sanarwan cewa, HKI tana fakewa da tsagaita budewa juna wuta a Gaza a matsayin dama ta sake shata kan iyakoki a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto cibiyar tana cewa a halin yanzu HKI ta maida ‘koren layin da Trump ya shata a shwarar tsagaita wuta da ya gabata na tsaida yaki a Gaza a matsayin sabon taswirar Gaza. Labarin ya kara da cewa an Trump ya gabatar gabatar da wannan shawarar ce don sake tsuge fadin gaza, wanda kuma a halin yanzi sojojin hki suna hana Falasdinawa a gaza zuwa kusa da layin da suka shata, kuma duk wanda ya matso kusa da shi suka...
    Daga Isma’il Adamu  Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar. Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace. Ya bayyana cewa kashi 82 cikin ɗari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin ɗari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa...
    Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a duk fadin kasar, sakamakon karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta. Shugaban ya ce za a dauki sabbin jami’an tsaro nan ba da jimawa ba, wadanda suka hada da na sojiin, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro — domin karfafa matakan tsaron kasa. A karkashin sabon umarnin, an bai wa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ikon daukar karin jami’aaidubu ashirin,  wanda hakan zai kawo yawan sabbin  jami’an da za a dauka bana zuwa dubu hamsin. Shugaban kasar ya kuma amince a yi amfani da sansanonin horas da matasa masu yi wa kasa  NYSC a matsayin wuraren horaswa na wucin gadi, sakamakon gyare-gyaren da ake yi a...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja daga birnin Luanda na Angola, inda ya halarci taron AU–EU karo na 7 a madadin Shugaba Bola Tinubu. Ya wakilci shugaban kasa a taron G20 na 2025 da aka yi a Johannesburg, Afirka Ta Kudu. A Angola, Shettima ya karanta sakon Shugaba Tinubu wanda ya sake jaddada bukatar Afrika na samun kujerun dindindin da ikon zartarwa a Majalisar Dinkin Duniya. Ya kuma bukaci Tarayyar Turai su hada kai da Afrika wajen samar da tsare-tsaren zaman lafiya da tsaro. Shugaba Tinubu ya tabbatar da kudirin Nijeriya na ci gaba da inganta zaman lafiya, tsaro da mulki na gari a Afrika, tare da yin aiki da Tarayyar Turai domin samun daidaito da kwanciyar...
    Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADVS, da kuma ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta. Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Aikin ya shafi ƙananan hukumomin Makarfi, Hunkuyi da Ikara. Rundunar ta ce manufar wannan samame shi ne “share dukkanin maɓoyar miyagu, rushe sansanonin da suka kafa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan...
    Majiyar ‘yan hamayyar siyasar kasar Uganda sun sanar da cewa, jami’an tsaron kasar sun kama magoya bayan Bobi Wine dake takarar shugabancin kasar 300 a tsawon yakin neman zabe. Mai magana da yawun Bobi Wine dan takarar shugabancin kasar ya fada a jiya Talata cewa; jami’an tsaron kasar sun kama fiye da mutane 300 da suke goyon bayansa tun da aka fara yakin neman zabe daga watan Janairu zuwa yanzu. Bob Wine wanda shahararren mawaki ne ya juye zuwa dan siyasa, yana yin takara a karo na biyu da shugaban kasar mai ci, Uweri Musaveni. A zaben 2021 Bob Wine wanda sunansa na yanke shi ne Robert Kyagulanyi,, ya zo na biyu. Kakakin jam’iyyarsa ta NUP,ya ce, a cikin wannan...
    Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
    Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
    Jakadan kasar Aljeriya a MDD ya gabatar da jawabi a kwamitin tsaro na majalisar a jiya Talata, inda ya yi tir da hare-haren da HKI take ci gaba da kaiwa kan Gaza, da Lebanon duk tare da yarjeniyar da ta cimma na tsagaita wuta da kungiyoyin Hizbullah da Hamas. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ammar Ben Jamaa jakadan kasar Aljeriya a MDD yana cewa HKI ba ta mutunta yarjeniyoyin da ta cimma da kasashen Larabawa a yankin,  sannan masu shiga tsakanita da wadannan kungiyoyin sun kasa tabuka wani abu na ganin bangarorin biyu sun mutanen hakkin ko wani banagare. Jamaa ya kara da cewa a halin yanzu HKI tana kai hare-hare a kan kasashen larabawa da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi. Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu? NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara. Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci. An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi A cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira. Sabon harin, wanda ya faru da misalin...
    Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi. ’Yan ta’addan sun kai hari makarantar  ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar. Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja. An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu. Shugaba Tinubu ya...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar. Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.4, wanda ya kai kimanin kashi 76 cikin 100, don ayyukan raya kasa. Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum. A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri. Malam Umar Namadi ya ƙara...
    ’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
    Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin. Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon gaba da maza biyu da mata shida. ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai Wani ɗan uwa ga waɗanda aka sace, Kabiru Usman, ya ce maharan sun zo ne a ƙafa ɗauke da makamai, suka kuma yi garkuwa da matarsa Umma, ɗiyarsa mai shekara 17, da matar ɗan’uwansa da wasu...
    Gwamnatin kasar ta Gambia ta sanar da bai wa jagoran ‘yan hamayyar kasar ta Kamaru Isa Chiroma mafaka bisa dalilai na “‘yan adamtaka”. A wani bayani da ma’aikatar harkokin waje ta kasar Gambia ta fitar, ta bayyana cewa; Chiroma dan shekaru 76 ya isa babban birnin kasar Panjul a ranar 27 ga watan Febrairu a karkashin wata yarjejeniya da aka cimmawa a tsakanin kasashen yankin domin lalubo hanyar warware takaddamar siyasar da kasar Kamaru take fama da ita. Tun bayan da Chiroma ya fice daga kasar ta Kamaru, ya nufi kasar Najeriya, mahukunta a kasar tasa suke kiran da a kama shi. Sai dai maimakon haka, gwamnatin kasar ta Najeriya ta cimma matsaya da mahukuntan kasar Gambia akan a bai...
    Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin  ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare. Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya kuma nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin. A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta...
    ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
    Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadi jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun.   Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye...
    Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadi jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun.   Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye...
    Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya sun bada sanarwan cewa lokacin kafa yansandan jihohi ya yi, har’ila yau dakuma karfafa kula da dazuzzukan kasar saboda magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar. Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnonin na fadar haka a jiya Litinin bayan taron gwamnonin shiyar kudu maso yammacin kasar da suka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo. Gwamnonin 6 sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika masu gadin dazuzzuka a shiyar kudu maso yammacin kasar don tabbatar da tsaronsu , sannan gwamnonin jihohin guda  shida ne zasu dauki nauyin kula da jami’an tsaron.  Labarin ya kara da cewa shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ne ya karanta jawabin bayan taron...
    Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan kasar Yamen yayi kira ga kasar iran ta ci gaba da nuna goyon bayan kokarin da duniya ke yi wajen ganin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar Yamen Han Grungdbag wakilin majalisar dinkin duniya  yayi wannan kira ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin muscat na kasar Oman. Grundberg ya bayyanawa Araqchi ci gaban da aka samu kan batun kasar yamen kana yayi kira Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View...
    Yayan kungiyar yan ta’adda ta ‘the Islamic State West African Province (ISWAP) ta bada sanarwan kamawa da tsare yan mata 13 a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno a jiya Lahadi. Jaridar Daily Trust ta Nageriya ta nakalto Abdullahi Askira dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan Askira yana tabbatar da labarin ya kuma kara da cewa ISWAP ta kama wadan nan yan mata wadanda suke da shekaru tsakanin 13-19 ne a lokacinda suke aiki a gonakinsu a gundumar Mussa na karamar Hukumar ta Askira. Jaridar ta kara da cewa wannan satar yan mata da yan makaranta ya biyo bayan irinsu da suka yi a makarantar mata ta Maga a karamar hukumar Wasagu na jihar Kebbi da kuma na makarantar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative.   Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba. NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da...
    Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ƴansanda dake gadi ko rakiyar manyan mutane domin mayar da su aikin tsaro. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar Mr Bayo Onanuga, da yammacin wannan Lahadi, ya ce daga yanzu za’a rika tura jami’an ƴansanda ne gudanar da ayyukan ƙasa. Tinubu ya bayar da umarnin ne yayin ganawar da ya yi da shugabannin tsaron ƙasar da suka haɗa da rundunar sojin sama, da na ƙasa da na ruwa da Darakta Janar na ma’aikatar tsaro ta DSS da kuma Sufeto Janar na ƴansanda Kayode Egbetokun. Sanarwar ta ce, daga yanzu duk mutumin da ke son jami’an tsaro su yi gadinsa to ya nemi...
    Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi. Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad. Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Wani mazaunin yankin, Shamsuddeen Hashimu Zalawa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je gidan mutumin da tsakar dare. Ya ce sun dinga harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici. Ya ƙara da cewa sun nufi gidan Bakoshi kai-tsaye, wanda hakan ya sa wasu ke zargin ko turo su aka yi....
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan sanda umarnin daina tsaron manyan mutane a faɗin Najeriya. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi. ’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a Bauchi Onanuga, ya ce daga yanzu ’yan sanda za su mayar da hankalinsu ne aikin kare al’umma da yaƙar ’yan ta’adda. An ɗauki wannan mataki ne a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja, wanda manyan shugabannin tsaro suka halarta, ciki har da shugabannin ’yan sanda, sojin sama, sojin ƙasa da hukumar DSS. Sabon tsarin ya nuna cewa duk wani babban mutum da yake buƙatar tsaro dole ne,...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce. Ya ce DPO na Pindiga da shugaban ofishin ’yan sanda na Kashere, sun tuntuɓi wani dattijo da ya halarci cocin domin yin addu’a a ranar Lahadi. Dattijon ya shaida musu cewa babu wani abu da ya faru, kuma ’yan sanda suna harabar cocin tun safe a domin kula da sha’anin tsaro kamar yadda suka saba. Rundunar ta ce yaɗa irin wannan jita-jitar na iya tayae da hankalin jama’a. Ta kuma ce ta...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai. Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi. An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN “‘Yan sanda biyar sun rasu, biyu sun jikkata, amma an yi nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a ƙauyen Sabon Sara, Ƙaramar Hukumar Darazo, a jihar Bauchi.” Wakil, ya ƙara da cewa, “Ma’aikatanmu suna jajircewa kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin musayar wuta.” Ya bayyana ’yan...
    Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita kissan kiyashi a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto magajin garin birnin NewYork musulmi na farko na cewa yana son shugaban Trump ya karkata kudaden da yake kashewa kan sojojin Amurka wadanda suke yake-yaken da masa da wani amfani ga mutanen kasar Amurka zuwa magance talaucin da Amurka suke fama da shi a cikin gida musamman masu kwana a waje a...
    Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yakin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta nuna damuwarta kan karin hare-haren da ake kai wa mabiya addinin Kirista a Nijeriya. Hegseth ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, yana mai cewa bangarorin biyu sun tattauna kan “mummunan tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta,” tare da bayyana cewa Amurka na aiki da gaggawa da Nijeriya wajen rage hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi. Ganawar ta gudana ne a daidai lokacin da Amurka ke kara nuna damuwa game da tsaro a Arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda Boko Haram da ISWAP da kungiyoyin ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a kauyuka, da...
    Majalisar Dattijai ta nuna damuwa kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar sannan ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta amincewa da daukar akalla matasa 100,000 cikin rundunar sojoji domin karfafa tsarin tsaro na Nijeriya da yake fuskantar kalu bale. ‘Yan majalisar sun kuma yanke shawarar kafa kwamitin musamman domin bincikar yadda aka yi amfani da kudaden da aka ware shekaru da dama don Shirin Makarantu Masu Tsaro (Safe School Programme), a yayin da ake sake nuna damuwa cewa makarantun Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin hadari, inda a baya-bayan nan aka sace ‘yan mata a Jihar Kebbi. Wadannan kudurori sun biyo bayan tayin da Sanata Abdullahi Yahaya (APC, Kebbi North) ya gabatar, wanda ya yi...
    Daga Aminu Dalhatu Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara ta ce ta samu nasarar ceto mutune 25 da aka yi  yunkurin sacewa, bayan  wani hari da ’yan bindiga suka kai wa kauyen Kuraje da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau. Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a 21 ga watan Nuwamban 2025, da misalin karfe 10 saura kwara, lokacin da gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye yankin, suna harbe-harbe tare da tasa keyar  mata 10 da yara 15 domin tafiyada su. Sanarwar ta ce bayan samun kiran gaggawa, tawagar sintiri ta ’yan sanda daga sashen Damba da Sashen Ayyuka...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Kuraje da ke gefen birnin Gusau. Wasu gungun ’yan bindiga, ɗauke da makamai ne, suka kutsa cikin ƙauyen suna harbi, lamarin da ya jefa mazauna Kuraje da maƙotan ƙauyukan cikin tashin hankali. Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja A yayin harin, sun yi awon gaba da mata 10 da yara 15. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce ’yan sanda sun ɗauki mataki bayan samun kiran gaggawa. Ya ce tawagar haɗin gwiwa daga sashen Damba, Sashen Ayyuka da kuma Rundunar Tsaron Al’umma (CPG) sun isa ƙauyen cikin gaggawa. Sun...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au /////… Madalla, masu sauraro zamu fara shirimmu da labarimmu na farko wanda yake cewa majalisar gwamnoni a hukumar IAEA ta amince da wani kuduri na takurawa JMI a taron da ta yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamban da muke ciki. Kuduri wanda kasashen E3 ko Traiko na...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Iran mohammad Bhakir Qalibaf ya bayyana cewa makiya JMI sun sawya salon yakaar kasar kamar yadda suka saba, a halin yanzu sun fibada karfi kan takurawa tattalin arziki da rikita al-adu da kuma zamantakewa tsakaninmutanen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP  nakasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya jumm’a a wani taro na mayakan sa kai a nan birnin Tehran a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, da wannan dalilin ne gwamnatin kasar ta ke karfafa kira ga mutanen kasar su kiyaye hadin kan da suke da shi, su kara dankon zumunci da ke tsakanin kabilu da bangarorin kasar don hana makiya cimma manufofinsu a wannan yakin da ke yi da kasar. Yayi...
    Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr John Kiriakou yana fadar haka a cikin makon da ya gabata. Ya kuma kara da cewa saboda wannan barazanar ce gwamnatin shugaba Trump ta kaiwa cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran wadanda suke Fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ya ce shugaban yana ganin hare-haren da ya kaiwa cibiyoyin yafi sauki idan an kwatanta da makaman nukliya wadanda HKI ta yi barazanar zata yi amfani da...
    A ranar Alhamis da ta gabata ce karamin kwamiti mai kula da al-amuran nahiyar afirka a majalisar dokokin kasar Amurka ya bude tattaunawa dangane da zargin da shugaban kasar Donal Trump yake yin a cewa ana kashe kiristoci a tarayyar Najeriya fiye da duk wata kasa a duniya. Wanda hakan ya say a yi barazanar daukar matakan soje idan akwai bukatar haka don kawo karshen kissan. Jaridar Premium times ta nakalto Chris Smith dan majalisan da ya jagoranci taron yana fadar cewa zargin Trump gaskiya ne kuma shi a karan kansa ya kai ziyara tarayyar Najeriya har sau uku a baya inda sakamakon ya tabbatar da hakan. Sannan Bishop Wilfred Anagbe daga jihar Benue wanda ya halarci taron ta kafar...
    ’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama. A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da aka kai musu mummunan hari suna tsaka da ibada a cocin. Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai Majiyoyi daga iyalai da shugabannin al’umma sun tabbatar a ranar Alhamis cewa masu garkuwar sun fara kiran ’yan uwan waɗanda aka sace ta hanyar amfani da wayoyinsu. Sakataren cocin, Josiah...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u ‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka sace a cocin. Shugaban al’umma kuma Olori Eta na Eruku, Cif Olusegun Olukotun, wanda mutane huɗu daga cikin danginsa suka kasance cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida. Olukotun ya ce yana cikin coci tare da mutane biyar na danginsa lokacin da lamarin ya faru, inda ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin yaran da yake kula da su ya tsere...