Kamaru: Sai ranar Litinin Majalisar tsarin mulki za ta bayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasa
Published: 23rd, October 2025 GMT
Majalisar tsarin mulki a Jamhuriyar Kamaru, ta ce sai zuwa ranar Litini 27 ga watan Oktoban nan ne za ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar.
Majalisar ta sanar da ranar ne bayan ta duba tare da yin watsi da duk wasu kararrakin da suka shafi zaben na ranar 12 ga watan Oktoba.
Kafin nan gwamnatin Kamaru ta haramta taron jama’a a birane da dama daga jiya Laraba, gabanin sanar da sakamakon zaben, biyo bayan da madugun ‘yan adawa na kasar Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
Tun a makon da ya gabata ne magoya bayan Issa Tchiroma, wanda bisa ga kidayar tasa, ya ce ya samu kashi 54.8% na kuri’un da aka kada suka fito kan tituna suna ikirarin samun nasara a zaben shugaban kasa,lamarin da ya rikide zuwa ga tarzoma da ‘yan sanda a wurare da dama.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza : Sabani tsakanin Isra’ila, Amurka da Masar kan mataki na biyu na tsagaita wuta October 23, 2025 Araqchi: Akwai Sharuddan Da Iran Ta Gindaya Kafin Sake Komawa Kan Teburin Tattaunawa Da Amurka October 22, 2025 Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Tsaron Iraki Ya Gana Da Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar Iran October 22, 2025 Kasar Iran Ta Kai Hare-Hare A Wuraren Da Kawayen Isra’ila Ba Su San Da Su ba A Lokacin Yakin Kwanaki 12 October 22, 2025 Makamin Amurka Ne Ya Janyo Kisan Kiyashi A Gaza Sakamakon Wadata Isra’ila Da Makamai October 22, 2025 Korarren Jami’in Isra’ila Ya Ce: Dole Ne A Yi Bincike Kan Sakacin Da Aka Yi Har Hamas Ta Kai Hari Isra’ila October 22, 2025 Wani Masani Dan kasar Iran Ya Samu Lambar Yabo Ta WHO A Yankin October 22, 2025 Majalisar Najeriya Ta Amince Da Dokar Daurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Kananan Yara Fyade October 22, 2025 Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda October 22, 2025 China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban rundunar sojin ruwa kuma tsohon Kantoman jihar Ribas, Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin Jakadan Najeriya.
Tinubu ya kuma naɗa Ita Enang, tsohon sanata da uwargidan tsohon gwamnan jihar Imo Chioma Ohakim da tsohon ministan cikin gida kuma tsohon shugaban rundunar sojin ƙasa Abdulrahman Dambazau, a matsayin jakadun.
’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwaSunayensu nasu na zuwa ne ’yan kwanaki bayan Tinubu ya aike wa Majalisar Dattijai jerin farko na waɗanda yake son nadawa a matsayin jakadun.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar sabbin naɗe-naɗen a gaban majalisar a yayin zamanta na ranar Alhamis.
A cikin wasikar, shugaban ƙasa ya roƙi ’yan majalisa da su yi gaggawar duba sunayen domin bai wa gwamnati damar cike muhimman guraben jakadun.
Akpabio ya mika jerin sunayen ga kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ƙasashen waje, tare da umarnin cewa kwamitin ya kammala tantancewa ya kuma dawo da rahoto cikin mako guda.
Shugaban ƙasa a baya ya naɗa tsohon mai ba da shawara na fadar shugaban ƙasa Reno Omokri da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode da tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin jakadu.