HausaTv:
2025-12-03@08:37:48 GMT

Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: An Rusa Gaza Gaba Daya

Published: 18th, October 2025 GMT


Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Ruguza Gaza “ba abin da za a gaskata ba ne” domin an rusa yankin gaba daya

Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai, Tom Fletcher, ya ce: Girman barnar da aka yi a zirin Gaza abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba, yana mai jaddada cewa, “an ruguza komai tare da mai da yankin baraguzai,” yana mai nuni da irin barnar da aka yi wa ababen more rayuwa, da gidaje, da kashe fararen hula.

A cikin wata sanarwa ga gidan talabijin na Al Jazeera, Fletcher ya nuna cewa an riga an fara shirin ba da agajin jin kai na kwanaki 60. Shiri ne mai girma, wanda kashi na farko ke da nufin sauƙaƙe shigar da kayan agaji mai mahimmanci a cikin yankin.

Ya bayyana cewa, “Tsarin ya hada da samar da biredi, kawo tantuna, da inganta ayyukan tsaftar muhalli, baya ga kokarin dawo da asibitoci da makarantu, ganin yadda bangaren lafiya da ilimi ke fuskantar durkushewa.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Joseph Kabila Ya Koma Kasarsa Domin Kalubalantar Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kansa October 18, 2025 Gaza Ta Bukaci A Binciki Isra’ila Kan Sace Sassan Jiki A Gawarwakin Falasdinawa October 18, 2025 Hamas Ta Bukaci A Kafa Kotun Kasa Da Kasa Kan Gawarwarkin Da Isra’ila Ta Dawo Mata Da Su. October 18, 2025 Madagascar : An rantsar Da Michael Randrianirina A Matsayin Shugaban Kasar October 18, 2025 Iran Ta yi Tir Da Harin da Isra’ila Ta kai Kudancin Kasar labanon. October 18, 2025  Majalisar Dattawa Za Ta Gana Da Ministan Ilimi Kan Batun Yajin Aikin Asuu. October 18, 2025 Gaza ta bukaci a binciki Isra’ila kan sace sassan jiki a gawarwakin falasdinawa October 18, 2025 Madagaska : An rantsar da Kanar Randrianirina a matsayin shugaban kasa October 18, 2025 Al-Houthi: Matsin lamba bai hana Iran ci gaba da goyon bayan Falasdinu ba October 18, 2025 Marzieh Jafari  Ta Dauki Lambar Yabo Ta Horar Da Mata Wasan Kwallon Kafa Ta Nahiyar Asia October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar

Shugaban Ƙungiyar Iyaye na Jami’ar MAAUN, Alhaji Mustapha Balarabe, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa jami’ar ta yanke wasu kuɗi masu yawa domin yaye ɗalibai.

A wata sanarwa da ya fitar tare da sakataren ƙungiyar, Hajiya Habiba Sarki, ya ce koken da aka kai wa PCACC da kuma rahotannin da aka wallafa ba su da tushe.

Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno

Ya bayyana zargin a matsayin yunƙurin ɓata wa jami’ar suna.

Ya ce MAAUN na daga cikin jami’o’in masu zaman kansu mafi sauƙin farashi a Kano, kuma tana ba da ingantaccen ilimi.

“MAAUN na ɗaya daga cikin jami’o’i masu zaman kansu masu sauƙin farashi a Kano, tana ba da ingantaccen ilimi tare da ƙayatattun gine-gine.

“Wasu jami’o’in a jihar suna cajin kuɗin makaranta ninki uku a kan na MAAUN, amma ba a jin kukan kowa game da su. Me ya sa sai MAAUN?

“Idan ɗalibi ya biya kuɗin makaranta na tsawon shekaru huɗu, me ya sa za a ga laifi idan aka nemi ya biya kuɗin yayewa a jami’a mai zaman kanta?

“Wannan ba wani sabon abu ba ne. Wannan batu gaba ɗaya na nuna wata maƙarƙashiya ce da ke nufin ɓata suna da barazana daga wanda ba a san ko waye ba da yake iƙirarin cewa yana kare muradun ɗalibai da iyaye,” in ji shi.

Ya kuma yi tambaya: “Me ya haɗa MAAUN da hukumar PCACC a kan wannan batu?”

A ƙarshe, ya shawarci wanda ya kafa jami’ar da ya ci gaba da jajircewa wajen samar da ilimi mai inganci.

A gefe guda kuma, ya yaba masa saboda ƙin ƙara kuɗin makaranta duk da halin matsin tattalin arziƙi da ya sa wasu jami’o’i ƙara ƙudinsu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro
  • Shugaba Pizishkiyan:  Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufar
  • Kungiyar Hamasa Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji  A Yankin Gaza
  • Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2026 Na Kimanin Triliyan Daya
  • Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta
  • N750,000 kuɗin bikin yaye ɗaliban Jami’ar MAAUN ya tayar da ƙura a Kano
  • Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala
  • An yi gangami a fadin duniya a zagayowar ranar Falasdinu