Cutar karnuka: An ƙaddamar da riga-kafin karnuka 2,500 a Gombe
Published: 23rd, October 2025 GMT
Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya ta ƙaddamar da yunƙurin ƙasa baki ɗaya na yin rigakafi kyauta ga karnuka da maguna domin yaƙar cutar haukan kare inda Jihar Gombe ke shirin yin riga-kafi ga karnuka 2,500 a matakin farko.
Da take jawabi yayin bikin ƙaddamarwar da aka gudanar a Gombe, Babbar Sakatariya na Ma’aikatar, Dokta Chinyere Akujobi wadda Mataimakiyar Darakta, Dokta Salome Bawa ta wakilta ta bayyana cewa cutar haukan kare na ci gaba da hallaka dubban mutane a duk shekara a faɗin duniya, musamman a nahiyoyin Afirka da Asiya.
Ta ce, mafi yawan waɗanda ke mutuwa sakamakon cutar yara ne ’yan ƙasa da shekara 15, wanda hakan ke nuna cewa haukan kare ba wai matsalar lafiya kaɗai bace, matsala ce ta zamantakewa da ke shafar iyalai da al’umma baki ɗaya.
Dokta Bawa ta bayyana cewa, haukan kare cuta ce da za a iya kauce mata gaba ɗaya ta hanyar yin riga-kafi ga karnuka da maguna waɗanda su ne manyan hanyoyin yaɗa cutar ga mutane.
Ta ce, daga cikin allurai 26,000 na riga-kafin haukan kare da aka tanada a wannan matakin na farko, Jihar Gombe ta samu allurai 2,500, waɗanda idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, za su taimaka wajen rage yaɗuwar cutar a jihar.
A nasa jawabin, Kwamishinan Noma da Kiwo na Jihar Gombe, Mista Barnabas Malle, ya bayyana cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na da cikakken ƙudiri na kare lafiyar dabbobi da namun gida daga cututtuka masu cutarwa.
Ya tunatar da cewa jihar ta taɓa yin riga-kafin shanu domin kare su daga cutar huhu (anthrax) a bara, tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗa kai da Ma’aikatar Tarayya domin faɗaɗa shirye-shiryen kiwon lafiyan dabbobi.
Farfesa Grace Sabo Nok Kia daga Kungiyar War Against Rabies Foundation ta yaba da wannan shiri, amma ta buƙaci a samar da ƙarin allurai domin tabbatar da cewa kowanne kare da mage a jihar su samu riga-kafi.
Ta buƙaci likitocin dabbobi da su tabbatar da gaskiya da adalci wajen rarrabawa da yin amfani da riga-kafin yadda ya dace.
Haka kuma ta roƙi masu karnuka da su kai dabbobinsu cibiyoyin rigakafi, tana mai cewa kawar da cutar haukan kare na buƙatar haɗin kan kowa da kowa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Cutar karnuka haukan kare
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Sanar Da Wa’adin Biyan Kafin Alkalami Na Shekarar 2026
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi kira ga Maniyyata Aikin Hajjin 2026 da su biya kafin alkalami nan da ranar 14 ga watan Nuwamban 2025.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ibrahim Datti ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2025.
Hukumar wacce ta ce kudin kama kujerar kar su gaza Naira Miliyan Biyu, ta ce Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, na kokarin sama wa Maniyyata rangwame bisa kudin kujera da ta sanar a baya.
Ta kara da cewa duk wanda bai biya ba kafin karshen wa’adin da ta bayar, ba zai sami kujerar Aikin Hajjin Bana ba.
Har ila yau Hukumar ta ce Maniyyata za su iya yin rajista a ofisoshinta da ke sakatariyar Kananan Hukumomi 23 na Jihar Kaduna, ko kuma hedikwatar hukumar a kan titin Katsina, da ke cikin garin Kaduna.
Hukumar ta kuma ja kunnen Maniyyata da su guji yin mu’amala da duk wanda ba ma’aikacinta ba, tare da gujewa bai wa kowa kudadesu a hannu.
Rel/Safiyah Abdulkadir