Leadership News Hausa:
2025-12-08@14:44:17 GMT

Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

Published: 24th, October 2025 GMT

Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Har ila yau, shirin nan nata Mata A Aikin Noma, ya bai wa matan karkara sama da 20,000 tallafi da horarwa da ƙara samun kuɗin shiga ga iyalai da kuma wadatar da al’umma. Kazalika, shirin Tallafin Ilimi, ya samar wa fiye da ɗalibai 3,000, guraben karatu, kwamfiyutoci da kuma jagoranci na gari.

Ga tsofaffi kuma, Asusun Tallafa wa Tsofaffi ya bai wa tsofaffi 5,000 alawus-alawus da kula da lafiyarsu tare kuma da maido da martabar musamman waɗanda aka yi watsi da su, aka kuma manta da su.

Lokacin da iftila’i ya afku a Jihohin Filato da Benuwe a tsakiyar 2025, ba saƙo ta aike da shi; cikin gaggawa ta garzaya domin jajanta musu. Ta ziyarci waɗanda abin ya shafa, ta jajanta wa waɗanda suka rasa matsugunansu, sannan ta bayar da gudummawar Naira biliyan ɗaya ga kowace jihohin guda biyu. Daga baya a watan Agusta, ta ba da irin wannan agaji da ya kai kimanin Naira biliyan ɗaya ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Neja tare da buhunhunan shinkafa da kayan sawa 2,000.

A watan Satumba, ta mayar da bikin cikarta shekaru 65 zuwa hidimar ƙasa, inda ta tara kuɗi kimanin  Naira biliyan 20.4, domin kammala ginin ɗakin karatu na ƙasa da aka daɗe ba a yi ba tare da yin watsi da shi a Abuja. Sannan, ta ƙi karɓar wasu kyaututtuka da aka ba ta, wanda hakan ke nuna kyakkyawan shugabanci na-gari.

Tausaya Wa Nakasassu

Tausayinta ga nakasassu ya bayyana a fili cikin shirin nan ‘Renewed Hope Initiatiɓe’, a ɓangaren nan na koyar da sana’a’i, wanda ya horar da aƙalla mutum 1,200 ilimin kwamfuta, samar da ‘yan kasuwa tare da horar da wasu.  Ta kuma ba da tallafin kiwon lafiya da wayar da kan jama’a tare da tantance ‘yan Nijeriya sama da 100,000 masu fama da cututtukan hawan jini, ciwon siga da kuma matsalar ido, domin tabbatar da ko suna ɗauke da cututtukan tare da ɗaukar matakan gaggawa.

Ta hanyar dagewa wajen ganin shirin ya tafi yadda ya kamata, Sanata Tinubu ta gabatar da kyakkyawan tsari, domin aiwatar da ayyukan jin ƙai.  Dagewarta kan nuna gaskiya, ya sa shirin RHI ya samu karramawa daga ƙungiyoyin farar hula da sauran abokan ci gaban ƙasa da ƙasa.

Sabunta Harkokin Ilimi

Tsohuwar malamar makaranta, Sanata Tinubu na kallon ajujuwa a matsayin wurin da aka samar da sabbin sauye-sauye.  Shirin da ta samar na matasa masu ilimi, wanda aka ƙaddamar a shekarar 2024, aka kuma sake faɗaɗa shi a 2025, na tallafa wa ɗalibai masu hazaƙa, waɗanda iyayensu ke da ƙaramin ƙarfi (Talakawa), wanda ya dace da su tare da ba su shawarwari, musamman ta fuskar harkar ilimin kimiyya da fasaha.  Fiye da ɗalibai 1,200 a halin yanzu sun samu damar shiga shirin, wanda ke nuni da cewa; sama da kashi 95 cikin 100 na waɗanda suka rabauta, ba su taɓa mantawa da wannan abin alhairi da aka yi musa ba.

Tasirin Abin Da Za A Iya Ƙirgawa Da Kuma Wanda Ke Shafar Ruwa Kai Tsaye

A duk fadin Najeriya, za a iya ƙirga ayyukanta, ba kawai a ƙididdiga ba, a cikin labarai.

Mata manoma 20,000 a halin yanzu, suna samun kuɗin shiga akai-akai, saboda tallafin noma da horo na RHI.  Dubban ɗalibai, sun faɗa kasadar ficewa daga makarantusu, amma yanzu ƙarƙashin wannan shiri nata, sun koma azuzuwansu sakamakon bayar da tallafin karatun da ta yi.   

Haka zalika, sama da ‘yan Nijeriya 100,000 ne aka yi wa gwajin kamuwa da cututtuka masu tsanani daban-daban, sannan da dama daga cikinsu sun samu tallafin ceton rai. Yanzu haka, tsofaffi dubu biyar ne ke cin gajiyar alawus-alawus na yau da kullun da kuma zuwa duba lafyarsu, yayin da nakasassu kuma aka ba su kayan aiki, domin fara sana’o’insu, wasu kuma da kansu sun zama masu horar da su.

A kowane irin hali, alƙalumman na ba da labari iri guda: a ƙarƙashin Sanata Tinubu, tausayi ya zama shi ne abin aunawa, sannan kuma abubuwan da ake sa rai da su, sun tabbata.

Imani, Iyali da kuma Amfanin Shugabanci

Kasancewarta mai tsananin tausayi da gaskiya, jagora tagari, mai kuma son yin aiki ta hanyar yin haɗin gwiwa, Sanata Tinubu na ɗaya daga cikin waɗanda ke jagorantar al’ummar da samar da haɗin kai tare da tausayinsu.  Ta auri Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sannan ta daidaita buƙatun shugabancin ƙasa da iyali, imani da kuma tawali’u.

Nutsuwa da halinta da kuma ɗabi’un aikinta, sun haifar da sha’awa; har ma daga masu suka, suna sake fasalin ofishin Uwargidan Shugabancin a matsayin ɗaya daga cikin kulawa, maimakon alama.  Ta nuna cewa, mulki a cikin lumana, ka iya haifar da sakamako mai kyau tare da kuma tausayi.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba October 24, 2025 Manyan Labarai Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya October 24, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno October 23, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa

Amurka ta faɗaɗa yawan ƙasashen da ta sanyawa haramcin samun bizar shiga ƙasar zuwa 32 ƙarƙashin jagorancin Donald Trump da ke tsaurara matakan shiga wannan ƙasa ta yammacin duniya saboda abin da ya kira barazanar ƙasashen ga tsaron Washington da kuma kange kwararar ƴan cirani.

Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka Kristi Noem yayin wasu kalamanta a shirin kai tsaye ta gidan talabijin, ta ce dole ne Amurka ta dakatar da bizar ga duk wata ƙasa da ke turo mata baragurbi waɗanda ke wargaza tsaro da zaman lafiyarta.

Duk da cewa Noem bata bayyana sunayen ƙasashen ba, amma wasu bayanai da suka fita daga ma’aikatar sirrin ƙasar sun ce galibinsu ƙasashe ne na Afrika ciki kuwa har da Kenya da Angola da Masar da Habasha da Ivory Coast sai kuma Najeriya a gaba-gaba.

Wasu majiyoyi sun ce, daga cikin dalilan da ya sanya Amurka saka haramcin visa kan ƙasashen har da yadda wasunsu suka ƙi amincewa da karɓar ƴanciranin da Washington ke tisa ƙeyarsu, sai kuma batutuwa masu alaƙa da rashin isassun takardun shaida daga ƴan ƙasashen kana rashin inganci fasfo.

A cewar Noem yanzu haka ana ci gaba da tantance waɗannan ƙasashe don fitar da jerinsu, matakin da ke zuwa bayan tun a ranar 28 ga watan Nuwamban da ya gabata shugaba Trump ya sanya haramci visa kan mutanen da ke shigowa Amurkan daga ƙasashe matalauta ko masu fama da yaƙi.

Matakin na Amurka na zuwa bayan harin ranar 26 ga watan na jiya, da ya kai ga kisan wani Soja guda, harin da ake zargin wani ɗan ƙasar Afghanistan da kaiwa wanda aka ce ya shiga Amurkan don neman mafaka a shekarar 2021.

Ko a watan Yuni Amurka ta sanya haramcin visa kan ƙasashen Chadi da Congo da Equatorial Guinea da kuma Eritrea baya ga Libya da Somalia da kuma Sudan.

A wani mataki na daban kuma gwamnatin ta Amurka ta buƙaci tsauri kan matafiyan da ke shiga ƙasar daga Burundi da Saliyo da kuma Togo.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
  • An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166
  • Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas
  • ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno
  • Sabuwar Dokar CBN: Nawa Za a Iya Cirewa a ATM da POS?
  • Shugaban Majalisar Dattawan Akpabio ya Nemi Sanata Natasha ta Biya Shi Diyyar Biliyan 200
  • Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa