Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI
Published: 26th, October 2025 GMT
Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa.
Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi.
Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya ba a cikin juyin juya halin masana’antu da ke faruwa a duniya a halijn yanzu.
NASENI na zuba jari mai yawa wajen bincike a ɓangaren ayyukan da ake yi na yanayi mai dorewa a Nijeriya domin bunkasa tattalin arzikin ƙasa kamar yadda yake a tsare staren tattalin arziƙin shugaba Bola Ahamed Tinubu.
Hukumar NASENI ta haɗa kai da gwamnatin Jamhuriyar Czech domin raba jimillar dala miliyan 21.7 ga zababbun mutane 11 da za su ci gajiyar ayyukan Delta-2 don fara aiwatar musayar fasahohin zamani zuwa Nijeriya. Shirin Delta-2 shi ne samfurin haɗin gwiwar Hukumar Fasaha ta Jamhuriyar Czech (TA CR) ta hanyar da TA CR ke tallafa wa aiwatar da bincike da haɓaka masana’antu da cibiyoyi masu ƙima. An ƙaddamar da shi ne a cikin shekarar 2021, shirin Delta-2 yana ba da kuɗi kuma yana ba da damar bincike da haɓaka ayyukan ƙirƙire- ƙieƙire a fannoni uku da aka mayar da hankali: aikin gona, ma’adinai, da masana’antu gaba ɗaya.
Samar da famfon ban ruwa mai amfani da hasken rana na NASENI ya kawo sauyi ga harkar noma ta hanyar inganta noman rani. Yanzu haka manoman Nijeriya suna amfana ta hanyoyi daban-daban daga wannan fanfo mai sauƙin gaske wanda ke samar da ingantaccen ruwa na amfanin gona. Manoma za su iya amfani da famfon ban ruwa mai amfani da hasken rana don samar da amfanin gona akai-akai, wanda hakan zai bunƙasa yawan amfanin gona da kuma girbi da yawa a kowace shekara.
Yana sa manoma su rage dogaro da yanayin ruwan sama maras tabbas, don haka yana rage haɗarin gazawar amfanin gona. Yana kawar da dogaro da man dizal ko man fetur don ban ruwa tare da rage hayakin iskar gas da gurɓataccen muhalli. Hakanan za a iya amfani da shi a wuraren da basa tare da babbar hanyar wutaingantaccen hanyar grid ba. Ta hanyar amfani da famfunan ban ruwa mai amfani da hasken rana na NASENI, manoma suna ƙara haɓaka aikin noma sosai, da rage tsadar aiki, da samun ƙarin kuɗin shiga da inganta rayuwa idan aka kwatanta da famfunan ban ruwa masu amfani da man fetur.
Domin wannan ci gaba mai ɗorewa na ci gaban masana’antun Nijeriya da kuma tsara makomar al’ummar ta hanyar dogaro da kai, NASENI ce Gwarzon Kamfanin LEADERSHIP na shekarar 2025.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Iran da Saudiyya sun sake jaddada fadada dangantakarsu
Iran, China, da Saudiyya sun kammala taronsu na uku na Kwamitin Kasashen, inda Beijing ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da karfafa dangantaka tsakanin Tehran da Riyadh.
Zaman, wanda mataimakin ministan harkokin wajen Iran Majid Takht-Ravanchi da takwarorinsa na Saudiyya Walid al-Kharaji da na China Miao Deo suka jagoranta aTehran yau Talata, a yayinsa jami’an uku sun sanya hannu kan wata sanarwa ta hadin gwiwa da ta bayyana muhimman alkawarai.
Sanarwar ta sake jaddada kudirin Iran da Saudiyya na bin dukkan tanade-tanaden Yarjejeniyar Beijing ta 2023, wanda ya sauwaka wajen dawo da huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shiga tsakani na China.
Dukkan kasashen biyu sun kuma jaddada muhimmancin girmama ‘yanci da hurumin kasa kamar yadda Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, da ta Kungiyar Hadin Kan Musulunci (OIC), da dokokin kasa da kasa suka tanada.
Sanarwar ta yaba da “rawar da China ke takawa” wajen saukake tattaunawar da kuma sa ido kan aiwatar da yarjejeniyar.
A nata bangaren, kasar Sin ta sake nanata shirinta na tallafawa da karfafa matakan da Tehran da Riyadh suka ɗauka don haɓaka hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki, al’adu, da tsaro.
Sanarwar haɗin gwiwa ta nuna ci gaba a fannin haɗin gwiwa a ofishin jakadancin, wanda ya ba da damar yin tafiya lafiya ga mahajjatan alhazan Iran sama da 85,000 da kuma mahajjatan Umrah sama da 210,000 a shekarar 2025.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa ta tabbatar da sa hannunta wajen dakile juyin mulki a Benin December 9, 2025 RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne December 9, 2025 An cire Tony Blair daga jerin wadanda zasu jagoranci Gaza December 9, 2025 Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon December 9, 2025 Trump Ya Yi Gefe Da Kasashen Turai Dangane Da Tattaunawa Kan Rikicin Ukraine December 9, 2025 Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba December 9, 2025 Najeriya : Matsala ce ta sa jirgin sojinmu yin saukar gaggawa A Burkina Faso December 9, 2025 Saudiya da Qatar Zasu Gina Layin Dogo Mai Sauri Tsakanin Kasashen Biyu December 9, 2025 Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki December 9, 2025 Pakistan ta Bai Wa Taliban Ta Aghanistan Zabi A Tsakanin Mu’amala Da Ita Ko Da ‘Yan Ta’adda December 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci