An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing
Published: 26th, October 2025 GMT
Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin tafiya kasar Koriya ta Kudu, domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabanni karo na 32, na kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar, an gudanar da wani taron tattaunawa, mai taken “Shugabancin duniya da samun wadata tare a yankin Asiya da Pasifik” a nan birnin Beijing, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da jami’ar Yonsei da gidan talabijin na YTN na Koriya ta Kudu suka shirya tare.
Yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce “CMG na fatan yin hadin gwiwa mai zurfi tare da kasashen yankin Asiya da Pasifik, don haka ya dace mu ba da labaran hadin gwiwa tare, mu kirkira, kuma mu bunkasa musayar al’adu, mu shiga tattaunawa da hadin gwiwa, sannan mu ba da gudummawar hikimomi da karfinmu, wajen kyautata tsarin shugabancin duniya”. (Safiyah Ma)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: Asiya da Pasifik Asiya Da Pasifik
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Wakilan kasar Sin da na Amurka sun yi taro da safiyar yau Asabar don tattaunawa kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis da ta gabata, wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin, ya bayyana cewa, bangarorin biyu za su gudanar da shawarwari kan muhimman batutuwa game da huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, bisa muhimmiyar yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin da suka tattauna ta wayar tarho a wannan shekarar.
Mataimakin firaministan kasar Sin kuma memba na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin He Lifeng ne ke jagorantar tawagar kasar ta Sin a tattaunawar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA