Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina
Published: 22nd, October 2025 GMT
Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda ke bai wa ’yan kasuwa rancen har zuwa Naira miliyan 5 da kaso tara cikin ɗari (9%) a matsayin kudin ruwa, da kuma Naira biliyan 50 a ƙarƙashin shirin Shugaba kasa Bola Tinubu da ke bai wa ƙanana ’yan kasuwa tallafin kuɗi kyauta bisa wasu sharuɗɗa domin bunƙasa kasuwanci (Presidential Conditional Grant Scheme) da ke ba da tallafin Naira 50,000 ga ’yan kasuwa miliyan ɗaya a fadin kasar.
Haka kuma, gwamnatin ta samar da Asusun Tallafin Masana’antu daga Gwamnati (Manufacturers Fund) na Naira biliyan 75 don tallafa wa masana’antu wajen rage tsadar samar da kayayyaki da sufuri.
Mataimakin shugaban ƙasan ya ce sama da ’yan kasuwa 39,000 a jihar Katsina sun amfana da shirye-shiryen gwamnatin tarayya, inda aka raba Naira Biliyan 2.5 a matsayin tallafi da rance mai rangwame.
A ƙarƙashin shirin RAPID, Shettima ya ce ’yan kasuwa 23 daga yankunan karkara sun samu fiye da Naira Miliyan 112 don faɗaɗa kasuwancinsu. Ya kuma yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa kafa KASEDA, yana mai cewa Katsina na zama cibiyar ci gaban masana’antu, noma, da kasuwancin yanar gizo a Arewacin Nijeriya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki
Gwamnonin Kano da Katsina da na Jigawa sun shiga wata yarjejeniyar haɗin gwiwa kan bunƙasa kasuwar wutar lantarkin jihohin uku.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnonin sun zuba hannun jari a kamfanin Future Energies Africa (FEA), babban mai zuba jari a kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano wato KEDCO.
Kano Pillars ta dakatar da Kocinta An kama ɗan uwan Nnamdi Kanu da lauyansa —SoworeA cewar wata sanarwa da Kwamishinan Wutar Lantarki da Makamashi na Jihar Kano, Dokta Gaddafi Sani Shehu, ya fitar, an cimma yarjejeniyar ne a yayin taron bunƙasa wutar lantarki da aka gudanar a birnin Marrakech, Morocco, daga ranar 16 zuwa 19 ga Oktoba, 2025.
Dokta Gaddafi ya bayyana cewa jihohin uku za su yi aiki tare wajen gano sabbin hanyoyin inganta kasuwannin wutar lantarki, tare da kafa tsare-tsaren doka da tsarin haɗin gwiwa don inganta aikin rarrabawa da samar da wuta.
Ya ce, “samun hannun jari a kamfanin FEA zai taimaka wajen ƙarfafa dabarun KEDCO da kuma bunƙasa samar da wutar lantarki a yankin Arewacin Yamma.”
Kwamishinan ya ƙara da cewa jihohin za su kashe naira biliyan 50 wajen aiwatar da ayyukan bunƙasa wutar lantarki da kuma samar da wuta ta hanyoyi daban-daban, ciki har da na tsarin amfani da fasahar samar da wuta da hasken rana.
“Kazalika, za mu yi aiki tare da KEDCO domin rage asarar wuta daga masu amfani a gida, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da ingantaccen samar da wuta ga al’umma,” in ji shi.
An tsara cewa wakilan jihohin za su gudanar da taron kasa da kasa a kowace shekara, sannan su gana sau huɗu a shekara domin duba ci gaban ayyuka da tsara manufofi da karfafa dangantaka a kasuwar wutar lantarki ta jihohi uku.