Leadership News Hausa:
2025-12-10@05:27:23 GMT

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Published: 25th, October 2025 GMT

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

A gun cikakken zaman taro na hudu na kwamitin kolin JKS na 20 da aka gudanar tun daga ranar 20 zuwa 23 ga wannan wata a nan birnin Beijing, an yi bincike da zartas da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, inda aka gabatar da jagora da burika kan yadda za a raya kasar a wannan lokaci, kana an tsara taswirar bunkasa kasar Sin a shekaru 5 mazu zuwa.

Ga duk duniya, shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar ba shiri na kasar Sin kawai ba ne, kuma ba kasar Sin ba ce wadda ta fara tsara shirin, amma kasar Sin ita kadai ta kiyaye aiwatar da irin shirin. Sirrin tafiyar da harkokin kasar Sin shi ne jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta Sin da tunanin bunkasa kasa bisa tushen fifita jama’a. Bisa labarin da aka bayar a shafin yanar gizo na mujallar Forum ta kasar Brazil a ranar 22 ga wannan wata, an ce, dalilin da ya sa kasar Sin ta samu nasara shi ne kiyaye aiwatar da manufofinta a dogon lokaci.

Bunkasa ita ce mabudin daidaita dukkan matsaloli, kasar Sin ta rike wannan mabudi. A cikin manyan ayyukan da za a gudanar a yayin shirin na shekaru biyar-biyar karo na 15, samun ci gaba mai inganci ya zama matsayi na farko. Amma ta taya za a cimma wannan buri? An lura da cewa, raya tsarin sana’o’i na zamani da tabbatar da tushen raya tattalin arziki na hadaka ya zama wani muhimmin aiki a cikin shirin.

Ban da wannan kuma, ana bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa tare da su yayin ake tafiyar da harkokin kasar Sin. An ba da shirye-shirye kan fadada bude kofa ga kasashen waje a shirin na shekaru biyar-biyar karo na 15, kana an dora muhimmanci kan bude sabon babi na hadin gwiwa da samun moriyar juna. An sa ran cewa, a shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta bude sabon babi na samun zamanantarwa irin ta kasar, da kuma kiyaye samar da gudummawa ga duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC October 25, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take October 24, 2025 Daga Birnin Sin An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan October 24, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: na shekaru biyar biyar kasar Sin ta

এছাড়াও পড়ুন:

Venezuela: Ba Mu Tsoron Kaudin Amurka Na Wuce Gona Da Iri

Ministan harkokin cikin gidan kasar Venezuela ya bayyana cewa al’ummar Venezuela ba ta tsoron barazanar da Amurka take yi ma ta, domin juyin juya halin kasar zai ci gaba, kuma azamar al’umma ce za ta yi nasara a gaban masu wuce gona da iri.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Venezuela Diosdado Cabello Rondón wanda kuma shi ne sakataren jam’iyyar gurguzu ta kasar, ya ce a halin yanzu juyin juya halin kasar yana fuskatar gwagwarmaya ce wacce ba ta makami domin fuskantar matsin lamba na kowace rana daga Amurka.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Venezuela wanda ya halarci bikin rantsar da sabbin shugabannin al’umma a jihar Monagas ya yi Ishara da yadda Amurka ta girke jiragen yaki a ruwa kasa da Venezuela, da kuma jiragen yaki na sama, ba don komai ba,sai kokarin tilastawa al’ummar Venezuela su mika ma ta wuya ta hanyar tsoratarwa.

Haka nan kuma ya jaddada cewa, abinda Amurkan take yi ba zai harfar ma ta Da, mai ido ba; domin ba su da masaniya akan cewa al’ummar kasar ba su tsoron wani abu ba.

Haka nan kuma ministan harkokin cikin gidan kasar ta Venezuela ya ce, babu wani abu da al’ummar kasar suke tsoro.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Zama Zakaran  Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21 December 7, 2025 Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi December 7, 2025  Dubban Mutane Suna Guduwa Daga  Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada December 7, 2025 Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan December 6, 2025 Iran Da Masar Sun yi Kira Da Kawo Karshen Keta Hurumin Gaza da Labanon da Isra’ila ke yi December 6, 2025   Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba December 6, 2025 Gwamnatin Najeriya Za ta Karbi Sabon Bashin Dala Miliyan 500 A Bankin Raya Kasashen Afrika December 6, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Sun Yi Gargadi Game Da Yunkurin Isra’ila Na Kashe Barghusi December 6, 2025 Gasar FIFA: Iran Ta Fada Cikin Group Mai Sauki A Gasar Kwallon Kafa Ta FIFA 2026 December 6, 2025 Kasashen Musulmi 8 Sun Ki Amincewa Da Korar Falasdinawa Daga Gaza December 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yaba Ma Iyaye Bisa Goyon Bayansu ga Shirin Rigakafin Shan Inna a Karamar Hukumar Ringim
  • Matsalar rashin tsaro ce ta sa na yi waqar “Arewa”-SKD Arewa
  • Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki
  • Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima Ya Isa Abidjan Wajen Rantsar da Shugaba Ouattara
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
  • Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Benin
  • Venezuela: Ba Mu Tsoron Kaudin Amurka Na Wuce Gona Da Iri
  • Iran Ta Zama Zakaran  Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21
  • Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi