Aminiya:
2025-10-25@14:23:46 GMT

’Yan sanda sun taimaka wa ’yan daba rusa gidaje — Al’ummar Shendam

Published: 25th, October 2025 GMT

Mazauna unguwar Tudun Wada da ke garin Shendam a Jihar Filato sun zargi wasu jami’an ’yan sanda da ba wa ’yan daba kariya wajen rusa gidajensu.

Shaidu sun ce sama da ’yan sanda 100 ɗauke da makamai ne suka isa yankin da misalin karfe 5 na safiyar Laraba, suka ba wa wasu ’yan daba kariya yayin da suke lalata gine-ginen jama’a

Lamarin ya jawo zanga-zangar da mazauna yankin, ciki har da mata da yara, suka gudanar don nuna adawa da abin da suka kira “cin zarafi daga jami’an tsaro.


Mazaunan sun bayyana cewa rushewar gidajen ta faru ne da haɗin gwiwar iyalan Fuanter duk da cewa ana shari’a a gaban kotun ɗaukaka ƙara kan mallakar filayen.

Sun ce suna da takardun mallaka, kuma sun daɗe suna zaune a wurin ba tare da wata matsala ba.
A cewar su, irin wannan yunƙurin rusa gidajen ya taba faruwa a shekarar 2023, sai dai Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda (DIG) na yankin ya dakatar da lamarin bayan ƙorafe-ƙorafen da ke zargin tsohon Kwamishinan Kasa da Tsare-tsare na Jihar Filato, Mista Festus Fuanter, da jagorantar aikin — abin da ya musanta, yana mai cewa rikicin tsakanin iyalansa ne da wasu mutum uku.

Wani mazaunin yankin, Muhammadu Bashiru, ya ce: “Da asubahin Laraba misalin karfe 5:45 na safe muka ga motoci Hilux guda shida ɗauke da ’yan sanda da ’yan daba suka fara rusa gidajenmu. Sun ƙona wasu gine-gine, sannan suka zuba wani sinadari mai guba a wasu wurare.”

Shi ma wani da abin ya shafa, Abbass Tega, ya ce an yi rusau ɗin ba tare da wata umarnin kotu ba kuma babu jami’in kotu da ya halarci lokacin da abin ke faruwa.

Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙaramar hukumar Shendam yana ƙoƙarin sasanta rikicin kafin jami’an su dawo da rushe-rushen a wannan makon.

Da aka tuntube shi ta waya, Mista Fuanter ya ce ba shi da hannu a ƙarar da ke kotu, kuma kotun faukaka ƙara ta riga ta yanke hukunci, yayin da waɗanda suka kai kara suka kasa ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli.

Kakakin ’yan sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da samun labarin lamarin, yana mai cewa rundunar ta fara bincike kan abin da ya faru.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya , Nyesom Wike, ya yi gargadin cewa irin yadda gwamnonin jam’iyyar PDP ke tafiyar da al’amuranta a yanzu, zai iya sanadin rushewar jam’iyyar.

Wike, ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Abuja ranar Juma’a, inda ya zargi gwamnonin PDP da gaza magance rikicin jam’iyyar yadda ya kamata.

An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai
Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027

Rahotanni sun nuna cewa akwai rashin jituwa tsakanin Wike da gwamnonin PDP.

Jam’iyyar na shirin gudanar da babban taronta na kasa a watan Nuwamba a birnin Ibadanna  Jihar Oyo, amma wasu rahotanni na cewar magoya bayan Wike na ƙoƙarin hana gudanar da taron.

A kwanakin baya, Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Samuel Anyanwu, ya zargi Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar naKasa (NWC) da yin amfani da sa hannunsa na bogi wajen aike wa INEc wasiƙa don sanar da shirin gudanar da taron.

Sai dai wasu shugabannin jam’iyyar sun ce Anyanwu yana aiki ne bisa umarnin Wike.

A yayin tattaunawar da ya yi da ’yan jarida, Wike ya ce: “Ban faɗa tun farko cewa tarkon da kuke saka wa kanku zai kama ku ba? Na faɗa tun da wuri, irin yadda waɗannan gwamnonin ke tafiyar da jam’iyyar, za su kashe ta ne.

“Kuna gudanar da taron jam’iyya, kuna kiran mutane manyan jam’iyya, amma kun bar ni saboda ba gwamna ba ne, ta yaya za ku ci gaba a haka?”

Wike ya kuma nesanta kansa daga masu goyon bayan tsohon Ministan Harkoki na Musamman, Tanimu Turaki, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

“Ban san wani abu game da Tanimu Turaki kan zama shugaban jam’iyya ba. Wataƙila zai zama shugaban wani bangare daban ne, ba PDP dana sani ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa tun da farko ya yi hasashen wasu ’ya’yan jam’iyyar za su fice daga cikinta.

“Tun farko na faɗa cewa idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, PDP za ta rika yin asara. Ana tafiyar da abubuwa bisa kuskure, kuma yanzu kowa yana gani. Abin kunya ne,” in ji shi.

“Duk abin da na faɗa a da yanzu yana faruwa,” a cewar Wike.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa
  • Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike
  • Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu
  • Gwamnan Neja ya ba dukkan iyalan wadanda suka kone a gobarar tankar mai N1m
  • Shugaba Tinubu Ya Jaddada Kudurin Gwamnatinsa Na Ƙara Zuba Jari A Ilimi
  • Majalisar Tattalin Arziki Ta Amince da Shirin Gyara Cibiyoyin Horar da Jami’an Tsaro
  • An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato
  • Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga
  • Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a fashewar tanka a Neja