Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Watsi Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Masa
Published: 25th, October 2025 GMT
Shugaba Gustavo Petro ya ce, ba wai kawai ba ya wata mu’amala ta kasuwanci da Amurka ba ne, ba shi ma da koda dala kwaya daya a cikin wani asusu na bankunan Amurkan balle a ce an rufe shi.
Gustavo ya kara da cewa; ko kadan ba zai taba rusunawa a gaban Amurka ba, ba kuma zai ja da baya ba.
A jiya Juma’a da marece ne dai Baitulmalin Amurka ya sanar da kakaba wa shugaban kasar ta Columbia takunkumi.
Gustavo ya kuma ci gaba da cewa; Yadda yake fada da yaduwar muggan kwayoyi na shekaru masu tsawo, shi ne ya sa Amurkan ta dauki wannan irin matakin akansa alhali kasarsa Columbia tana taimakawa wajen hana Amurkawan shan hodar Iblis.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya taba zargin takwaransa na Columbia da cewa yana taimakawa wajen yaduwar hodar Iblis, tare da siffata shi a matsayin dillalin muggan kwayoyi.
Amurka dai ta shiga tsama da Shugaban Columbia ne saboda siyasarsa ta kin jinin HKI da take tafka laifukan yaki a Gaza, bayan da kasarsa ta yanke duk wata alakar diplomasiyya da kasuwanci da ita.
A yayin taron babban zauren MDD a birnin New York, shugaban kasar ta Columbia ya yi kira da a kafa rundunar kasa da kasa domin kare al’ummar Falasdinu da HKI take yi wa kisan kiyashi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Kwallon Kafa Ta Futsal Ta Matan Iran Sun Sami Nasara Akan Kasar Bahrain October 25, 2025 Antonio Gutrress: MDD Tana Bukatuwa Da A Yi Ma Ta Kwaskwarima October 25, 2025 Lebanon: An Sami Shahidai 3 Sanadiyyar Hare-haren HKI A Kudancin Lebanon October 25, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Isra’ila Kan Kasar Lebanon October 24, 2025 Rasha Ta Jaddada Cewa: Kasashen Turai Sun Taka Doka Kan Batun Makamashin Nukiliyar Iran October 24, 2025 Ayatullahi Khatami Ya Ce: Shugaban Kasar Amurka Trump Dan Ta’adda Ne October 24, 2025 Shugaban Amurka Ya Ce: Za Su Dauki Matakin Soji Kan Kasar Venezuela Nan Gaba Kadan October 24, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Yi Allah Wadai Da Mamaye Yankin Yammacin Kogin Jordan Na Falasdinu October 24, 2025 ‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu October 24, 2025 Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada October 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da kawi karshen tattaunawa da kasar Canada dangane da batun kasuwanci
Shugabann a kasar Amurka ya zargi Canada da yin amfani da kalmomin tsohon shugaban kasar Amurka Ronald Regan ta hanayar da ba ta dace ba a cikin wasu tallace-tallace akan kudaden fito, inda ya bayyana cewa; ” Saboda la’akari da halayyarsu an kawo karshen tattaunawar kasuwanci da kasar Canada.”
Shugaban kasar na Amurka ya ci gaba da cewa; Cibiyar Ronald Ragan ta sanar da cea, Canada ta murguda zancen Regan yana Magana akan illolin kudin fito, kuma an yi hakan ne domin yin tasiri a cikin matakin da kotun koli ta Amurka za ta dauka akan batun da ake jiran ta fitar da hukunci nan gaba.
Cibiyar ta Regan ta wallafa sako a shafinta na X cewa; hukumar yankin Ontario a kasar Canada ta yanko maganar tsohon shugaban kasar ta Amurka da ya yi a watan Aprilu a 1987, don haka tana tunanin matakan da za ta dauka akan haka ta fuskar shari’a.
A can kasar ta Canada hukumar yankin Ontario ta sanar da cewa, maganar Regan da ta watsa ta jawo hankalin Donald Trump.
Firimiyan gundumar ta Ontario a Canada Dodge Ford ya ce; Na tabbata Trump ba zai ji dadin wannan sanarwar da mu ka wats aba.
Tun da fari, Fira ministan kasar ta Canada Mark Joseph Carney ya fada wa manema labaru cewa; Ba za mu bar Amurka ta cimma manufarta wacce babu adalci a ciki ba dangane da batun kasuwanci.”
Kasar ta Canada dai tana takaddama da Amurka akan batun kara kudaden fito da Trump yake yi kasashe abokan kasuwanci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Akan Yara Da Matan Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Shugaban Amurka Ya Soke Shirin Ganawa Da Takwaransa Na Rasha October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci