Leadership News Hausa:
2025-10-24@22:43:23 GMT

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Published: 24th, October 2025 GMT

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Bugu da kari, Han ya ce, zamanantar da aikin gona da raya yankunan karkara tana da matukar muhimmanci a cikin aikin zamanantarwa irin ta kasar Sin, saboda haka ya kamata a ba wannan bangare fifiko. Ya ce shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar na jaddada bukatar mai da raya harkoki masu alaka da aikin gona da raya yankin karkara da kyautata rayuwar manoma, a matsayin abu mai matukar muhimmanci, da tabbatar da bunkasar birane da yankin karkara na bai daya, da kuma hanzarta wajen inganta karfin kasar a fannin raya aikin gona.

 

A yayin taron, direktan hukumar raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin, Mr. Zheng Shanjie ya bayyana cewa, “kirkira da habaka sabbin abubuwa” na nufin habakawa da karfafa sabbin masana’antu da masana’antun da za su bullo a nan gaba. A shekarar 2024, tattalin arzikin “sabbin abubuwa uku” (wato sabbin masana’antu da sabbin nau’o’in cinikayya da sabbin hanyoyin kasuwanci) na Sin ya kai kashi 18% cikin alkaluman GDP na kasar. Shawarar da kwamitin tsakiyar JKS ya gabatar game da shiri na 15 na ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na shekaru biyar-biyar, ya yi kira da a kirkiro sabbin masana’antu masu muhimmanci, da gaggauta habaka gungun masana’antu masu muhimmanci kamar sabbin makamashi, sabbin kayayyakin aiki da bangaren harkokin sararin samaniya, da tattalin arzikin kasa, wanda zai haifar da kasuwanni da darajarsu za ta wuce Yuan tiriliyan 1. Kazalika shawarar ta yi kira da a shirya da wuri don kafa masana’antu na nan gaba, kamar ta fasahar lissafi ta quantum da kirkirar kayayyakin halitta da makamashin hydrogen da na nukiliya da hada kwakwalwar bil adam da na’ura da fasahar wayar hannu na zamani, da sauransu, wadanda za su zama sabbin hanyoyin habaka tattalin arziki. Wadannan masana’antu a shirye suke don kara karfi wajen kokarin habaka masana’antar fasaha a nan kasar Sin, a cikin shekaru 10 masu zuwa.

 

Ministan kula da cinikayya na kasar Sin Wang Wentao ya bayyana a yau Juma’a cewa, kasar za ta fadada bude kofarta ga kasashen waje yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru 5, na 15.

 

Wang Wentao ta kara da cewa, tsakanin shekarar 2026 zuwa ta 2030, za a yi kokarin fadada ba da damar shiga kasuwa da bangarorin da za a kara bude wa kofa, a bangaren bayar da hidimomi. Ministan ya ce wadannan na cikin shawarwarin da kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya gabatar wajen tsara shirin na 15 dake da burin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, wanda aka amince da shi yayin zama na 4 na kwamitin kolin da aka kammala jiya Alhamis.

 

A cewarsa, sauran manyan ayyuka sun hada da raya sabbin harkokin cinikayya da samar da karin hanyoyin zuba jari tsakanin Sin da kasa da kasa da kuma daukaka hadin gwiwar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. (Safiyah Ma, Amina Xu, Fa’iza Muhammad Mustapha)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan October 24, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15  October 24, 2025 Daga Birnin Sin Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu October 24, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An gano sauro a karon farko na tarihin ƙasar Iceland

A karon farko a tarihi, an gano sauro a ƙasar Iceland, tare da gano samfura guda uku a wannan watan a Kjos, wani yanki mai ƙwari a kusa da Hvalfjordur.

Wani mai sha’awar ƙwari, Bjorn Hjaltason ne ya fara ba da rahoton ganowar a cikin wani zaure na Facebook mai suna Skordyr a Islandi (wato ƙwari a Iceland), kamar yadda Hukumar Watsa Labarai ta Iceland ta faɗa a ranar Litinin.

Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya

An miƙa samfuran ga Cibiyar Tarihin Halittu ta Iceland domin bincike, inda masanin ilimin halitta Matthias Alfredsson ya tabbatar da cewa lalle sauro ne.

An bayyana samfurin a matsayin Culiseta annulata, sauro mai jure sanyi da ake samu a arewacin Turai.

“Da alama sauron ba zai taɓa barin wajen ba,” in ji Matthias.

“Yana son ci gaba da samun ɗumi a lokacin hunturu a wurare masu inuwa kamar ɗakunan ajiya da gidajen dabbobi.”

Duk da cewa sauro na zuwa kasar Iceland a wasu lokuta a cikin tayoyin jiragen sama, wannan shi ne karon farko da aka gano sun samu wajen zama a kasar.

Masana kimiyya sun daɗe suna hasashen cewa sauro na iya samun kansa a Iceland.

Gano sauro a kasar ya jaddada yadda yanayi da sauyin muhalli ke iya faɗaɗa kewayon nau’in ƙwari masu jure sanyi fiye da kowane lokaci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 
  • Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba
  • Masu Tasiri a Kafafen Sada Zumunta sun samu horo kan RMNCAH+N, Tsarin Iyali da Rigakafin Cin Zarafin Mata
  • Gwamna Yusuf Ya Gwangwaje Kano Pillars Da Sabbin Motocii
  • Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina
  • Jihar Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 2 Wajen Binciken Albarkatun Kasa
  • An gano sauro a karon farko na tarihin ƙasar Iceland
  • Masu kwacen waya sun kashe ma’aikaciyar lafiya a Zariya