Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025
Published: 25th, October 2025 GMT
Lokacin da Etuh ya zama wanda ake maganarsa musamman ma idan an taɓo maganar Takin zamani, masana’antar ta kama hanyar lalacewa saboda ‘yan baran da sun mamaye ta, ga kuma cuwa-cuwa da ta yi wa wurin katutu, lamarin da ke sa ba a iya gane manoman gaskiya.
Duk da hakan ba ta sa Etuh ya yi ƙasa a gwiwa ba wajen haɗa kan da ya yi da gwamnatin tarayya, Etuh ya taimaka wa tsarawa da kuma gabatar da lamarin Takin zamani na Shugaban ƙasa Bola Tinubu (PFI),lamarin da ya kawo gaggarumin ci gaban aikin gona, domin kuwa an samu raguwar farashi,ya kuma samar da wata kafa inda manoma suke samun Takin zamanin kai tsaye.
Sakamakon haka ya sa yanzu an ƙara samun ci gaba, domin da farko ana da inji 1 ake amfani da shi a shekarar 2016, Nijeriya yanzu tana da injuna fiye da 70 duk kuma mashin ɗaya yanzu akwai hanyar samar da ayyuka , yin takin, da kuma bunƙasa ƙauyuka.
Kamfanin Etuh’s Mikap tare da tawagar FEPSAN sun haɗa kansu wajen samar da Takin zamani fiye da buhuna miliyan 50 na takin zamani mai suna Kamfa ko kuma NPK a ƙasa baki ɗaya, hakan ya sa an bar dogara da shigo da shi Takin daga ƙasashen waje, an kuma ceto Nijeriya daga amfani da biliyoyin Naira ta hanyar kuɗaɗen ƙasashen waje.
Taimakawa wajen yin takin zamani na gida
Hangen nesa irin na Etuh abin ya wuce maganar Takin zamani. Saboda yana son bunƙasa aikin noman ne daga ciki zuwa waje— daga lokacin shukawa zuwa har ya kai ga nuna a yi girbi a kawo gida ko kuma zuma kasuwa.
Ta hanyar Kamfanin Mikap Nijeriya, ya zuba jari na yadda ake yin Takin zamani da inji, yadda za a kai shi gida bayan an girbe, kai shi wurin ajiya, tabbatar da cewa an bar noma ta kai ga shigar kowane ɓangare na tattalin arziki.
Ganin yadda ya maida hankali ya sa gwamnatocin Jihohi suka haɗa kai da shi, ƙungiyoyin tsimi da tanaji, da kuma ƙananan Bankuna da suke harkar kuɗaɗe, suna ba da dama ta bayar da bashi ga ƙananan manoma waɗanda suka rasa waɗanda za su ba su bashi.
A kowace Jiha inda ake yin wannan tsarin, rayuwar jama’a ta inganta, matasa sun samu aikin yi, yayin da mata kuma suka samu madafar da za su tsaya da ƙafafaunsu.
Yadda ake amfana da Thomas Etuh
An raba buhunan Takin Zamani miliyan 50 a faɗin tarayyar Nijeriya
An gyara injinan yin Taki fiye da Injina 70 da kuma sake duba wasu, inda dubban manoma suka amfana da irin taimakon kai tsaye.
An samu dubban ayyukan yi sanadiyar lamarin na Takin Zamani.
An hana kashe bilyoyin kuɗaɗen ƙasar wajen da za a yi amfani da su saboda shigo da Takin da ake yi cikin gida Nijeriya wanda ake yi ta hanyar amfani da kayan gida.
Kowane ya samu wakilci ba kawai ya cancanci abin da ya samu ba, sai dai kuma babban jin daɗi— an samu ƙaruwar jin daɗin ‘yan Nijeriya.
Daga tsarin Takin Zamani na Gida Zuwa Ga Tsari Ko Manufar Nijeriya
A matsayin shi na Shugaban masu yin Takin Zamani da raba shi na ƙasa (FEPSAN), Etuh shi ya kasance murya wanda ya damu da yadda ɓangaren yake.
Ya jagoranci maganar samar da kayan da za a haɗa wajen yin Takin Zamani, domin tabbatar da cewar masana’antun kamar su limestone, urea, da phosphate sun zama sune abubuwan da za ‘a riƙa yin amfani da su wajen yin shi Takin Zamanin.
Haka nan ma shi ne jagora na kula da ingancin shi Takin Zamanin yin hakan kuma an samu maganin waɗanda suke shigo da Takin Zamani da baya da inganci. Manoma yanzu suna samun Takin Zamani wanda ya dace da yanayin da ƙasar gonarsu take da kuma irin amfanin gonar da za su shuka— domin kimiyya ta sa an bar yin cece- kuce ana amfani da zarihi ne.
Ta hanyar tattaunawar da yake yi da masu aiwatar da tsare tsare, Etuh ya taimaka wajen kawo gyara kan lamarin daya shafi Takin Zamani na ƙasa yadda za a inganta shi, wanda yanzu ɗauki matakin ya sa ana amfani da irin matakin da aka yi amfani da shi a nahiyar Afirka ta kudu da Sahara.
Abin ya wuce kasuwanci har da taimaka wa al’umma
Yadda Etuh yake manufa da sha’awa ta taimakawa al’umma domin su samu ci gaba. Ta hanyar gidauniyar Thomas Etuh, ya taimaka wa ɓangaren ilimi, lafiya, da kuma tallafa wa matasa a Jihohin Kogi, Benuwe, da kuma Nasarawa.
Ya ba da tallafin ga ɗalibai ‘yan asalin Jihar, da kuma ba su horo ta ɓangaren aikin gona, da kuma ba da tallafi domin ƙananan masana’antu inda za a riƙa sarrafa abin da aka noma saboda ƙungiyoyin mata.
A shekarar 2024, gidauniyar ta ƙaddamar da tsarin Green Rural Initiatiɓe, wanda ke da sabbin manoma — 5,000 kowace shekara. Tsarin yana nuna duk ƙaryar ci gaban Birane da ƙauyuka suke taƙama.
Shugaba mai niyyar taimako
Ya san yadda zai ja hankalin mutane ta hanyar iya maganarsa, an san Etuh kan yadda yake shirye- shiryen shi , ga shi da son taimakon al’umma da kuma haɗin kai.
Abokan harkokinsa sun shi mutum ne wanda Allah ya sa ma shi tausayi na taimakawa, sai dai kuma duk wani , matakin da zai ɗauka sai ya yi tunani tukuna—ɗa bi;un nasa su sukka sa al’umma suka amince da shi har ma tare da gwamnati.
Ya yi karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya kuma samu horo kan tsare-tsare da manufofi na manyan jami’ai a nan cikin gida da kuma waje, Etuh ya kawo ƙwararru ƙwarai da gaske zuwa ga ɓangaren waɗanda wani lokaci ba a ɗaukesu da muhimmanci ba. Manyan jami’an da yake yi aiki da su sun kwashe shekaru masu yawa a masana’antu, harkar kuɗaɗe da kuma ci gaba, amma duk da hakan babban abin da ya fi damuwa da sa shi ne ƙasar da ake yin noman a kanta, saboda ita ce babbar ma’aikatar dukiya.
Yadda ya samu jinjina daga gida da waje
A ƙarƙashin jagorancin Etuh, masana’antar takin zamani ta Nijeriya ta samu gagarumin nasara a nahiyar. Ƙungiyoyin yankin kamar irinsu Ƙungiyar Haɗin Gwiwar Takin Zamani da Kasuwancin Noma na Afirka (AFAP) da Shirin Haɓaka Noma a Afirka (AGRA) sun amince da haɗin gwiwa da Nijeriya a harkar noma da kamfanoni masu zaman kansu suka jagoranta.
Ya sama lambobin yabo masu tarin yawa a harkokin kasuwanci da samar da kayayyaki na ƙasa da ƙasa da kuma ɓangaren shugabancin noma, amma Etuh babbar bajintarsa ta fi shahara lokacin girɓin amfanin gona.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Korarren Jami’in Gwamnatin Isra’ila Ya Ce: Dole Ne A Yi Bincike Kan Sakacin Da Hamas Ta Samu Sukunin Kai HariIsra’ila
Shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila ya jaddada cewa: Dole ne a gudanar da bincike kan sakacin Isra’ila har Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023
Tzachi Hanegbi, shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila, ya yi kira da a gudanar da bincike kan bala’in gazawar da aka yi a ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023 har kungiyar Hamas ta yi nasarar aiwatar da gagarumar nasara kan Isra’ila.
Wannan ya zo ne a cikin kalaman farko da Hanegbi ya yi tun bayan da Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kore shi daga kan mukaminsa.
Hanegbi ya ce: “Netanyahu ya sanar da shi yau cewa ya kore shi daga kan mukaminsa.”
Ya kara da cewa: “Dole ne a bincika mummunan gazawar ranar 7 ga watan Oktoba domin daukar darasi da kuma taimakawa wajen dawo da amanar da ta ruguje.”
Hanegbi na daya daga cikin fitattun makusantan masu aikata laifukan yaki Benjamin Netanyahu, amma sabanin baya-bayan nan da aka samu tsakanin bangarorin biyu dangane da gudanar da yakin da ake yi a zirin Gaza ya taimaka wajen korar tasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wani Masani Dan kasar Iran Ya Samu Lambar Yabo Ta WHO A Yankin October 22, 2025 Majalisar Najeriya Ta Amince Da Dokar Daurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Kananan Yara Fyade October 22, 2025 Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda October 22, 2025 China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D October 22, 2025 Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta October 22, 2025 Sheikh Qasim: Natanyahu Ya Zubar Da Jini Mai Yawa Amma Babu Lamuni Ga Amincin Isra’ila Nan Gaba October 22, 2025 Aragchi Da Guterres Sun Tattauna Kan Gaza Da Rikicin Yemen Ta Wayar Tarho October 22, 2025 Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya October 22, 2025 Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza October 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci