Masu yabon Buhari sun yi masa ba’a bayan ya sauka daga mulki —Gwamna Sule
Published: 27th, October 2025 GMT
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce wasu daga cikin mutanen da saba yabon tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari lokacin yake kan mulki, su ne suka fara yi masa ba’a tare da suka bayan ya sauka daga mulki.
Da yake jawabi a wani taron “Lakcar Raymond Dokpesi” da Ƙungiyar Masana Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR) ta shirya a birnin Abuja, Gwamna Sule ya ce ya shaida da idonsa yadda wasu ’yan siyasa ke yabo da fadanci a gaban Buhari, amma daga bisani su sauya baki sheƙa da zarar shugabannin sun bar mulki.
Ya ce, “Tun da na zama gwamna, na ga abin da son kai da kwaɗayi ke iya haifarwa. Na ga mutane suna zaune a gaban Shugaba Buhari suna cewa, ‘Kai ka fi kowa, babu wanda zai iya yin wannan kamar kai.’
“Amma bayan saukar Buhari daga mulki, sai suka fara cewa, ‘Ai, yana cikin shugabannin mafiya rauni.’ Waɗannan mutanen ɗaya ne, amma lokaci ne ya bambanta. Wannan shi ne kwaɗayin yabo da son kai,” in ji shi.
Mai mata ɗaya abin tausayi ne — Sanata Nwoko Saukar Farashin abinci: Manoma da gwamnati na nuna wa juna yatsaA wajen taron, an karrama Gwamna Sule da kyauta da kuma lambar girmamawa ta NIPR, inda ya bayyana farin cikinsa da irin jarumtakar marigayi Cif Raymond Dokpesi, wanda ya kafa tashoshin rediyo da talabijin na farko masu zaman kansu a ƙasar tun lokacin mulkin soja.
“Ina nan ne don mu taya murna da tunawa da gwarzon kafafen yaɗa labarai. Dokpesi mutum ne mai gaskiya da jajircewa wajen faɗin gaskiya ga masu mulki, ko da a lokutan da suka fi wuya,” in ji Gwamna Sule.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Buhari yabo Gwamna Sule
এছাড়াও পড়ুন:
Kamfanin Mangal ya kori direba kan dauko yara 21 da aka kama a Kogi
An kori direban Kamfanin Simintin Mangal bayan jami’an tsaro sun kama shi da motar kamfanin dauke da yara 21 da ake zargin an yi safarar su ne daga jihohin Arewa.
Gwamnatin jihar ta ce yaran da ke tsakanin shekaru 6 zuwa 17 an kama su ne bisa sahihan bayanan sirri.
Sanawar da Kwamishinan Yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar bayan kama yaran a cikin motar ta yi zargin za a yi amfani da su wajen horar da ’yan ta’adda.
Kamfanin ya nesanta kansa daga lamarin, ya ce direban ya karya dokokin aiki, kuma ya jefa al’umma cikin haɗari.
Yara masara zuwa makaranta barazana ne ga kasa — Shettima Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashentaBabban Manajan sashin kula da mulki na kamfanin, Musa Umar, ya ce ba da izininsa direban da aka kama ya fita da motar ba, domin iya jigilar siminta kaɗai suke yi ba ɗaukar fasinja ko yara ba.
Gwamnatin Kogi ta ce za a mika yaran ga gwamnatocin jihohinsu bayan tantancewa, yayin da duk wanda aka samu da hannu a safarar zai fuskanci shari’a bisa dokokin hana safarar yara da kare haƙƙin yara.