2025-10-18@05:37:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10335
«Madagascar»:
Tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, Janar Alvin Holsey, kwamandan rundunar sojin Amurka ta Kudu, ya yanke shawarar yin murabus nan da watan Disamba, saboda takun-saka tsakaninsa da sakataren tsaron Pete Hegseth, kan rashin jituwar da aka samu game da batun ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean. Rahoton ya bayyana cewa, a...
Tawagar sun gabatar da kansu ga babban sakataren hukumar gudanarwar ci gaban Jihar Katsina, Dakta Mustapha Shehu. Tawagar sun ce ziyarar wani bangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikace-aikace domin inganta zaman lafiya da kuma sanar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira. Gwamnan Katsina ya yaba wa Bankin Duniya da ya yi...
Shugaban ya kara da cewa, aana sa ran aikin za a fara gudanar da shi ne, a zangon farko na shekarar 2026. Ya ci gaba da cewa, aikin na yiwa wadannan Tashoshin garanbawul, na daga cikin kudurorin Gwamnatin Tarayya na zamantar da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa, musamman ta hanyar samar da kayan aiki...
Shin menene makasudin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin ilimi da aka gudanar a yau? Makasudin wannan taro shi ne a fadakar da mutane ayyukan wannan hukuma ta TETFUND da take yi, sannan kuma a yi magana da wadanda suka fi amfana da shi wannan tsari na TETFUND. Kamar...
Cibiyar Tsare-tsaren Harkokin Ilimi da Gudanarwa ta Kasa (NIEPA) ta yaba da kokarin Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) wajen kare hakkokin yara na samun ilimi a Najeriya. Darakta Janar na Cibiyar, Dakta David Shofoyeke ne ya bayyana hakan yayin bude taron horaswa na kwanaki uku ga masu gudanar da shirye-shiryen...
An rantsar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaban gwamnatin sojin Madagascar, bayan ya jagoranci hamɓarar da shugaba Andry Rajoelina. Sabon shugaban Madagascar kuma ya jaddada cewa hawan sa, ba juyin mulki ba ne, domin ya samu goyon bayan kotun tsarin mulkin ƙasar. Gwamnonin APC sun yi taro a Jihar Kebbi ’Yan sanda sun...

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana October 17, 2025 Daga Birnin Sin Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki October 17, 2025 Daga Birnin Sin Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin:...
Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC) ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da kare muhimman kadarorin gwamnati a kokarinta na cimma manufar kafa ta. Kwamandan hukumar a Jihar Kaduna, Malam Panam Musa, ya bayyana haka yayin da yake gabatar da wasu mutane uku da ake zargi da lalata kayayyakin gwamnati a gaban manema labarai a...
Sanarwar ta ce: “Sauya wurin da aka yi wa fursuna Malam Abduljabbar Nasiru Kabara zuwa daya daga cikin cibiyoyin tsarewa da ke karkashin ikon tarayya hanya ce ta gudanar da aiki ta yau da kullum wacce aka yi bisa ga dokokin aiki da ka’idojin hukumar.” Ta kara da bayanin cewa motsa fursunoni daga cibiyar...
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnonin Jam’iyyar APC sun gudanar da wani taron sirri a gidan gwamnati da Jihar da ke Birnin Kebbi. An bayyana cewa aƙalla gwamnoni 20 daga cikin gwamnoni 24 na jam’iyyar ne suka gudananar da taron ƙarƙashin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma, wanda shi ne gwamnan Jihar Imo. Gwamnan Gombe ya...

Kwamandan Dakarun Sa Kai Na Iran Ya Bayyana Cewa: Iran A Yayin Yaki Da Isra’ila Ta Tarwatsa Wasu Muhimman Wurare 21
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tarwatsa wasu muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya a lokacin yakin 12 Kwamandan Dakarun sa-kai na Basij Birgediya Janar Gholamridha Sulaimani ya bayyana cewa: Tunanin kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yakin kwanaki 12 da aka yi, wauta ce ta makiya yahudawan sahayoniyya, wadanda suka gaza...

Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka
Abokan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa: Sake dawo da takunkumi bayan karewarsa baya da wani tushe na doka ko tsari Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa game da cikar kudiri mai lamba 2231 kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran a ranar 18 ga watan Oktoba, inda ta...

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana
Sabbin alkaluman da babbar hukumar kula da haraji ta kasar Sin ta bayar yau 17 ga wata sun nuna cewa, a cikin watannin tara na farkon bana, kamfanoni sun kara zuba jari wajen kirkire-kirkire, kuma sabbin masana’antu bisa manyan tsare-tsare sun ci gaba da habaka. Lamarin da ya shaida cewa, ana samun ci gaba cikin...
Kasar Iran ta yi Allah wadai da harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankin kudancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai a wurare da dama a kudancin kasar Lebanon. Ya jaddada cewa, sun biyo bayan yadda...
Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su matsa wa haramtacciyar kasar Isra’ila lamba kan aiwatar da sharuddan yarjejeniyar Gaza Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su ci gaba da taka rawa wajen bin diddigin aiwatar da sauran tanade-tanaden yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, musamman ma wadanda...
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da shirin AGILE na tallafin karatun yara mata da tallafin gyaran makarantu, domin inganta ilimi a faɗin jihar. A wajen bikin da aka gudanar a Otal ɗin Custodian, Gwamna Inuwa, wanda Mataimakinsa Dakta Manasseh Jatau, ya wakilta, ya ce gwamnati na da niyyar kawar da duk wani...

Zanga-Zangar Miliyoyi A Yemen Ta Jaddada Alkawari Ga Shahidai Da Ci Gaba Da Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu
Zanga-zangar miliyoyin mutane a birnin Sana’a na sabunta alkawarin da aka yi wa shahidai tare da tabbatar da shirin tallafawa Falasdinu Babban birnin kasar Yemen, Sana’a, ya halarci wani tattaki na miliyoyin mutane a yau Juma’a mai taken “Shekaru biyu na bayar da gudummawa… da aminci ga jinin shahidai”, tare da tabbatar da gwagwarmaya na...
Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da wasu manyan kwangiloli da kudinsu ya haura Naira Biliyan 6, domin karfafa bangarorin noma, ilimi da ci gaban tattalin arziki a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar da aka gudanar a fadar gwamnatin Dutse, kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth October 17, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika October 16, 2025 Daga Birnin Sin...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta fara aiki kan dokar da za ta kafa wuraren tsaro (safe spaces) a makarantu domin karfafa ilimin yara mata a jihar. Shugaban Kwamitin Ilimi, Honarabul Mahmud Lawal, ya bayyana hakan a babban taro kan Ilimin Yara Mata da aka gudanar a Zariya, wanda Cibiyar Kula da Ilimin Yara Mata (CGE)...
An tsara fara sauraron ƙarar a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2025, a gaban Mai Shari’a Yusuf Ubale. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025...
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, inda ta gudanar da samame a wata maɓoya da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da safarar ƙwayoyi a cikin jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ta bayyana...
A taron majalsar zartarwar, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa zabinsa na Amupitan ya yi ta’allaka ne a kan rashin nuna son kai na siyasa, gaskiya da kyakkyawan tarihinsa. Mambobin majalisar, ciki har da shugabanni na yanzu da na baya, sun amince da nadin, suna bayyana Farfesa Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya....

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
Dangane da harajin 100% da Amurka ta sanya wa kayayyakin Sin, He Yongqian ta ce, Sin ba ta ji dadin matakan na Amurka ba, kuma tana adawa da su da babbar murya. Ta kuma yi fatan Amurka za ta dauki kyawawan sakamakon tattaunawar ciniki da kasashen biyu suka samu da daraja, ta kuma gyara...
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta sanar da nadin CP Dantawaye Miller a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja. Ya karɓi ragamar aikin ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Oktoba, 2025, daga hannun CP Ajao Adewale, wanda Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun, ya sauya wa wajen aiki. Wani mutum...
Dantsoho ya sanar da haka ne, bayan kaddamar dashi a matsayin Mataimakin Shugaban Kungiyar a kwanan baya a wani taro kan harkokin Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya da aka gudanar. Kazalika, Dantsoho ya ci gaba da cewa, zai mayar da hankali ne, kan wanzar da tsarin da NPA, ta sanya a gaba da kara...
Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo, ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lawal Faruƙ da ake zargin ya bankawa tsohuwar masoyiyarsa wuta bayan da dangantakar su ta yi tsami. Majiyar PUNCH Metro ta samu labarin a ranar Alhamis cewa, lamarin ya faru ne a barikin sojoji da ke Ibadan babban birnin jihar. Jami’an tsaro...
An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa. Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana. Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya...
Abin da ya rage yanzu shi ne za a zuba ido don ganin irin sauyin da zai kawo na tsaro a birnin tarayyar, sakamakon taɓarɓarewar tsaro da ya addinin garin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 Manyan Labarai Shugaban Ƙasa...
Jami’an tsaro a Jihar Kogi, sun kama wasu ’yan bindiga biyu da suka ji rauni tare da likitocin bogi da ke yi musu magani. Hakazalika, sun lalata sansaninsu a lokacin da suka kai musu farmaki. Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay Akwai yiwuwar...
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bi sahun dan rajin kare hakkin dan adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin jagoran kungiyar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu. A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na D, Atiku, ya bayyana ci...
Iyalan marigayi Herbert Macaulay sun soki matakin gwamnatin tarayya na haɗa sunan fitaccen ɗan gwagwarmayar cikin riƙaƙƙun masu laifi a jerin waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa bayan ransu. A wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas ranar Alhamis, iyalan tare da goyon bayan dattijo kuma Atona Oodua na Yarabawa,...
Rahotanni sun bayyana cewa marziyeh Ja’afari ta kafa tarihi inda ta samu kyautar da hukumar kwallon kafa ta asiya ke bayarwa , inda ta zama kociyar da ta kasance zakara a wannan shekara, yayin da Salar Aghapur kuma ya zamo gwarzo a bangare kwallon Fustal na shekara ta 2025 da hukumar AFC ke bayarwa a...
Majalisar koli ta sisaya ta kasar yamen ta sanar da nada major janaral Yousef hassan al-Madani a matsayin sabon babban hafsan hafsoshin sojin na kasar Yamen , inda ya gaji Janaral Mohammad Abdulkarim Al-Ghumari wanda yayi shahada a baya bayan nan sakamakon Harin da sojojin HKI suka kaddamar kan kasar ta yamen. Wannan sabon nadi...
Baya ga yi masu afuwa, Shuagaba Tinubu, ya kuma karama su da lambar yabo ta kasa. ‘Yan Ogonin su tara, sun dai fuskanci shari’a ne, bisa zarginsu da kitsa kisan sarakunan Ogoni Albert Badey, Edward Kobani, Theophilus Orage da kuma Samuel Orage. Kotu ta tuhumi ‘yan Ogonin su tara, ta kuma yanke masu hukuncin rataya...
Rahotanni sun bayyana cewa shakih Naim Qassim babban sakatare janar din hizbullah na kasar labanon ya bayyana a jiya Alhamis a gaban mambobin kungiyar Kashafat Al-Mahadi cewa Amerika da Isra’ila ba za su iya yin galaba akan hizbullah ba, Babban hadafin kafa wannan kungiyar shi ne kokarin wayar da kan yara matasa yan shekara 6...
Majalisar Dattawan ta Najeriya ta tabbatar da naɗin Farfesa Joash Amupitan, mai mukamin SAN, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a yammacin ranar Alhamis. Tabbatar da Farfesa Amupitan, ta kasance ta hanyar kuri’ar murya da ‘yan majalisar suka gudanar bayan kammala tantance shi tare da amsa tambayoyi daga mambobin...
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, taron goron gayyata ne na kafa Nijeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi tare da sabuntawa a Afirka, sannan kuma sauyin da aka samu na makamashi Nijeriya, ya bayar da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410, daga tsakanin yanzu zuwa shekarar 2060. Ya kara da cewa,...
Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin. Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin...
A baya- bayan nan ‘yan ta’addan wadanda suka daura damarar hanawa al’umma kwanciyar hankali sun kashe daruruwan mutane, kona gidaje tare da garkuwa da mutane ciki har da mata da kananan yara. Rahotanni daga yankunan sun tabbatar da yadda al’umma suka gaji suka kosa da jin alkawura marasa adadi daga gwamnati wadda ke kasa cikawa...
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin...

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da KuraAfuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da Kura
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin...
Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Israel Sunny-Goli, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ya guji duk wata matsin lambar da wasu ƴan siyasa ke yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Sunny-Goli ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin halartar shirin Politics Today na tashar Channels,...
Kasar Saudiyya ta rage yawan guraben kujerun aikin hajjin da take ware wa Najeriya daga 95,000 zuwa 66,910 daga shekarar 2026. Aminiya ta ruwaito cewa a baya Najeriya ta shafe tsawon shekaru uku tana samun guraben na 95,000 a yayin Aikin Hajjin. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara...
Shugaban kasar ta Sudan Janar Abdulfattah al-Burhan ya ziyarci Masar inda ya gana da takwaransa Janar al-Sisi, inda su ka tattauna halin da ake ciki a Sudan, da kuma matsalolin da yankin yake fuskanta. Haka nan kuma bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi akan madatsar ruwan kasar Habasha da Masar take da sabani da Addis...
A jiya Alhamis jiragen yakin HKI sun kai hare-hare na wuce gona da iri garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahada da kuma jikkatar mutane da dama. Majiyar tsaro daga kudancin Lebanon ta ambaci cewa, mutum daya ya yi shahada yayin da wasu 7 su ka jikkata. Hare-haren sun shafi garin...
Jaridar Wall Street Jouranl ta kasar Amurka ta buga labarin da yake cewa, kasar Amurka ta fada girke makamai a kusa da tekun Caribbean da kuma wasu jiragen sama a arewacin kasar Venezuela. Labarin ya kara da cewa;Rundunar da ma’aikatar yakin Amurka ta “Pentagon” ta girke ta zaratan mayakan kundunbala ce wacce ta kashe Usama...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya wallafa sako a shafinsa yana cewa ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Vladmir Putin yakan yiyuwar za su gana da juna a birnin Bhudapast na kasar Haugary, domin lalubo hanyar kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban kasar na Amurka ya kuma bayyana tattaunawar da su ka yi a jiya...
A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da...
Aƙalla jami’an tsaro takwas, ciki har da ɗan sanda guda ɗaya da masu tsaron al’umma bakwai, sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da aka kai musu a hanyar Gusau–Funtua da ke Jihar Zamfara a ranar Alhamis. Lamarin ya faru ne a lokacin da gamayyar jami’an tsaro, waɗanda suka haɗa da ’yan sanda da...