Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila
Published: 14th, October 2025 GMT
Rahotanni sun bayyana cewa wani ƙazamin faɗa ya barke tsakanin wata ƙabilar Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da ƙungiyar Hamas a yankin zirin Gaza bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila.
A ranar Litinin da aka fara musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ne rahotanni suka ɓulla game da faɗan da ya ɓarke tsakanin mayaƙan Hamas da ƙabilar Doghmush a ranar Lahadi.
Wani jami’in Hamas ya bayyana cewa an samu asarar rayuka daga kowane ɓangare a yayin musayar wutan daga misalin ƙarfe 9.30 na dare ranar Lahadi.
Wani mazaunin yankin Sebra da ke Birnin Gaza, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa “Mayaƙan Hamas kimanin 200 ne suka zo aka fafata da su, har sai da suka murƙushe ’yan ƙabilar Doghmush.
Issa Bakary Tchiroma ne ya lashe zaɓen Kamaru —’Yan adawa NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Ta Yajin Aiki?“Wasu ’yan ƙabilar da mayaƙan Hamas sun rasu a yayin artabun,” in ji shi yana mai neman a dakata sunansa saboda dalilan tsaro.
Wata majiya daga ma’aikatar harkokin cikin gida ta Hamas ta zargi ’yan ƙabilar da yi wa sojojin Isra’ila aiki kuma sun kashe mutane da dama, ta ƙara da cewa an tsare mutum shiga daga danginsu.
Iyalan sun musanta zargin da ake musu na yi wa Isra’ila aiki, amma sun amsa cewa sun kai wasu farmaki ba tare da yin ƙarin haske ba.
Sun kuma zargi Hamas da kai musu hari barkatai, kamar yadda AFP ya ruwaito.
Shugaban kabilar, Abu al-Hassan Doghmush, ya wallafa a Facebook cewa abin “ya kai matakin da in dai kai dan ƙabilarmu ce to a iya harbin ka a ƙafa koma kone maka gida.”
Tun da Hamas ta kwace iko a yankin Gaza a 2007 ta sha fama da kabilu da ƙungiyoyi masu ɗaukar makamai.
A ranar Lahadi ne kungiyar ta sanar da afuwa ga duk kungiyoyin masu laifi, waɗanda ba su aikata kisa a lokacin yaƙin ƙasar da Isra’ila.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies.
Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci.
An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara baDokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci gaba ɗaya.
Indonesia na daga cikin ƙasashen da har yanzu ake cin naman karnuka da kyanwa, duk da cewa wasu birane sun daina wannan al’ada a ’yan shekarun nan.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi sun yaba da sabon matakin, suna mai cewa ya dace da manufofin kare lafiyar al’umma.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce mutane da dama kan mutu da cutar rabies a kowace shekara a Indonesia, inda rahoton Ma’aikatar Lafiya ya nuna cewa mutane 25 suka mutu daga watan Janairu zuwa Maris 2025.
Duk da cewa a yawancin yankunan Indonesia ana kallon karnuka a matsayin dabbobin da ba su da tsabta, wasu ƙananan ƙabilu na ci har yanzu, musamman ma saboda samun naman a farashi mai sauƙi.