Leadership News Hausa:
2025-10-24@10:27:40 GMT

Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Published: 23rd, October 2025 GMT

Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa a ranar 16 ga watan Oktoba.

Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin? Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja 

A yayin taron, Shugaba Tinubu ya buƙaci Farfesa Amupitan da ya tabbatar am gudanar da sahihancin zaɓe a Nijeriya tare da inganta INEC domin tabbatar da gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci.

An tabbatar da naɗin Amupitan bayan Majalisar Dattawa ta tantance shi, inda ta tabbatar da cewa yana da ƙwarewa da hangen nesa wajen gudanar da ayyukan hukumar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki  October 22, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jihar Kaduna Sun Yabawa Gwamna Sani Kan Amincewa Da Sabon Albashin  Ma’aikata

“Shirin gwamnan na aiwatar da sabon tsarin albashi duk da ƙalubalen tattalin arziki ya nuna tausayinsa, gaskiya, da girmama kimar ma’aikata,” in ji shugabannin kungiyoyin.

 

Kungiyoyin sun kuma yaba da kokarin gwamnatin wajen gyara da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya inda suka bayyana gyaran da sabunta azuzuwan karatu a dukkan kananan hukumomi 23, amincewa da tsarin ritaya bayan shekaru 65 ko shekaru 40 na aiki ga malamai, da kuma dawo da sama da naira miliyan 500 na ajiyar ( ENDWELL) da aka rike a baya, a matsayin muhimman nasarori.

 

Ma’aikatan sun kara jinjina wa dawowar tsarin biyan gudunmawar adashin gata na malaman makaranta wato (ENDWELL) na kowane wata, inda suka bayyana cewa tsarin yana taimakawa wajen inganta walwalar malamai da iyalansu. Haka kuma sun yaba da gyaran da gwamnati ta yi wajen biyan kudin kungiyoyi da kuma nasarar tantance ma’aikata wanda ya kara gaskiya da tsari a cikin aikin gwamnati.

 

A fannin lafiya, kungiyoyin sun yaba da sauye-sauyen da Gwamna Uba Sani ya aiwatar, ciki har da farfado da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 255 (PHCs), kafa cibiyoyin kwarewa guda 23 na PHC, da kuma shirin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 a duk shekara na tsawon shekaru biyar.

 

Haka kuma shugabannin ma’aikatan sun jinjina wa gwamnan bisa kaddamar da motocin bas masu aiki da iskar gas (CNG) guda 100 domin bayar da kyautar sufuri ga ma’aikata da dalibai, suna bayyana wannan shiri a matsayin wani mataki na taimakawa wajen rage radadin cire tallafin mai da sauƙaƙa rayuwar jama’a.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala October 24, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Tafka Ɓarna A Kasuwar Shuwaki, Ta Ƙona Fiye da Rumfuna 500 A Kano October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu October 24, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jihar Kaduna Sun Yabawa Gwamna Sani Kan Amincewa Da Sabon Albashin  Ma’aikata
  • Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027
  • Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
  • Babban Lauyan Jihar Kwara Ya Tabbatar da Gudanar da Adalci da Kare Hakkokin Mace
  • Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 
  • Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo
  • Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni
  • Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi
  • Tinubu ya naɗa sabon Minista