Aminiya:
2025-10-18@06:40:15 GMT

Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka

Published: 18th, October 2025 GMT

Jakadan Amurka na Musamman kan Harkokin Larabawa da Afirka, Massad Boulos, ya ƙaryata iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya babu gaira babu dalili.

Ya ce hare-haren ta’addanci da ke faruwa a ƙasar suna shafar Kiristoci da Musulmai baki ɗaya.

An rantsar da Randrianirina shugaban Madagascar Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun yara mata

Boulos, wanda mashawarci ne ga Shugaban Amurka Donald Trump, ya faɗi hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Jumma’a.

Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka sun nemi gwamnatin Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashe masu hatsari wadda ake zaluntar Kiristoci.

Sai dai Jakadan ya ce lamarin ba haka yake ba.

“Waɗanda suka san Najeriya sosai sun fahimci cewa ta’addanci ba shi da launi, addini, ko ƙabila,” in ji Boulos.

“Kungiyoyin Boko Haram da ISIS sun kashe Musulmai sama da Kiristoci. Mutane daga kowane ɓangare na fama da wannan tashin hankali. Ba a iya wani ake kai wa hari ba.”

Ya bayyana cewa rikicin da ake samu a Arewa ta Tsakiya a Najeriya, rikici ne tsakanin manoma da makiyaya, wani lokaci yana shafar Kiristoci, amma asalin rikicin yana da nasaba da harkar noma, ba addini ba.

“Ba shi da nasaba da addini,” in ji shi.

“Najeriya ƙasa ce da ta ƙunshi ƙabilu da addinai da dama waɗanda suke zaune tare tsawon shekaru. Bai kamata a juya wannan matsala zuwa ta koma ta addini ba.”

Boulos, ya kuma yaba wa gwamnatin Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarin da ta ke yi wajen inganta tsaro, inda ya ce sakamakon ƙoƙarin ya fara bayyana.

Maganar “kisan gillar Kiristoci” a Najeriya ta ƙara yawaita ne bayan jawabin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA).

A yayin taron ya yi kira da a samar da zaman lafiya a Gaza da kuma goyon bayan tsarin ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Falasɗinu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: rikicin manoma da makiyaya taro tattaunawa

এছাড়াও পড়ুন:

FMC Birnin Kudu Ya Yi Bikin Ranar Maganin Kashe Radadi Ta Duniya

Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana.

Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata Oktobar kowacce shekara domin bikin wannan rana.

Shekaru 170 ke nan da fara amfani da maganin kashe radadi, inda wasu likitoci su ka yi gwajin wannan magani a asibitin birnin Massachusetts na kasar Amurka, abin da ya kawo sauyi wajen yi wa marasa Lafia aikin tiyata daga shekara 1846.

Malam Aliyu Umar Yusuf na sashen bada maganin kashe radadi na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu ya ce taken ranar bikin na bana shi ne “Muhimmancin aikin kashe radadi a yanayin da ake bukatar agajin gaggawa” abin da yasa su ka yi amfani da wannan dama wajen shirya bita ga jami’an hukumar kiyaye hadura na karamar hukumar Birnin kudu kan hanyoyin lalubo numfashin wanda ya suma saboda bugun zuciya ko hadarin mota.

Da ya ke gabatar da bitar a aikace, Shugaban Sashen bada maganin kashe radadi lokacin aikin tiyata na asibitin gwamnatin tarayya dake Birnin kudu, Dakta Oliwe Augustus Chuks, ya ce akwai matakai da dama da ake bi wajen lulubo numfashin wanda ya yanke jiki ya fadi sumamme.

Yana mai cewar wadannan hanyoyi sun hada da tabbatar da yiwuwar bada agajin gaggawa lami lafia kafin taba jikin maras lafiya, da neman taimakon jama’a dan ceton rai da kuma danna kirjin wanda ya suma a hankali dan jini ya gudana daga zuciya zuwa kwakwalwa.

Yace sai kuma hura iska a baki domin bude kafofin da su ka toshe da motsa kashin mukamuki dan bude kofofin shan iska wadda hakan zai kai ga dadowar numfashi.

Sai dai kuma Likitan ya yi kira ga jama’a a tashar mota da makarantu da gidaje da su lakanci dabarun lalubo numfashin wanda ya suma domin kuwa wannan ilimi bai takaita ga likitoci kadai ba har ma da gamagarin mutane dan ceto rai kafin zuwa asibiti.

A nasa bangaren, Jami’in hukumar kiyaye hadura ta kasa na karamar hukumar Birnin Kudu, Malam Shu’aibu Uba Baba, ya bayyana jin dadin sa bisa wannan bita da ma’aikatan bada maganin kashe radadi lokacin aikin tiyata na asibitin FMC da ke garin Birnin Kudu su ka shirya musu.

Ya lura cewar, bitar za ta sake inganta abin da su ka sani wajen bada agajin gaggawa lokacin hadarin mota, inda ya roki ma’aikatan asibitin da su ware lokaci domin ci gaba da yi musu irin wannan bita nan gaba.

Taron ya samu halartar kungiyar kiyaye hadura ta masu yiwa kasa hidima, inda aka bada damar tambayoyi da bada amsa yayin da wasu daga cikin ma’aikatan hukumar kiyaye hadura da na masu yiwa kasa hidima suka jarraba matakan da likitocin su ka koyar da su muraran a aikace.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An rantsar da Randrianirina shugaban Madagascar
  • Zanga-Zangar Miliyoyi A Yemen Ta Jaddada Alkawari Ga Shahidai Da Ci Gaba Da Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu
  • Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
  • Hizbullah: Amurka ِDa Isra’ila Ba za Su Iya Yin Nasarar Akanmu ba.
  • FMC Birnin Kudu Ya Yi Bikin Ranar Maganin Kashe Radadi Ta Duniya
  • Pezeshkian Ya Yi Gargadi Akan Makircin Makiya A Tsakanin Al’ummar Musulmi
  • Majalisar Dattawa ta amince da Amupitan Shugaban INEC
  • An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato
  • Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles