2025-12-10@02:23:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1283
«Jirage Marasa Matuƙa»:
Kananan yara sama da 93,200 ne ake sa ran yiwa allurar rigakafin cutar shan Inna da ake gudanarwa a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Kazalika, kananan yara sama da 53,800 ne ake sa ran digawa sinadarin vitamin A a yankin. Shugaban hukumar lafiya matakin farko na yankin Aminu Abubakar Kwandiko ya yaba da yadda...
Firai ministan kasar Iraki Mohammad Shia Assudani ya bayyana cewa gwamnatinsa bata tushe asusun kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon da kuma Ansarallah ta kasar Yemewn ba. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran IP ya nakalto sudanina cewa gwamnatinsa tana kokarin hana tasowar wani riki a yankin sannan da kuma kaucewa duk wani rikicin siyasa...
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana sabbin dabarun tsaron Amurka na cimma maradun gwamnatin Isra’ila ne. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce sabbin dabarun tsaron Kasa na Amurka (NSS) da ke bayyana ka’idojin Washington da muhimman manufofin harkokin waje a zahiri cimma maradun tsaro ne ga gwamnatin Isra’ila ne. Esmaeil Baghaei ya yi wannan...
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a...
Tom Barrack jakadan Amurka na musamman a kasar Siriya ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta yi kokarinkifar da gwamnatin JMI a baya har sau biyu amma ta kasa yin haka. Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Barrack yana fadawa wani kamfanin dillancin labaran UAE a ranar jumma’an da ta gabata, ya...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya yi tir da kungiyar kasashen larabawa na yankin tekun Farisa, wadanda suka fidda bayanin bayan taronsu a baya bayan nan suka allawadai da kuma nuna goyon bayansu ga kasar UAE kan mallakar tsibiran Tumb babba da tumb karami da Abu Musa. Kamfanin dillancin labaran IP na...
Kungiyar ‘yan wasan ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda...
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada...
Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano. An gurfanar da shi ne a kan zargin...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya yi tir da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka take ci gaba da dorawa JMI na shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada nakalto Baghaei yana fadar haka a dai dai ranar tunawa da ranar haramcin takunkuman tattalin arziki na bangare...
Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale
Hassan Fadlallah wanda dan majalisar kasar Lebanon ne daga kungiyar Hizbullahy a bayyana cewa; gwargwadon yadda ake ja da baya a gaban makiya, suke kara samun karfin gwiwa,don haka da akwai bukatar hadin kai a tsakanin kasashen larabawa da na musulmi domin fuskantar kalubalen dake gaba. Shi dai Hassan Fadlalalah yana halartar taron majalisun kasashe ...
Rahotanni daga kasar Lebanon sun ambaci cewa da marecen yau jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare a garuruwan Mahruna,jibaa, Bar-ishit da Majadil dake kudancin Lebanon. Hare-haren sun rusa gidaje da dama na garuruwan da su ka kai wa harin. Wannan harin dai yana faruwa ne kwana daya bayan da Lebanon ta aike da...
Iran ta yi watsi da zarge-zargen da wakilan gwamnatin Isra’ila da gwamnatin Yemen mai murabus suka yi a zaman taron hukumar kula da harkokin teku ta duniya (IMO) karo na 34. A wata wasika da ta aike wa Sakatare Janar na IMO Arsenio Dominguez, Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kungiyar da ke Landan...
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na shirin sayen jirage marasa matuƙa da wasu kayan aiki domin kare yankunan da ke iyakar Kano da Katsina. Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja CBN ya...
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana aniyar maka hamshakin kamfanin nan na hakar uranium na faransa (Orano) a gaban kotu bayan gano sinadarai masu guba a yankin Madaoulela, dake arewacin kasar. Dama dai Nijar da Orano sun sun shafe watanni suna takaddama kan sinadarin uranium da ake fitwarwa a kamfanin Somaïr, wanda aka mayar da shi...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Sharhin bayan labarai, wand ani tahar amin zan karanta. A cikin shirimmu na yau zamu yi Magana dangane cewa, shin gaskiyar ne ‘HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran...
Daga Abdullahi Jalaluddeen Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da babura a fadin jihar. Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya...
Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai...
Wata fitacciyar sinima a Faransa, Cinematheque Francaise, ta rufe ɗakunan kallonta na tsawon wata guda saboda yaɗuwar kuɗin cizo da aka gano a cikinta Cibiyar wadda ke gabashin birnin Paris ta ce rufe sinimar zai ba ta damar tabbatar da cewa masu kallo sun samu “aminci da kwanciyar hankali” bayan ƙorafe-ƙorafen da aka yi na...
Babban kwamandan sojojin kasa na JMI Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su maida martani ko kuma kai hari kan makiya a duk lokacinda suka takali kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hatami yana fadar haka a bikin kaddamar da jiragen ruwan yaki masu suna...
Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara. A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon ta sanar a ranar Juma’a cewa ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da gina katanga biyu na siminti a cikin yankin Lebanon da ke kudu da garin Yaroun (yankin Bint Jbeil). A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar ta ce tawagar Jakadancin...
Rahotanni sun bayyana cewa kasashen larabawa na tekun fasha da kuma kasar Iran sun yi tir da hare-hare ta kasa da sojojin isra’ila suka kai a wasu yankuna dake kudancin kasar Siriya kamar su bait jinn da ya kai ga mutuwar mutane 13 ciki har da yara kanana. A cikin bayani da ya fitar a...
Iran Za ta Kauracewa taron fasalta kasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya na shekara ta 2026
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa za ta kauracewa taron da za’a yi a makon gobe a birnin Washington bayan da kasar Amurka ta ki yarda ta bada shedar izinin shiga kasar ga wasu daga cikin wakilanta Kakakin hukumar kwallon kafa ta kasar iran yace mun riga mun...
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya. CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan...
Kasar Portugal ta kafa tarihi a birnin Doha na Qatar bayan da ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 (U-17) a karon farko, inda ta doke Austria da ci 1-0 a wasan ƙarshe. An jefa ƙwallon da ta bai wa Portugal nasara ne ta hannun Anisio Cabral, wanda ya ci a minti...
Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai. Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila Katz, ya yi gargadin cewa Tel Aviv a shirye take ta kaddamar da wani sabon yaki kan kasar Labanon matukar kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta ki mika makamanta zuwa karshen shekarar...
Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas. Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta. El-Rufai ya koma...
Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata (AGILE) a yankin. Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan...
Babban sakataren tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani a shafinsa na X ya soki siyasar Amurka a lokacin ziyararsa a kasar Pakistan kuma ya jaddada cewa Tehran tana son ayi gaskiya a duk tattaunawa da za’a yi. Kalaman na larijani yana nuna matsayar iran ne kan diplomasiyar iyakoki, yace yanci da mallaka wasu abubuwa ne...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara a wasan mako na 14 na Nigeria Premier Football League (NPFL), bayan da ta doke Ikorodu City da ci 2–1 a filin wasa na Muhammad Dikko, da ke birnin Katsina. Wannan ita ce nasara ta uku da Pillars ta samu a kakar bana, cikin wasanninta 14,...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea za ta karɓi baƙuncin Barcelona a wasan mako na biyar na gasar cin Kofin Zakarun Turai (Champions League) da ke ci gaba da gudana a kakar nan. Wasan da za a buga a filin Stamford Bridge, yana zuwa ne bayan da ’yan wasan Barcelona suka ƙauracewa atisayi a bainar jama’a...
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan. A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila. Mayaƙan...
Ɗalibai 50 da aka sace a Makarantar St. Mary’s da ke garin Papiri, a Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja, sun tsere daga hannun ’yan bindiga. ’Yan bindigar da suka sace su, sun kai hari makarantar da safiyar ranar Juma’a. Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji An rufe duk...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ’yan awaren ƙungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu. Obi ya bayyana hukuncin matsayin “abun takaici” kuma alamar gazawar jagoranci. Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin...
Kwamandan sojan kasa na Rudnunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgerdiya Janar Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin kasar a shirye suke su mayar da martani akan duk wata barazana daga abokan gaba saboda suna da zaratan mayaka da kuma sabbin makamai.” Har ila yau Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin za kuma su yi amfani da...
Gwamnatocin jihohin Katsina da Taraba sun ba da umarnin rufe makarantu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka sace daruruwan ɗalibai a makarantu a cikin mako guda a jihohin Kebbi da Neja. Gwamnatin Jihar Taraba ta rufe makarantun kwana a fadin jihar, inda ta ba da umarnin a koma tsarin jeka-ka-dawo sakamakon tabarbarewar tsaro. Gwamnan Agbu...
Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta...
Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da...
Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai ’yan mata 24 a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin tallafin hadin gwiwa na kowace shekara domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana...
Iyalan Waɗanda Aka Kashe Yayin Zanga-zangar Bangladesh Sun Yi Maraba Da hukuncin Kisan Tsohuwar Firaminstar
Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga,...
a Rahotanni sun nuna cewa kungiyar gwagwarmaya Ta hamas ta yi gargadi game karuwar hadari bayan mutuwar falasdinawa guda 28 sakamakon harin da sojojin HKI suka kai a yankin Gaza, da hakan yake kara lalata yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakani. Akwai yara guda 9 daga cikin wanda harin na isra’ila...
An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen...
Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga...
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya {IAEA} ya bayyana cewa: Suna tuntubar Tehran kuma masu binciken hukumar sun koma kasar ta Iran Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya tabbatar da komawar masu binciken Hukumarsa ta IAEA zuwa Iran da kuma ci gaba da duba wasu wurare da...
Masu gangamin da adadinsu ya kai 100 sun tsaya a gaban babbar kofar shiga wurin taron kare muhalli na MDD da aka bude a garin Belem dake yankin Amazon na Brazil. Sojojin kasar Brazil sun bai wa masu gangamin kariya, tare da kaucewa yin taho mu gama saboda su sami damar isar da sakonsu akan...
Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a...
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba. ’Yan Majalisar...