Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga
Published: 23rd, October 2025 GMT
Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kama ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore, bisa ci gaba da zanga-zangar neman a saki shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Sowore, wanda aka kama a ranar Alhamis a birnin Abuja, wasu jami’ai dauke da bindiga ne suka yi masa dirar mikiya, sannan suka tafi da shi zuwa wani wuri da ba a bayyana ba tukuna.
Lauya mai kare haƙƙin ɗan adam kuma mai rajin kare ’yancin jama’a, Deji Adeyanju, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu.
“Eh, Sowore yanzu haka ’yan sanda sun kama shi,” in ji shi.
Har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa aka kama shi ba, amma an ji wasu daga cikin jami’an na cewa an tafi da shi ne saboda ci gaba da tayar da hankalin jama’a.
A ranar Alhamis ce dai Sowore ya jagoranci shirya zanga-zangar neman a saki mai fafutukar neman kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu, inda daga bisani jami’an tsaro suka tarwatsa su.
Bayan kammala zanga-zangar dai, jami’an tsaron sun kuma kama kanin Kanu da kuma lauyansa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini
Majalisar Dokokin Amurka ya iso Abuja yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma zargin tauye haƙƙin addini.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba.
“Tawagar ta ƙunshi ‘yanmajalisar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” in ji Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta.
Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar.
A cewar Ribadu, tattaunawar ta mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, tabbatar da zaman lafiyar yanki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka.