Leadership News Hausa:
2025-10-25@10:45:51 GMT

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Published: 25th, October 2025 GMT

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Rashin Biyan Yan-fansho Bisa Lokaci

Ta tabbata a lokacin mulkin Kwankwaso, “yan fansho a Kano, kan jira tsawon Watanni zuwa Shekaru ba tare da an biya su hakkokinsu na barin aiki ba. Haka ɗan-jummai Ganduje, yakan dan fara biyan hakkokin “yan fanshon, sai kuma a ga ya watsar. Sai a dauki tsawon lokaci yana ɓaɓatun za a ci gaba da biya, amma sai a ji shiru.

Sai aka wayi gari karɓar fansho, musamman giratuti, ya zama tamkar tafiya Lahira, yau ne? Gobe ne? Babu wata cikakkiyar amsa!. Haƙiƙa kwata-kwata babu tausai, mutane sun kwashe akasarin Shekarunsu na haihuwa suna masu hidimtawa ƙasa dare da rana, cikin yanayi na sanyi, ruwan sama da garjin rana, dole ne su fito, su aje komai su tai wurin aiki. Gashi yau sun kammala wancan aiki lafiya ba tare da an caje su da wani laifi na cin-amanar Kasa ba, amma an ci moriyar guga tare da tasamma ya da kwaurenta!!!.

Jigata “Yan-fansho Da Sunan Tantancewa

Ta faru a lokacin Kwankwaso, sai a ɗauki tsawon lokaci a na tantance “yan fansho, tantancewar dake sake haifar musu da wasu miyagun yanayai abin tausayi. Akan nemi duk tsufan mutum, ko duk zafin cuta da yake dauke da ita, sai ya zo wajen tantance sunayen “yan-fanshon. Halifansa Ganduje, shi ma ya yi matuƙar amfani da irin wannan salo na Kwankwaso, na yunkurin tantance tsoffin ma’aikatan. Babban ƙalubale da irin tantance “yan-fanshon nasu ke da shi shine, sai a dauki dogon lokaci a na ɓurarin tantance yan-fanshon, amma a karshen lamari, babu biyan bukata, domin kuwa ba a ci gaba da ba su hakkokin nasu, wahalar yau daban, ta gobe daban. Zafin rana, bugun ruwan sama da turmutsun bin layin fansho da giratuti a Kano lokacin Ganduje da Kwankwaso, ya jaza kara cuta ga masu dauke da tsananin cuta, wasu ma, sun nemi hadiyar zuciya ne bisa layin: sakamakon haka, an garzaya da wasu zuwa asibiti, wasunsu kuwa, nan take sun mutu ne ba tare da sun shura ba. Sai kuma magadansu su dora daga inda mamatan suka tsaya. Nan ma dai babu biyan buƙata.

Duba da irin yadda ake gallazawa tsoffin ma’aikata da sunan tantancewa a lokacin mulkin Kwankwaso da Ganduje, ta kai ta kawo kungiyoyin “yan-fansho na kasa da ƙungiyoyin ma’aikata (Nigerian Union of Pensioners, NUP, Nigeria Labour Congress, NLC) suka riƙa yin Alla-wadai da irin wannan cutarwa da gwamnatocin biyu ke yi wa “yan fanshon. Ba su kadai ba, hatta sauran kungiyoyin al’umar gari, suma sun yi tirrr da irin wannan yanayi na cutarwa, rashin jinkai gami da urustawa da ake nunawa tsoffin ma’aikatan dare da rana, salon yau daban, na gobe daban.

Jefa Razani A Zukatan Ma’aikata

An wayi garin cewa, duk wani ma’aikaci da lokacin ritayarsa ya matso a lokacin Kwankwaso da Ganduje, za a samu yana cikin fargaba iri biyu ne, saɓanin lokacin Shekarau da Abba Gida-Gida. Lokacin Shekarau da Abba, fargabar ma’aikaci ba ta wuce idan na aje aiki, wace kalar sana’a ce zan yi? Ba fargabar yadda zan karɓi fanshona da giratutina ba, irin yadda ma’aikatan ke fama a lokutan Kwankwaso da Ganduje. Wannan tunani na rashin tabbas wajen karɓar fansho da giratuti akan lokaci, ya jefa da yawan ma’aikatan gwamnati cikin ta’adar kuruciyar ɓera, kamar yadda masana da sauran masharhanta suka tsinkayar.

Salwantar Kudaden “Yan-fanshon

Duka a lokutan gwamnatocin Kwankwaso da Ganduje, biliyoyin kudaden “yan fanshon sun salwanta, ko dai an wawashe su ne, ko kuma an canja ainihin alkiblarsu, maimakon a bai wa tsoffin ma’aikatan hakkokinsu, a’a, sai aje a yi wani aiki daban da hakkokin nasu, ta yadda za su kara nesanta daga gare su. Gwamnonin, ba su da asara, wajen karkatar da akalar wadancan makudan kudade na “yan-fansho, saboda duk yadda aka mirgana kudaden, suna da nasu kamasho. Wani abu daga miyagun yanayai da “yan-fanshon ke shiga kamar yadda aka yi zargi shi ne, cikin wadannan gwamnoni biyu dake dandanawa tsoffin ma’aikata kuda a Kano, akwai wanda iyalansu ke zama da “yan-fanshon, a yi yarjejeniya, nawa ne kasonsu, nawa ne kason ainihin masu hakkin?. Idan dan-fansho ya yarda da gwaggwaɓan kason iyalan gwamna, na iya samun hakkin nasa na fansho a cikin Mako guda. Saɓanin haka kuwa, sai baba-ta-gani! Sau da yawan lokuta, masu fanshon, sai bayan sun bakunci lahira ne wani kason na fanshonsu ke fitowa. Wasu kuwa, sai anje Lahira ne za a banbance kwaya daga tsakuwa.

Babu shakka, mulkin Kwankwaso da Ganduje ga “yan-fansho a Kano, tamkar wani irin nau’in mulki ne da ake wa fatan kada Allah Ya maimata mana!!!.

Gaskiyar magana, lokacin Kwankwaso da Ganduje, “yan-fansho a Kano sun tagaiyara iya tagaiyara, sun shiga mummunan yanayi na talauci, wasunsu ma sun koma bara ne. Wasunsu kuwa, an kore su ne daga gidajen da suke haya ciki, saboda gaza biyan kudin haya. Wasunsu kuwa, har gaban alkali an dangane da su, saboda basuka da suka yi musu katutu. An koro “ya”yayen “yan-fanshon da dama daga makarantu, saboda gaza biyan kudin makaranta. Harkar lafiya da sauran wasu muhimman ababe dake da jiɓi da kashe kudi, sai dai “yan-fanshon su ga a na yi ne, ya fi karfinsu. Komai ya gagari kundila, sai kallo.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba October 25, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar October 24, 2025 Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri October 24, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kwankwaso da Ganduje yan fanshon

এছাড়াও পড়ুন:

Fiye da Gidaje 280 Sun Amfana da Kwandunan Zubar Sharar a Jihar Nasarawa

Fiye da gidaje dari biyu da tamanin (280) a Karamar Hukumar Lafia sun samu kwandunan ajiyar shara (trash bins) domin inganta kula da tsaftar muhalli da rage datti a babban birnin jihar.

 

An gudanar da rabon ne a birnin Lafia, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Nasarawa, Dr. Margaret Elayo.

 

Shirin wayar da kai da rabon kwandunan ya shafi wasu kananan hukumomi da suka haɗa da Karu, Keffi, Akwanga, Wamba, Obi, da Keana, inda Lafia ta fi kowa samun masu cin gajiyar wannan shiri.

 

A yayin taron, Dr. Margaret Elayo ta bayyana damuwarta kan yadda datti ke ƙaruwa a tituna da magudanan ruwa, lamarin da ke haifar da barazana ga lafiya da muhalli.

 

Kwamishinar ta yi kira da a rungumi sabon tsarin zamani na sarrafa shara zuwa dukiya (waste-to-wealth), inda ta shawarci masu karɓar kwandunan da su yi amfani da su yadda ya dace wajen zubar da kwalabe da robobin ruwan sachet, tana mai bayyana cewa ana ci gaba da haɗin gwiwa da masana’antun da ke sarrafa waɗannan kayan don sake amfani da su.

 

Masu cin gajiyar shirin sun yaba da wannan ƙuduri na Dr. Elayo, suna jinjinawa hangen nesanta da jajircewarta wajen kare muhalli, tare da yin alkawarin amfani da tankunan cikin gaskiya da aminci domin taimakawa wajen samar da muhalli mai tsafta a Jihar Nasarawa.

 

Aliyu Muraki, Lafia

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe
  • Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu
  • Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna
  • Gwamna Abba Ya Jaddada Mubaya’arsa Ga Kwankwaso 
  • Fiye da Gidaje 280 Sun Amfana da Kwandunan Zubar Sharar a Jihar Nasarawa
  • ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum
  • Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio
  • Kasar Iran Ta Kai Hare-Hare A Wuraren Da Kawayen Isra’ila Ba Su San Da Su ba A Lokacin Yakin Kwanaki 12
  • Jihar Kwara Ta Ware Naira Biliyan 8 Don Biyan Haƙƙin Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya