Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki
Published: 26th, October 2025 GMT
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal, Abdussamad Dasuki, ya ce ba zai tsaya takara a zaɓen 2027 ba.
Dasuki, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin bai wa matasan Najeriya damar shiga harkokin mulki.
El-Clasico: Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2 Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a NajeriyaYa bayyana cewa tun daga shekarar 2011 yake majalisar dokoki, kuma yana ganin zai fi dacewa idan aka bai wa matasa dama a dimokuraɗiyya.
“Najeriyar da muke mafarki za ta tabbata ne kawai idan mun yi sadaukarwa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bayan tuntuɓar iyalansa da jagororinsa, ya yanke shawarar bai zai sake tsayawa takara ba don ya gaji ba, sai don bai wa wasu dama.
Dasuki dai shi ne shugaban riƙon kwarya na ƙungiyar ‘Future Is Now Project’, ƙungiyar da ke fafutukar ganin an dama da matasa a harkokin siyasa.
An ƙaddamarda ƙungiyar a ranar 1 ga watan Oktoba, 2025 a Abuja.
Ƙungiyar ta buƙaci cewa a zaɓen 2027, kashi 70 cikin 100 na kujerun majalisar wakilai su kasance a hannun matasa ’yan kasa da shekaru 40.
Ya ce ko da yake shi ma matashi ne duk da ya haura shekaru 40, don haka dole ya gwada misali da kansa.
“Idan muna son ganin matasa sun jagoranci ƙasar nan, dole mu nuna hakan a aikace, Wannan ita ce sadaukarwa. Idan na matsa gefe sabbin jagorori za su fito,” in ji shi.
Shawarar Dasuki ta zama abun a yaba, a siyasar Najeriya, domin ba kasafai ake samun ’yan siyasa suna hakura da kujerunsu don raɗin kansu ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗan Siyasa Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa matsalar kashe-kashen da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar nan ba ta da alaƙa da addini, illa dai ayyukan miyagu da ke kashe Musulmi da Kirista ba tare da la’akari da bambancin addini ba.
Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a matsayin bako mai jawabi a taron cika shekaru 35 da kafuwar Cocin Anglican da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna.
NSCDC ta yi alhinin mutuwar Kwamishinan Tsaron Gombe An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a KanoTsohon Ministan ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su dawo daga rakiyar mutanen da ke amfani da addini wajen raba kan al’umma, yana mai cewa masu kashe Kiristoci su ne dai ke kashe Musulmi.
Ya buƙaci mabiya addinan biyu da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna, tare da guje wa duk wani yunƙurin na kawo rarrabuwa ko tashin hankali.
A nasa ɓangaren, Babban Mai Shari’a na Jihar Kaduna, Barista James Kanyip, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da kare ‘yancin addini da tabbatar da haɗin kai da shugabannin addinai, musamman masu wa’azin zaman lafiya da jituwa.
Shi ma Bishop Markus Dogo na Cocin Anglican da ke Kafanchan, ya bayyana irin ayyukan jin ƙai da cocin ya gudanar cikin shekaru 35, ciki har da gina makarantu, asibitoci da cibiyoyin koyon sana’o’i don tallafa wa marasa galihu.
Haka kuma, Sanatan Kaduna ta Kudu, Barista Sunday Marshall Katung, wanda ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Jema’a da Sanga, Hon. Daniel Amos ya wakilta, ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake tafiyar da mulki cikin adalci da rashin nuna wariya ga kowane ɓangare na jihar.
Taron ya samu halarci manyan shugabannin addini, na siyasa da na al’umma, inda suka jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai a matsayin ginshiƙai na ci gaban Najeriya.