Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
Published: 26th, October 2025 GMT
A kwanan nan, wata manufa da aka zartas a yayin wani taron kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta janyo hankalin al’ummun duniya, wato yadda kasar Sin take neman gaggauta dogaro da kai wajen kirkiro sabbin fasahohi, da zama mai jagorantar ci gaban masana’antun zamani a duniya. Inda dimbin kafofin yada labaru na kasashe daban daban ke ganin cewa, manufar ta nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora a bangaren raya kasa ta wata ingantacciyar hanya, da bunkasa fannin kimiyya da fasaha, wadda ita ma ta zame wa sauran kasashe abin koya.
Hakika, a wannan zamani da muke ciki, kusan dukkan kasashe suna sa lura kan aikin raya sabbin masana’antu. Saboda ra’ayi na kariyar cinikayya ya haifar da cikas ga tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya, da yunkuri na samun farfadowa a fannin saurin ci gaban tattalin arziki, lamarin da ya sanya kasashe daban daban ke kokarin neman sabbin sana’o’in da za su sa kaimi ga karuwar tattalin arzikinsu. Kana a bangaren kasar Sin, yawan kamfanoninta masu sarrafa sabbin fasahohi ya riga ya zarce dubu 500, yayin da adadin manyan rukunonin kirkiro sabbin fasahohin zamani a kasar, wadanda ke cikin jerin sunayen rukunoni mafi girma guda 100 na duniya, ya kai 26. Wadannan misalai sun shaida yadda kasar take dogaro kan ci gaban fasahohi wajen raya tattalin arziki.
Bisa shirin da aka zartas a taron kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin na wannan karo, Sin za ta kara kokarin samar da sabbin fasahohi masu muhimmanci, da hada bangaren kirkiro fasahohi da na sabunta masana’antu waje guda, da raya aikin ilimi a kokarin samar da kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha, da dai makamantansu. Hakan ya nuna yadda kasar ke neman raya kai ta wasu ingantattun dabaru, tare da sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da raba damammaki na samun ci gaba tare da sauran kasashe. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing
Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin tafiya kasar Koriya ta Kudu, domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabanni karo na 32, na kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar, an gudanar da wani taron tattaunawa, mai taken “Shugabancin duniya da samun wadata tare a yankin Asiya da Pasifik” a nan birnin Beijing, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da jami’ar Yonsei da gidan talabijin na YTN na Koriya ta Kudu suka shirya tare.
Yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce “CMG na fatan yin hadin gwiwa mai zurfi tare da kasashen yankin Asiya da Pasifik, don haka ya dace mu ba da labaran hadin gwiwa tare, mu kirkira, kuma mu bunkasa musayar al’adu, mu shiga tattaunawa da hadin gwiwa, sannan mu ba da gudummawar hikimomi da karfinmu, wajen kyautata tsarin shugabancin duniya”. (Safiyah Ma)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA