Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf.

 

Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani ya yabawa hukumar DSS kan nasarar da ta samu, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawar da miyagun laifuka a fadin jihar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki  October 22, 2025 Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar.

Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Barrister Lawan D. Baba ya bayyana cewa ma’aikatar ta yi kiyasin kashe naira milyan 311 da dubu 847 a kasafin kudin sabuwar shekara.

Babban sakataren yace za su mayar da hankali ga batun kawar da jinkiri wajen gudanar da shari’o’i domin karfafa matakan samun shari’a cikin sauri ga al’ummar jihar.

A nasa jawabin, Shugaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Hadejia, Barrister Abubakar Sadiq Jallo, ya jaddada bukatar wanzuwar dangantakar aiki tsakanin kwamatin da bangaren shari’a domin inganta aikin shari’a a kotu.

Kazalika, magatakardar Babbar kotun jihar da sakataren hukumar kula da ma’aikatan shari’a da kuma sakataren hukumar bada tallafin shari’a su ma sun kare na su kiyasin kasafin kudaden a gaban kwamatin.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’
  • ’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
  • ’Yan bindiga ya hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
  • Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi
  • Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas
  • Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa
  • ’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo
  • Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara