Shugaba Tinubu Ya Taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu Murnar Ranar Haihuwa
Published: 16th, October 2025 GMT
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci mai tawali’u, mai aminci, kuma mai kishin kasa wanda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa abin a yaba ne.
Shugaban ya yaba wa Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma kuma shugaban kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati bisa “kishin sa na gaskiya, rikon amana, tsarin kasafin kudi, da dokoki masu tasiri da ke magana kan makomar kasarmu.
Da yake karin haske kan tarihin Sanata Wadada a Majalisar Dokoki ta kasa, Shugaba Tinubu ya lura cewa “a cikin shekaru biyu kacal a Majalisar Dattawa, kun bambanta kanku a cikin doka, wakilci, da kuma kulawa a matsayin daya daga cikin masu basirar majalisa, mai taka rawa, kuma abin koyi ga matasa masu tasowa.”
Shugaban ya bi sahun al’ummar Nasarawa ta Yamma, ‘yan uwa, abokan arziki, da abokan zaman Sanatan wajen taya shi murna, tare da yi masa fatan Allah ya kara masa karfin gwiwa, da hikima da kuma koshin lafiya domin ya ci gaba da yi wa kasa hidima.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Taya Murna
এছাড়াও পড়ুন:
Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin tare da mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.
Kungiyar ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da da’a, kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da ingancin wasan kamar yadda hukumar NPFL da hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta tanada, Pillars ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su gudanar da ayyukansu cikin lumana tare da ci gaba da ba kungiyar goyon baya, amma kuma wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yan wasan 3SC da aka jikkata tareda raunuka a jikinsu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA