An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato
Published: 23rd, October 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan manoman da suke aikin girbin amfanin gona a yankin Mbor na masarautar Mushere na Ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Filato, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu biyu a ranar Laraba da yamma.
Shugaban Ƙungiyar matasan Mushere, Kopmut Monday ne ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin a ranar Alhamis.
A cewar shugaban matasan, ’yan bindigar sun kai farmaki wurin ne inda suka buɗe wuta kan manoman da ke cikin aikin girbin amfanin gona, inda ya ce manoman sun tsere domin tsira da rayukansu.
Shugaban ya zargi makiyaya da kai wa mambobinsu hari, inda ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin “mazauna garin Rongjing ne a jiya da yamma sun kai wa ’yan ƙungiyarmu hari a yankin Mbor a lokacin da suke girbin amfanin gona, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku da jikkata mutum biyu da harbin bindiga. Waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.
Monday yya ƙara da cewa, al’ummar yankin suka sha fama da irin wannan hari a ranar 26 ga watan Mayu an kashe mutane bakwai.
Ya ce “lamarin baya-bayan nan wani mummunan al’amari da ya faru a watan Mayu, wanda ya yi sanadin kisan mutane bakwai, da jikkata wasu da kuma ƙona gidaje da dama ciki har da coci guda biyu.”
Monday ya kuma bayyana cewa, al’ummar da aka kai wa harin baya-bayan nan, sun yi kira ga jami’an tsaro da su tura isassun ma’aikata don dawo da zaman lafiya a yankin saboda mazauna yankin ba za su iya gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaron kasashen pakistan da Afghanistan sun yi musayar wuta mai tsananin a iyakokin kasashensu, kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 5, hakan na nuna irin rikicin dake tsakanin kasashen masu makwabtataka da juna, bayan sun cimma yarjejeniyar sulhu a kasar saudiya amma da alama babu ci gaban da aka samu.
A wani sakon da kakakin gwamnatin Taliban ya wallaka a shafinsa na x zabihullah majahid yace sojojin kasar Pakistan sun kaddamar da hari a wani yanki dake lardin kandahar na kasar Afghanistan da hakan yasa sojojin su mayar da martani.
Sai dai ana sa bangaren firaministan kasar Pakistan Shebaz sharif ya ce sojojin kasar afgahnistan ne suka fara harbe harbe a iyakar chaman,
Dangantaka tsakanin Afghanistan da Pakistan ta kara tabarbarewa ne a yan watannin baya bayan nan, inda rikici ya kara Kamari tsakaninsu a iyakokin kasar duk da tattaunawar sulhu da ka yi a a Qatar da kuma na bayan bayanna a kasar saudiya amma har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Masar Sun yi Kira Da Kawo Karshen Keta Hurumin Gaza da Labanon da Isra’ila ke yi December 6, 2025 Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba December 6, 2025 Gwamnatin Najeriya Za ta Karbi Sabon Bashin Dala Miliyan 500 A Bankin Raya Kasashen Afrika December 6, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Sun Yi Gargadi Game Da Yunkurin Isra’ila Na Kashe Barghusi December 6, 2025 Gasar FIFA: Iran Ta Fada Cikin Group Mai Sauki A Gasar Kwallon Kafa Ta FIFA 2026 December 6, 2025 Kasashen Musulmi 8 Sun Ki Amincewa Da Korar Falasdinawa Daga Gaza December 6, 2025 Sojojin Afganistan Da Pakistan Sun Yi Musayar Wuta A Tsakaninsu Duk Tare Da Tsagait Wuta December 6, 2025 Rasha Tace Ta Kakkabo Jiragen Drones Na Ukrai 116 A Daren Jiya December 6, 2025 ‘Yar Iran ta isa wasan karshe na gasar cin kofin duniya na wasan harbi a karo na 4 December 6, 2025 Iran da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi 20 da kwangiloli 5 a fannin fasaha December 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci