2025-10-15@16:23:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8093
«a wannan manhaja»:
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da fitar da Naira biliyan 5.8 domin biyan haƙƙin tsoffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar. Kwamishinan kuɗi na jihar, Mohammed Abatcha Geidam, ya ce wannan mataki na nuna yadda gwamnatin ke ƙoƙarin inganta rayuwar ma’aikatanta, musamman waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar. Farashin kayayyaki ya sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba — NBS Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan Ya ce gwamnan ya bayar da umarni cewa daga yanzu, biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata zai zama cikin jadawalin kuɗin wata-wata kamar yadda ake biyan fansho. “Ina nufin daga yanzu za a riƙa biyan kudin a kowane wata tare da fansho, domin...
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, ta sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba, 2025, idan aka kwatanta da kashi 20.12 da aka samu a watan Agusta. A cewar rahoton hukumar, hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya a watan Satumba ta kasance kashi 0.72, yayin da farashin kayan abinci ya ragu da kashi 1.57, idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF Cikakken bayani na tafe…
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa. Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu. ’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF Lawan, wanda ya wakilci mazabar Bagwai/Shanono a Jihar Kano, yana cikin mutane 175 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa afuwa a ranar 9 ga watan Oktoba. An kama shi a shekarar 2021 bayan samun sa da laifin karɓar cin hanci a 2012, domin cire sunan wani kamfani daga jerin...
Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, ya bayyana Jihar Borno a matsayin jiha mafi juriya a Najeriya, yana jaddada gagarumar nasararta wajen shawo kan ƙalubale da dama tsawon shekaru. Yayin wata ziyarar ban-girma da ya kai wa Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Isa Kadafur, a Maiduguri, Ministan ya yaba wa mutanen jihar bisa jajircewarsu da himmarsu wajen fuskantar matsaloli. Wannan ziyara na daga cikin shirye-shiryen taron Kwamitin Kwamishinonin Yada Labarai na jam’iyyar APC. Ya bayyana cewa abubuwan da suka faru a Borno cikin shekaru goma da suka wuce sun nuna jarumtaka da haƙurin mutanen jihar, waɗanda ke ci gaba da ginawa da tafiya gaba duk da matsalolin da suka fuskanta. Ministan ya jaddada cewa ƙarfin gwiwar mutanen Borno abin alfahari...

Dakta Umar Kabir Yusuf-Bakatsinen da ya kirkiro manhajar Masjid Suite da ke sada zumuncin hada masallaci da masallata
Dakta Umar Kabir Yusuf-Bakatsinen da ya kirkiro manhajar Masjid Suite da ke sada zumuncin hada masallaci da masallata Daga Ibrahim B. Surajo Dakta Umar Kabir Yusuf matashin manazarci ne dan asalin Jihar Katsina da yake zaune a kasar Amurka wanda ya kirkiri wata manhaja mai suna Masjid Suite. A cikin hirar da ya yi da Jaridar Aminiya matashi ya bayyana abin da ya sa ya kirkiri manhajar da kuma da ayyukan da take yi. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Ko za ka fada mana wacce manhaja ce ka kikira? Sunan manhajar Masjid Suite, wacce ake saukewa a wayar hannu. Kuma na kirkire ta ne saboda saukake sadarwa a tsakanin masallaci da masallata musamman a nan kasarmu Nijeriya da sauran...
Amma ya nuna damuwa cewa jinkiri wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta yi da ASUU na ƙara haifar da rashin jituwa. Ya roƙi Shugaba Tinubu, da ya sa baki kai-tsaye don kawo ƙarshen rikicin, yana mai gargaɗin cewa jinkiri wajen ɗaukar mataki na iya gurgunta ci gaban da aka samu a fannin ilimi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025 Labarai Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu October 15, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako October 15, 2025
’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace dabbobi da dama a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, inda aka kashe wani mazaunin ƙauyen Kwadawa da ke yankin Gachi, yayin da wani kuma ya jikkata. Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike Shaidu sun ce kimanin ’yan bindiga 100 ne suka kai harin, inda suka kuma mamaye ƙauyen Bogga; ƙauyen Fulani da ke kan hanyar Kankia zuwa Ingawa. Sakamakon haka, mazauna ƙauyukan Bogga, Taiba Badole, Arahiya Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo duk da ke yankunan Gachi da Fakuwa/Kafindangi, sun tsere daga...
Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta zuba jari a fannin kayan aikin wanke hannu da kuma ilimin tsafta. Asusun ya kuma ce kaso 35 cikin 100 na makarantu ne kawai ke da kayan wanke hannu na asali, yayin da kashi 8 cikin 100 na ’yan Najeriya ne kawai ke iya nuna yadda ake wanke hannu daidai. Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike Yayin wata ziyara da aka kai makarantu a Jihar Borno a ranar Laraba, a wani ɓangare na bikin Ranar Wanke Hannu ta Duniya ta shekarar 2025, Shugabar Ofishin UNICEF a Maiduguri, Dr....
Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya fice daga jam’iyyar PDP. Mai magana da yawun gwamnan, Daniel Alabrah, ne ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook na ainihi, kodayake bai bayyana dalilin ficewar gwamnan daga jam’iyyar ba. Har ila yau, bai bayyana ko Gwamna Diri zai koma APC mai mulki ko kuma hadakar ’yan adawa ta ADC ba. Aminiya ta gano cewa Gwamna Diri yana halartar wani taro da mambobin majalisar zartarwa ta jiha, inda ya bayyana musu wannan bayani. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa, Rt. Hon. Abraham Ingobere, yana cikin mahalarta taron. A cikin sa’o’i kaɗan da suka gabata, Gwamna Diri tare da tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, sun halarci bikin ƙaddamar...
Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar da ta kafa asusun adashen gata na kiwon lafiya na jihar ya sahalewa asusun damar samo kudade daga wasu bangarori da ba na gwamnati ba. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan tsokaci lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a ofishin asusun da ke Dutse. Ya bayyana bukatar ganin asusun JICHIMA ya nemo kudade daga hannun masu taimakon al’umma da cibiyoyi da ‘yan siyasa da kwamitocin zakka da na waqafi domin bunkasa asusun, ta yadda zai biya bukatun kiwon lafiyar al’ummar jihar. Alhaji Usman Musari ya lura cewar fadada hanyoyin samun kudade ga...
Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya kai ziyarar ba-zata ta duba aiki a Asibitin karbar Haihuwa na Imamu Wali, na Marmara, da kuma Asibitin Sabon Bakin Zuwo. Ya kai ziyarar ce domin tabbar bin umarnin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na wucin gadi wajen sauya wuraren gudanar da ayyukan karbar haihuwa da na yara zuwa wasu cibiyoyi daban. A karkashin wannan umarni, an mayar da sashen haihuwa na Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase zuwa Asibitin Haihuwa na Imamu Wali, yayin da aka mayar da ayyukan yara kyauta da ake yi a Asibitin Yara na Hasiya Bayero zuwa Asibitin Haihuwa na Marmara. Wadannan canje-canjen sun biyo bayan ci gaba da...
Ya ce manufofi da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata sun ƙara wa jama’a ƙwarin gwiwa game da tattalin arziƙin ƙasa da tafiyar da gwamnati, abin da ya sa zai yi wuya a kayar da shi a 2027. “Babu wani ɗan siyasa a yau da zai iya ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Muna tafiya da ‘sabon fata’ zuwa ‘farfafowa,’ kuma wannan farfaɗowar dole ne ta bayyana a rayuwar talakawa,” in ji Bwala. Ya ƙara da cewa shugabannin ƙungiyoyi daga dukkanin shiyyoyi shida na ƙasar nan sun halarci taron, ciki har da wasu da suka zo daga Biritaniya. Bwala, ya bayyana cewa taron ba yaƙin neman zaɓe ba ne, amma wata dama ce don gina...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadawa kungiyar Hamas su mika makamansu da radin kansu ko kuma zai kwance damararsu da karfi. Jaridar Daily Mails ta kasar Burtaniya ta nakalto shugaban yana fadarwa kafafen yada labarai a washinton a jiya Talata. Amma kungiyar Jihadul Islami daya daga cikin kungiyoyin da ke dauke da makamai a zirin gaza ta bakin mataimakin babban sakataren kungiyar Mohammad Al-Hindi a hirar da yayi da tashar talabijan ta Aljazeerah cewa kungiyoyi masu gwagwarmaya a gaza basu amince su mika makamansu a yarjeniyar sulhu na Trump ba kuma basu damu da barazanar shugaba Trump na kwance damarasu da karfi ba. Alhindi ya kara da cewa banda haka babu wata kalma ko guda a cikin yarjeniyar da...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kungiyar kwallon kafa ta kasaSuper Eagles murnar nasarar da suka samu ta ci 4 da nema a kan Cheetahs ta Jamhuriyar Benin, tare da yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi na ci gaba da kokarin cika al’umma, yayin da suke neman cancantar zuwa gasar cin Kofin Duniya ta FIFA a shekarar 2026. Shugaban ƙasar ya jinjina wa Super Eagles bisa ƙwazo, da jajircewar da suka nuna a filin wasa na Uyo, yana mai cewa wannan gagarumar nasarar ta sake karfafa ‘yan Najeriya kan harkar ƙwallon ƙafa. “Yanayin farin ciki da ake ciki a fadin ƙasar nan na nuni da yakinin da muke da shi cewa Najeriya ta cancanci samun gurbi a gasar...
Ya kuma roƙi shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka su haɗe kai wajen yaƙi da ƙungiyoyi masu amfani da ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, inda ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka suna ƙara haifar da tashin hankali da talauci. Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, shi ma ya yi kira ga ƙasashen yankin su amince da yarjejeniyar ECOWAS kan cin hanci, domin hana masu rashawa samun wajen ɓuya. “Mu tabbatar babu inda ɓarayi za su ɓuya. Duk wanda yake tayar da hankali a ƙasashenmu bai kamata ya samu natsuwa ba,” in ji Fagbemi. Ƙungiyar NACIWA ƙungiya ce ta hukumomin yaƙi da cin hanci daga ƙasashen ECOWAS, wadda ke aiki tare wajen yaƙi da rashawa. Shugaban ƙungiyar na yanzu shi ne Ola Olukoyede, wanda kuma...
Wasu kudurori guda 3 da ke dauke da bukatun kafa wasu hukumomi 3 sun samu karatu na biyu a zauren majalaisar dokokin jihar Jigawa. Kudurorin guda 3 sun hada da na kafa Hukumar Samar da Hanyoyin Mota a yankunan karkara, da na kafa Hukumar Samar da Kudade Domin Ayyukan Hanyoyin Mota a yankunan karkara da Kuma na Hukumar Bunkasa Kwazon Malamai ta jihar Jigawa. A lokacin ya ke gabatar da kudurorin domin neman goyon baya kan bukatar kafa hukumar bunkasa kwazon malamai, mataimakin shugaban masu rinjaye na majlaisar, Alhaji Sani Sale Zaburan ya ce gwamnatin jihar na da nufin inganta aikin koyarwa ta hanyar kafa hukumar da za ta rinka horas da malamai akai akai. Da su ke tattaunawa kan...
Kotun Babban Majistare da ke Yaba ta bayar da umarnin a tono gawarwakin mutane 10 da gobara ta kashe a ginin Afriland Towers da ke Legas a ranar 16 ga Satumba, 2025, domin a gudanar da bincike a kansu. Alkalin kotun, Mai shari’a Atinuke Adetunji ce ta bayar da umarnin a ranar Talata bayan ta samu labarin cewa an riga da binne wasu daga cikin waɗanda gobarar ta ritsa da su. “Mai ƙorafi ya rubuta wa Gwamnatin Jihar Legas don neman izinin tono gawarwakin waɗanda suka mutu, sannan a gudanar da bincike a kansu,” in ji Mai Shari’a Adetunji. Wannan umarni ya biyo bayan wata wasiƙa daga ofishin babban lauya Femi Falana da aka aike wa Babban Mai Kula da...
Kotun Babban Majistare da ke Yaba ta bayar da umarnin a tono gawarwakin mutane 10 da gobara ta kashe a ginin Afriland Towers da ke Legas a ranar 16 ga Satumba, 2025, domin a gudanar da bincike a kansu. Alkalin kotun, Mai shari’a Atinuke Adetunji ce ta bayar da umarnin a ranar Talata bayan ta samu labarin cewa an riga da binne wasu daga cikin waɗanda gobarar ta ritsa da su. “Mai ƙorafi ya rubuta wa Gwamnatin Jihar Legas don neman izinin tono gawarwakin waɗanda suka mutu, sannan a gudanar da bincike a kansu,” in ji Mai Shari’a Adetunji. Wannan umarni ya biyo bayan wata wasiƙa daga ofishin babban lauya Femi Falana da aka aike wa Babban Mai Kula da...
“Kusan kullum muna cikin tashin hankali a Shinkafi,” in ji shi. Mutumin ya kuma zargi gwamnati daga matakin tarayya har zuwa ƙaramar hukuma da zuba wa matsalar ido. “Hare-haren suna ci gaba a Birnin Yero, Jangeru, Shanawa, da Shinkafi kanta. Ko jiya da safe sun kawo hari sun kama manoma.” A cewarsa, manoma da dama sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron za a sace su. Wasu kuma suna zuwa da dare ne kawai don samun ɗan abin da za su ci. Sai dai, gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana sane da matsalar da jama’ar yankin ke fuskanta, kuma tana ɗaukar matakai don magance ta. Mai magana da yawun gwamna, Mustafa Jafaru Kaura, ya ce: “Gwamnati tana yin duk abin da...

A Lokacin Yaki, Iran Ta Tarwatsa Wata Cibiyar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya Da Ke Yankin Farar Hula
Iran ta kai hari a wani sansanin sojan Isra’ila na sirri da ke karkashin wata hasumiya a Tel Aviv Yankin Gray, wani dandali ne na bincike, ya bayyana samuwar wani maboyar sirri na sojan Isra’ila da ke karkashin wani hasumiya a Tel Aviv, wanda ake kyautata zaton yana cikin wadanda aka kaiwa hari da makami mai linzami na Iran yayin harin da aka kai ranar 13 ga watan Yuni. Bisa binciken da aka gudanar, dandalin ya gano wurin da wani wurin karkashin kasa da aka fi sani da “Site 81”, wani rukunin jami’an leken asiri na hadin gwiwar sojojin Amurka da Isra’ila da ke karkashin rukunin gidaje na Da Vinci a wata unguwa mai yawan jama’a a tsakiyar birnin Tel...
Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta sanar da cewa, sake gina Gaza na bukatar dala biliyan 70, kuma a halin yanzu ana bukatar dala biliyan 20 domin fara ayyuka a cikin shekaru masu zuwa. UNDP ta yi tsokaci game da abin ta kira alamomi masu kyau game da samar da kudade don sake gina Gaza, kuma ta ambaci Amurka da kasashen Larabawa da Turai a cikin wadanda zasu taka rawa a wannan batu. Rahoto ya bayyana cewa yawan baraguzan dake jibge ya kai tan miliyan 55. Da yake amsa tambaya game da lokacin sake gina Gaza, wani jami’in UNDP ya ce, mai yiwuwa a cikin shekaru goma zuwa 20 a iya sake gina yankin. A gefe guda...
“Salon shugabancinsa da amincewa da cancanta sama da son rai ne ya sa kowane mai kishin ci gaba daga ƙarshe yake samun mafaka a APC,” in ji shi. Gwamna Mbah ya bayyana shiga jam’iyyar APC bayan tattaunawa da magoya bayansa, yana mai cewa hakan “sabuwar tafiya ce” ga Jihar Enugu da yankin Kudu maso Gabas wajen samun babban matsayi a siyasar ƙasa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta October 14, 2025 Manyan Labarai Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato October 14, 2025 Siyasa PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai October...
Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya. Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki. Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Hukumar Hana Fatucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce dai da gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harkallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, wadanda su ba su...
Majalisar Wakilai ta ƙaddamar da bincike kan ƙaruwar koke-koken ’yan Najeriya kan yawan cire musu kuɗaɗe ba tare da bayani ba daga asusun ajiyarsu da bankunan kasuwanci ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da wani ƙuduri da ɗan majalisa Hon. Tolani Shagaya (APC, Kwara) ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan abin da ya kira “cire kuɗaɗe ba tare da bayani ba, da kuma yawan kuɗaɗen da ake karɓa ba bisa ka’ida ba,” duk da dokokin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kafa. An kama mata da miji suna safarar makamai a Kaduna Kofin Duniya: Da sauran rina a kaba duk da Najeriya ta ci Jamhuriyar Benin 4-0 Yayin gabatar da ƙudurin a zaman majalisa ranar Talata, Shagaya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya. Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi. Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta fara gushewa ne a siyasar Najeriya? NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Yajin Aiki? DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
Daga nan sai kakakin ya ce, “Ba zai yiwu bangaren Amurka ya nemi tattaunawa a bangare guda, alhali a daya hannun yana barazanar kaddamar da sabbin takunkumai kan kasar Sin ba. Wannan ba ita ce hanya mai dacewa ta gudanar da cudanya da Sin ba.” (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani October 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani
A nata bangare, Sima Bahous ta yabawa ci gaban da Sin ta samu wajen cike gibin fasahohi tsakanin jinsi, da ingiza ci gaban harkokin mata ta kowanne bangare da kare hakkoki da muradun mata. Ta kuma yi kira ga kasa da kasa su hada hannu tare wajen karfafa gwiwar mata da ‘yan mata su samu ci gaba a zamanin amfani da fasahohi. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025 Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude...
Sayyidi Aliyu ya shaida hakan ne yayin jawabin bankwana da wayar da kan ɗaliban da suka samu gurbin karatun zuwa ƙasar Algeria na shekarar 2025, da ya gudana a cibiyar Sheikh Dahiru da ke Bauchi a ranar Litinin 13 ga watan Oktoba. Ya ce an ɗauki tsawon lokaci ana wayar da kan ɗaliban na tsawon shekara guda kan yadda za su kyautata rayuwarsu a can ƙasar da kuma samun ilimin da ake tsammani a garesu ba tare da matsaloli ba tare da koyar musu harsunan Farsanci da Larabci domin sauƙaƙa musu fara rayuwa a ƙasar Algeria. Ya yaba wa Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad bisa biyan kuɗin jirgi wa dukkani ɗaliban jihar su 50 daga cikin waɗanda za...
Sojoji sun kama wata mata da mijinta da suka yi kaurin suna wajen safarar makamai a yankin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna. Dubun ma’auratan ta cika ne a wani shingen binciken inda sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma suka gano harsasai 1,207 hannunsu. Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom ya ce an kama su ne a hanyars ta kai wa ’yan ta’addan da ke addabar yankin Arewa maso Yamma makaman. Ya ce matar mai shekaru 18 mijin masi shekaru 40 suna tsare suna amsa tambayoyi, yana mai jinjina wa sojoji da ’yan banga bisa kwarewar da suka nuna wajen kama miyagun. Kofin Duniya: Da sauran rina a kaba duk da Najeriya ta ci Jamhuriyar Benin 4-0 Na yafe...

Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025 Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata October 14, 2025
A zaman na ranar Talata, lauyan masu shigar da kara, Salisu Muhammad-Tahir, ya shaida wa kotun cewa biyu daga cikin wadanda ake tuhumar, Abubakar da Odlyne, ba a samu gabatar da su a gaban mai sharia ba duk da kokarin tilasta musu halartar zaman. Muhammad-Tahir ya ce “Mun yi iya bakin kokarinmu don tabbatar da kawo su gaban mai shari’a, amma muna neman afuwar kotu,” in ji Muhammad-Tahir, inda ya bukaci alkalin da ya dage sauraron karar tare da tsare Ogugua a gidan yari har sai an gabatar da wadanda ake nema. Lauyan wanda ake kara, Gideon Uzo, ya roki kotun da ta bar wanda yake karewa ya ci gaba da zama a hannun hukumar hana fataucin mutane...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata October 14, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique October 14, 2025
Tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kara da Cheetahs na Jamhuriyar Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026. Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta. Tun kafin a fara wasan, an samu sauye-sauye hudu daga tawagar da ta doke Lesotho, inda Wilfred Ndidi ya hau matsayin kyaftin, yayin da Moses Simon ke shirin yin buga na 85 a wasannin kasa da kasa. A gaba kuma, an hada Victor Osimhen da Akor Adams domin tayar da kura. Wasan ya fara da sauri — ina minti na uku kacal, Osimhen ya zura kwallo ta farko bayan Chukwueze yi mika...
Mahaifin margayi Bilyaminu wanda matarsa Maryam Sanda ta kashe, ya ce shi ne ya roki Shugaba Tinubu ya yafe mata duk da hukuncin kisa da kotu ta yanke mata kan laifin. Malam Ahmed Bello Isa ya bayyana haka ne yayin ganawa da ’yan jarida, tare da mahaifin Maryam, Alhaji Garba Sanda. Sun gudanar da taron ’yan jaridar ne bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan yafiyar da Shugaban Kasa ya yi mata tare da wasu mutane 174 da ke tsare a gidajen yari bayan an yanke musu hukunci kan manyan laifuka daban-daban. Aminiya ta ruwaito dangin Bilyaminu ta hannun Dakta Halliru Bello Muhammad, wanda kawu marigayin ne kuma a hannunsa ya taso yana bayyana yafiyar da aka yi wa Maryam Sanda...

An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato October 14, 2025 Labarai An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa October 14, 2025 Manyan Labarai Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi October 14, 2025

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata
Ta ce shawarwari hudu da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, duk suna kira ne da a yi hadin gwiwa don tabbatar da daidaiton jinsi, ya zama bai daya cikin manyan batutuwa da ya dace a tattauna a duniya. Ana bukatar karin ayyuka, kuma ba shakka wannan taro yana da matukar muhimmanci. A nata bangare kuwa, wakiliyar kasar Tanzaniya Juliana Kibonde, cewa ta yi, an saurari jawabin shugaba Xi Jinping, wanda ke da matukar muhimmanci ga kasashen Afirka. An kuma lura da yadda za a ba mata ikon ci gaba a fannoni kamar na fasaha, da siyasa da sauyin yanayi. Kazalika, shugaba Xi ya ambaci batun gibin dijital, kuma ana iya fahimtar cewa, wasu kasashe suna...
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta kammala aikin titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano kafin ƙarshen shekara mai zuwa. Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka, Barista Bello Muhammad Goronyo, ne ya bayyana haka bayan ya kai ziyara domin duba yadda aikin ke tafiya a ranar Talata. Barista Goronyo ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya ba da umarni cewa a tabbatar da kammala aikin cikin lokaci, ganin muhimmancin hanyar wajen haɗa Arewa da Kudancin ƙasar da kuma babban birnin tarayya Abuja. Ya bukaci kamfanin da ke gudanar da aikin da ya hanzarta kammalawa kafin wa’adin da aka tsara, tare da gyara ramukan da ke hanyar domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a. Ministan ya kuma nuna damuwarsa kan halin da...
Al’ummar yankin sun bayyana cewar matsalar tsaron ta gurgunta tattalin arzikin yankin musamman ayyukan noma wanda ya sa ɗaruruwan mutane da dama neman mafaka a sansanin gudun hijira a Sakkwato da makwabtan jihohi. Dasuki ya bayyana cewar a ranar 12 ga Augusta 2025, ‘yan ta’adda sun shiga mazaɓar Fakku a karamar hukumar Kebbe tare da kashe mutane biyar da garkuwa da mutane 28 da satar shanu 37. “Haka ma a ranar 15 ga Agusta, ‘yan bindigar sun kai farmaki mazaɓar Sangi tare da tilastawa jama’a neman mafaka a Kuchi da Koko a jihar Kebbi. Bugu da kari a ranar 18 ga Agusta ‘yan ta’adda sun afkawa mazabar Ungushi tare da kisan mutane biyu da garkuwa da mutane bakwai...
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad ta yi maraba da sako Falasdinawa kusan 2000 daga gidajen yarin Isra’ila, tare da cewa jarumtakar mayakan gwagwarmaya da hadin kan al’ummar Falasdinu ne ya haifar da wannan babbar nasara. A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ziyad al-Nakhalah ya fitar ya bayyana cewa, wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta samo asali ne sakamakon jajircewa da tsayin daka da hadin kan al’ummar Falasdinu, wanda idan ba tare da hakan ba yarjejeniyar ba za ta taba cimma ruwa ba. Bayan shafe sama da shekaru biyu ana kai hare-hare ba kakkautawa wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatan Falasdinawa, gwamnatin Isra’ila bisa matsin lambar kasa da kasa ta amince da yarjejeniyar da Amurka ta kulla...
Rukaiya Abdullahi mawakiya ce a Masana’antar Kannywood wacce daga bisani kuma ta dawo yin fim duk a masana’antar. A hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara aiki a matsayin sakatariya ta ofishin daya daga cikin masu shirya fim. Ga yadda hirar ta kasance: Gabatar da kanki ? Sunana Rukaiya Abdullahi Yaushe kika shigo Masana’antar Kannywood? Na shigo Masana’antar Kannywood a shekarar 2020, amma zan samu kamar shekara 15 ina tare da su sai dai ban fara yin fim ba sai a 2020. Me ya jawo hankalinki kika shigo harkar fim? To da farko dai ba harkar fim na fara da ita ba a Kannywood, na fara da aikin sakatariya ne a wurin ’yan fim, yayan Nasiru Sarkin waka wato...
Majalisar Wakilai ta gayyaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da bankunan kasuwanci domin amsa tambayoyi kan yadda suke cirar cajin kudade barkatai daga asusun masu ajiya. Majalisar ta gayyace su ne bayan kudurin da Honorabul Tolani Shagaya ya gabatar kan abin da ta kira ‘cirar cajin kudade barkatai babu bayani ba,’ da bankuna suke yi daga asusun masu ajiya, sabanin dokokin CBN. Honorabul Shagaya ya ce kodayake bankuna da gudanar da hidima ne da ake biya, amma yawancin ’yan Najeriya suna kuka kan yadda suke yawan ciyar kudade — kamar na tura sakon tses, kula da katin ajiya, kula da asusun ajiya, tura kudi, hrajin kan sarki da wasu da ba su san da ake fiye da sau daya. Ya ce...
Gwamna Peter Mba na Jihar Enugu da kwamishinoninsa da sauran mukarrabansa sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki. Da yake sanar da hakan a ranar Talata a garin Enugu, Gwamna Mbah ya jaddada aniyarsa ta kare muradun jihar, tare da bayyana kwarin gwiwa cewa APC za ta ba wa jihar karin damar hadin gwiwa domin samun ci-gaba. Mbah, wanda ya samu rakiyar magabacinsa, tsohon Gwamna Ifeanyi Ugwanyi, da ’yan majalisar dokokin jihar da takwarorinsu na Majalisar Dokoki ta Kasa ya ce sun yi ittifafkin komawa APC ne domin kara hidimta wa al’ummar jihar da kuma kare manufofinta na ci gaba. “Bayan tsawon lokaci ana ta nazari, a yau dai, mun yanke shawarar sauya sheka daga PDP zuwa...
’Yan Majalisar Tarayya uku daga Jihar Kaduna sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya sanar a ranar Talata cewa masu sauya shekar sun hada da Honorabul Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da kuma Sadiq Ango Abdullahi. Tajuddeen, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, ya sanar da cewa, Gwamnan jihar, Uba Sani ya halarci zaman majalisar domin shaida dawowar ’yan majalisar zuwa APC daga PDP. Masu sauya shekar sun bayyana cewa rikin cikin gida da rabuwar kai da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP ce ta sa suka yanke shawarar sauya sheka. Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila...
Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki. Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin da ma’akatan agajin suka shafe kimanin awa hudu ba su motsa ba saboda luguden bamabaman. Kwamandan hukumar soji da ke yankin ta bayyana cewa an kona motoci hudu tare da lalata wata a cikin tawagar kayan agajin, amma ba a samu asarar rayuka ba a harin da aka kai da jirage marasa matuka da manyan bindigogin atilare a garin Bilozerka. Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Ya kuma kara da cewa JMI zata saurari shawarorin kawayenta amma kuma tana cikin shirin ko ta kwana idan makiya sun yi kuskure sun fadawa kasar da yaki. Baghaei ya na nuni ne da zantawar firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a makon da ya gabata, inda kuma ya bukaci shugaba...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donal Trump a cikin majalisar dokokin HKI a jiya Litinin inda ya bayyana cewa HKI ta sami nasara a yakin da ta kaiwa JMI a cikin watan Yunin da ya gabata, sannan daga karshe ya ce akwai bukatar a cimma yarjeniya da JMI kan shirinta na makamashin Nukliya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na cewa jawabin Trump a majalisar Knesset jawabi ne wanda bai da wani kima. Musamman a lokacinda yake gabatar da ita a gababan yan ta’adda makasa. Ma’aikatar ta tunatarwa Trump har yanzun tana jirin randa za’a gabatar da shi a gaban kuliya kan kissahn Janar shahida Qasim Sulaimani, wanda...

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya yi gargaɗin cewa dogaro da soja kaɗai, ba tare da inganta rayuwar jama’a ba, zai ƙara haifar da rikice-rikice. Ya ƙara da cewa ingantacce tsaro na ƙasa yana farawa ne idan gwamnati ta ƙirƙiro damarmakin samun aiki da kuma mayar da amincin jama’a ga gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa October 14, 2025 Manyan Labarai Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan October 14, 2025 Manyan Labarai Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026 October 13, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan October 14, 2025 Manyan Labarai Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026 October 13, 2025 Ilimi Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba October 13, 2025
Dangin Marigayi Bilyaminu Ahmed Bello sun bayyana takaicinsu bisa sanya matarsa, Maryam Sanda, wadda kotu ta ɗaure ta kan laifin soka masa wuka har lahira, a cikin jerin mutanen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa. A shekarar 2020 ne kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu. Sanarwar da dangin marigayin suka fitar ɗauke da sa hannun Dakta Bello Haliru Mohammed (Dangaladiman Gwandu) ta bayyana afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda a matsayin “mummunan famu,” da kuma ƙololuwar rashin adalci ga ɗan uwansu. Sun bayyana takaici bisa sakin Maryam Sanda daga gidan yari, wanda suka kira da neman faranta wa danginta rai, ba...
“Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah Ya kawo dama ta afuwa, dole ne ya yi farin ciki. Ni da iyalina da masoyana mun yi murna ƙwarai,” in ji Lawan. “Na gode wa Allah da kuma Shugaba Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata a yaba masa.” Ya bayyana cewa rayuwa a gidan yari ta koya masa juriya da fahimtar cewa komai ƙaddara ce. “Tun kafin na bar kotu na sallama komai ga Allah. Na sani cewa duk inda mutum ya samu kansa, akwai darasi a ciki,” in ji shi. Bayan fitowarsa daga gidan yari, Faruk Lawan ya sauya tafiyarsa ta siyasa. Ya ce ya rabu da tafiyar Kwankwasiyya da aka san shi da ita, duk da cewa har...
Rahotanni sun bayyana cewa wani ƙazamin faɗa ya barke tsakanin wata ƙabilar Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da ƙungiyar Hamas a yankin zirin Gaza bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila. A ranar Litinin da aka fara musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ne rahotanni suka ɓulla game da faɗan da ya ɓarke tsakanin mayaƙan Hamas da ƙabilar Doghmush a ranar Lahadi. Wani jami’in Hamas ya bayyana cewa an samu asarar rayuka daga kowane ɓangare a yayin musayar wutan daga misalin ƙarfe 9.30 na dare ranar Lahadi. Wani mazaunin yankin Sebra da ke Birnin Gaza, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa “Mayaƙan Hamas kimanin 200 ne suka zo aka fafata da su, har sai da suka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba. Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiyar malaman ASUU za ta iya bi don warware matsalar ta ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba. Domin sauke shirin, latsa nan
Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye. Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na ƙuri’u a rumfunan zaɓe da dama. Sun buƙaci Shugaba Paul Biya, wanda ke neman wa’adin mulki na takwas a zaɓen da ya gaggauta miƙa saƙon taya murna ga Issa Bakary Tchiroma. “Muna kira ga shugaban ƙasa mai barin gado da ya gaggauta taya sabon shugaban ƙasa murna,” in ji ƙungiyar,” in ji wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Anicet Ekane da Djeukam Tchameni, suka fitar a...
A cewar su, wannan sabon tsarin zai taimaka wajen gina dimokuraɗiyya mai ƙarfi da ɗorewa a ƙasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ilimi Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba October 13, 2025 Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a ranar Litinin. Piwuna ya ce ASUU ta tsaya tsayin daka tare da sauran ƙungiyoyin Malamai kamar CONUA, da NAMDA, da SSANU, da NASU, wajen goyon bayan yajin aikin da ke gudana. Ya zargi Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da ƙoƙarin rarraba malamai ta hanyar yin alƙawarin biyan wasu ma’aikata albashi. “Ya na ƙoƙarin rarraba kan mu, amma kan mu a haɗe yake. Babu wanda...
Hukumar da ke shirya gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) ta hukunta Kano Pillars FC da tarar Naira miliyan ₦9.5, tare da rage musu maki uku da ƙwallaye uku, bayan magoya bayansu sun kutsa cikin fili a yayin wasan da suka buga da Shooting Stars a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano. Hakan ya sa NPFL ta rufe filin wasan tare da umartar cewa Pillars za ta ci gaba da buga wasanninta na gida a filin Muhammad Dikko a Katsina. A cewar NPFL, hukuncin ya fito ne bisa dokar C1.1, wadda ke hukunta hare-haren da ake kai wa tawagar baƙi da jami’an wasa. Hukumar ta ce wannan mataki yana nufin tabbatar da tsabtace filayen wasa daga tashin hankali da rashin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA October 13, 2025 Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025
Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara himma wajen aikin al’umma (CSR), tana taimakawa hukumomi masu ruwa da tsaki da al’ummomi domin karfafa zaman lafiya da tattalin arziki. A cewar Issa-Onilu, wannan nasara da aka samu a watan Satumba na nuna cewa hukumar Customs ba wai kawai tana cigaba da gyara ba ce, har tana kafa sabon ma’auni na kwarewa da ingantaccen aiki a tsarin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa...
Shugaban kasar iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana a yau a wajen taron da yayi da gwamnoni jihohin kasar baki daya cewa jamhuriyar musulunci ta iran tana da karfin juriewa duk wata matsin lamba kuma ba zata taba risunawa duk wani nuna karfi ko cin zarafi ba. Yace kasa kamar iran mai makwabta 16 ba abu ne mai sauki a kakaba mata takunkumi ba, idan muka kara gyara dangantakarmu da makwabtanmu cin sauki zamu iya shawo kan matsin lambar da muke fuskanta, Har ila yau ya kara da cewa ba zasu sa ido kan iyakokin ko wacce kasa ba, amma zamu rufe ido kan duk kasar da ta nemi shiga harkokin kasar ba tare da bata lokaci ba, Iran tasha nanata...
Ya kuma ce matakan takaita fitar da ma’adanan farin karfe da Sin ta dauka a baya bayan nan, ba su da alaka da kasar Pakistan. Yana cewa matakai ne da gwamnatin Sin ta dauka bisa doka da oda da nufin inganta tsarinta na fitar da kayayyaki. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana October 13, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya October 13, 2025 Daga Birnin Sin Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina October 12, 2025
Ɗan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Sabon Gari Daga Jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya fice daga Jam’iyyarsa ta PDP. Honorabul Abdullahi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamishinan Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) ya alaƙanta ficewarsa da rikicin cikin gida da rabuwar kai da ya ki ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar. A ranar Litinin ya aike da wasikar ta ficewa ga Shugaban PDP na Mazabar Hanwa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, yana mai cewa rikicin ya hana shi taɓukawa matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya. Ya cewa saboda haka yana dacewar ficewarsa daga jam’iyyar ba tare da la’akari da siyasa ba, domin amfanin ɗauƙacin al’ummar mazabar. Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary...
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar. ‘Yan sanda a jihar Neja da ma Nijeriya ƙwararru ne don haka za su ci gaba da aiki da kuma nuna basira da ƙwarewa tare da ƙa’idarta ta sirrin rashin bayyana tushen bayanansu don samun sakamako mafi girma. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman wanda ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, ya bayyana cewa a kwanan baya ya halarci wani taron...
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar. Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu. “A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu. “A cikin sa’o’i 24 da...
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu ma’aurata da wasu mutane biyar bisa zarginsu da gudanar da ɗaurin aure ba tare da izinin iyayensu ba ko kuma bin tsarin addinin Musulunci a unguwar Nasarawa da ke cikin birnin Kano. Wadanda ake zargin sun hada da ango mai suna Aminu mai shekaru 23 da amaryarsa Sadiya mai shekaru 22. Sauran wadanda aka kama su ne Umar mai shekaru 24 wanda ya kasance wakilin ango; Abubakar, mai shekaru 23, wanda ya kasance waliyyin amarya; Usaina, mai shekaru 21; da kuma wasu ‘yan mata guda biyu wadanda suka kasance shaidu a yayin ɗaurin auren. Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano Ambaliyar Ruwa...
Wani mummunan rikicin ƙabilanci a ƙaramar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa ya yi ajalin mutane biyu, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka. Kakakin ’yan sanda ta jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin Operation Salama sun garzaya wurin domin dawo da zaman lafiya tare da cafke wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a rikicin. Ganau sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wasu da ake zargin Fulani ne suka kai farmaki ƙauyen Dagaceri, inda suka ƙona gidaje tare da kai wa mazauna garin hari da kibau a lokacin da suke barci. Rahotanni sun ce gidaje da dama sun ƙone...
A safiyar yau litinin ce majiyar gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan ko kuma ministan harkokin wajen kasar ba zasu halarci taron sanyawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin HKI da Falasdinawa a birnin Sharm sheikh na kasar masar ba. Saboda ba sa son haduwa da shuwagabannin kasashen yamma azzalumai wadanda da makaman sune aka kashe falasdinawa kimani 70,000 a gaza a cikin shekaru 2 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar gwamnatin na cewa shuwagabannin kasar Iran ba zasu amince su zauna kusa da wadanda suka kashe iraniyawa a cikin watan yunin da ya gabata, da kuma jinin mutanen da dama a yankin ba, suna mika masu hannu ba. A taron...
Magu ayyukan ceto a gaza sun gano gawakin Falasdinawa fiye da 320 a karkashin burbushin gine-ginen da aka rusa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tun bayan fara yakin tufanul Aksa shekaru biyu da suka gabata Falasdinawa kimani fiye da 10,000 suka bace. Kuma a zatun mafi yawansu suna bisne a karkashin burbushi na gine-ginan da HKI ta rusa a kansu a zikin gaza. Asbitoci a gaza ya zuwa yansu sun bada sanarwan karban gawakin Falasdinawa 323 wadanda aka zakulo karkashin burbushin gine-gine. Da HKI ta rusa a kansu. Labarin ya kara da cewa a lissafin MDD ya zuwa tsagaita budewa juna wuta a gaza HKI ta rusa gidajen falasdinawa 430,000 a gaza. Banda haka akwai...
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta. Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako. Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista...
“Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”. Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa. Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27...
An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya. Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse. Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben. Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka...
Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 9 tare da kwato kudi fansa kimanin Naira miliyan 5 a yankunan Magumeri da Gajiram a jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), Laftanar Kanar Sani Uba , ya ce sojojin da suke sintiri a yankunan ne suka hallakan mayakan bayan sahihan bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan ta’addan a kusa da Goni Dunari a Karamar Hukumar Magumeri. Sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025 ta ce, “Dakarun mu sun yi gaggawar daukar matakin dakile barazanar bayan da suka ga yadda ’yan ta’addan suka kona gidaje tare da tsoratar da mutanen yankin.” Ya bayyana cewa sojoji sun yi artabu da ’yan ta’addan ne bayan sun shafe sa’o’i hudu suna...
Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin tare da mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya. Kungiyar ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da da’a, kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da ingancin wasan kamar yadda hukumar NPFL da hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta tanada, Pillars ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su...
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa. Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako October 13, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin...
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja. Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja. Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025. Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan...
An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya. Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta gayyaci muqaddashin jakadan kasar Oman a kasarta Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gayyaci babban jami’in ofishin jakadancin kasar Oman a birnin Tehran a jiya Lahadi, bayan wani rade-radin da ake yadawa cewa; Mutane biyu a kasar Oman sun mutu sakamakon shan ruwan ma’adinai da aka shigo da su daga kasar Iran. Bayan wasu zarge-zarge marasa tushe da wasu kafafen yada labarai na kasar Oman suka wallafa na alakanta mutuwar mutane biyu a masarautar Oman da shan ruwan ma’adinan da aka shigo da su daga kasar Iran, a ranar Lahadin da ta gabata ne Abdul Rasoul Shabibi, shugaban sashen ma’aikatar kula da tekun Farisa ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ya gayyaci mai kula...
Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba. Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.” Trump ya kara da...
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane afuwa, ciki har da waɗanda suka aikata manyan laifuka. A cikin saƙon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ana yin afuwa ne ga waɗanda aka yi wa rashin adalci ko waɗanda suka nema gafara bayan sun shafe wani lokaci a gidan yari. Yajin Aikin ASUU: Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna Ya ce a wannan karon an yi wa masu safarar ƙwayoyi, masu garkuwa da mutane, masu kisan kai, da kuma masu cin hanci da rashawa afuwa. Atiku,...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025
An wallafa wasu kundi 2 masu kunshe da ra’ayoyin shugaba Xi Jinping na kasar Sin kan batutuwan da suka shafi mata da yara da kungiyar mata ta kasar, da kuma ra’ayoyinsa kan karfafa zumunci da akidu da al’adun iyali, cikin harsunan Rashanci da Faransanci da Spaniyanci da Larabci, bayan irinsu da aka wallafa cikin harsunan Ingilishi. Madabba’ar tattara bayanai da fassara ta kwamitin tsakiyar JKS ce ta wallafa kundin, wadanda ake sa ran za su taimakawa masu karatu na kasa da kasa kara fahimtar ra’ayoyin shugaba Xi da dabaru da shawarwarin da Sin ta gabatar game da daukaka daidaiton jinsi da raya dukkan harkokin da suka shafi mata a fadin duniya. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin...
Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu. A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana. Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja “Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar. Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin...
Sufeton ƴansanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya maye gurbin Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya, CP Ajao Adewale, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba da yake fuskanta saboda rashin gamsuwa da aikinsa tun bayan karɓar ragama daga CP Benneth Igwe. Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa sauya shi ya shafi yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a Abuja, musamman bayan harin fashi da makami da ya yi sanadin mutuwar mai gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin ɗin ARISE, Somtochukwu Maduagwu, da mai gadi Barnabas Danlami, a Katampe, ranar 29 ga Satumba, 2025. Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna NAFDAC Ta Rufe Manyan Shaguna 2 Na...
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sharhi:...
Kotun daukaka kara ta Marseille ta tabbatar da soke dokar da ta bayar da umarnin rufe makarantar sakadare ta Musulinci da ke birnin Nice. A cikin wata sanarwa da ya fitar, lauyan makarantar, Sefen Guez Guez, ya yaba da nasarar ta uku a jere” tare da bayyana fatan cewa “za a daina tsananta wa wannan makaranta gaba daya. Takadammar data shafi makarantar ta hana da Rashin haske kan kudadenta, wanda hukumomjin yankin ke zargin makarantar da ta ina take samun kudadenta kamar yadda doka ta tanada. ” An bude makarantar ne a cikin shekarar 2016 a gundumar Ariane, kuma makarantar mai zaman kanta a halin yanzu tana da dalibai 130. Rahotanni sun ce makarantar, wadda wata kungiya ce mai alaka...
Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da ta danganta da na karya da Amurka ke yi wa kasar cewa ta na da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, tana mai daukar wadannan zarge-zarge a matsayin wani makirci na siyasa da nuna kiyayya. A cewar ma’aikatar harkokin wajen Cuba, hukumomi “ba su da wani takamaiman bayani kan ‘yan kasar Cuba” da suka shiga ko kuma suke shiga cikin rikicin “da kansu” a cikin “dakarun sojan bangarorin biyu da ke rikici da juna” tsakanin Rasha da Ukraine. Tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, kotunan kasar Cuba sun saurari kararrakin laifuka tara da suka shafi ayyukan sojan haya, inda suka yanke wa wadanda ake tuhuma 26 hukuncin zaman gidan yari tsakanin...
Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere. Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha. Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru. Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan Ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira miliyan 1.5. An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje. ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Dukkaninsu suna hannun ’yan sanda. Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa. Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya...
Sojojin Nijeriya sun kashe wani kwamandan ƙungiyar ƴan ta’adda IPOB/ESN da ake nema ruwa a jallo, mai suna ‘Alhaji’, tare da wasu mutane 26 a jerin hare-haren da suka kai a sassan ƙasar tsakanin 8 zuwa 11 ga Oktoba, 2025. Rundunar Sojin ta ce an kuma ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace makamai, da harsasai, da kuɗaɗe. A kudu maso gabas, Sojojin Operation UDO KA sun kai farmaki a Izzi, jihar Ebonyi, inda suka kashe ‘Alhaji’ bayan ya yi yunƙurin kwace bindiga daga hannun wani Soja lokacin kama shi. Haka kuma, a jihar Imo, an rusa wata maboyar IPOB/ESN da ake amfani da shi wajen horar da mambobi. Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB...
Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje. A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka suna da wasu damarmakin da idan suka yi sa’a za su iya tsintar kansu a gasar a badi. Kasar Masar ta wuce Burkina Faso da maki biyar, sannan idan ta samu nasara a kan Djibouti shikenan ta samu tikiti. Ita kuma kasar Djibouti tana can karshen teburi ne, domin maki daya tak take da shi a wasa takwas da ta buga. Idan ma...
A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau? A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa. Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News. Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Ɗaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki. Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a...
Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa. Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama. A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin. Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi. Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce kasar Iran ta yi maraba a tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo karshen kisan kiyashi wa Falasdinawa, amma ya kara da cewa HKI ba abar amincewa bace, don haka tana iya yaudara da kuma kawo karshen tsagaaita budewa junan wutar gaba daya. Abu ne da saba yi don haka Falasdinawa su yi hattara. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa, Iran tana maraba da dukkan abinda zai kai ga kawo karshen kisan kiyashi a gaza, wanda ya dau shekaru 2 ana yi. Ministan ya jawo hankalin Hamas da sauran Falasdina kan amincewa da duk abin HKI...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Makaie ya tir da HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a kudancin kasar, Lebanon wanda ya sabawa da farko yarkeniyar tsagaita wutan da ta cimma da kungiyar Hizbulla a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 sannan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Baghaei ya bayyana cewa ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon a kai a kai, da kuma shirun da kasashen duniya suka yi duk sun sabawa dokokin kasa da kasa wadanda HKI da wadanda suke riya daukar nauyin kola da cewa an dabbaka yarjeniyar MDD na kuduri mai lamba 1107. Ya zargi kasashen Faransa da kuna Amurka wadanda suka gabatar da kansu a matsayin masu lamuni don aiwatar...
Kasar China ta maida martani kan kasar Donal Trump na kasar Amurka, wanda ya karawa kasar kudaden fito 100% na kayakin kasar da ke shigowa Amurka. SHafin yanar gizo na ArabNews ya nakalto kasar China a jiya Asabar tana cewa zata dauki matakan da suka dace kan Karin kudanen fito na 100% wanda shugaban Trump yayi. Kuma ta yi kira ga Trump kan cewa ya rungumi tattaunawa da kasar China ya fi masa kan barazana gareta. Ma’aikatar kasuwanci na kasar China ta bayyana cewa, basa son yakin kudaden fito amma basa tsoronta. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name*...
Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.” Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna October 12, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Yi...
Daga cikin wadanda shugaban kasar ta Nigeria ya yi wa afuwa da kawai Maryam Sanda ‘yar shekaru 37 wacce aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunta da kashe mijinta da wuka a 2017. Mai Magana da yawun shugaban kasa Bayo Onangua ya saki bayanin afuwar da shugaban kasar ya yi, wacce kuma ta hadad a Faruka Lawan tsohon dan majalisa da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a 2021. Sai kuma Ken Saro-wiwa wanda dan fafutuka ne mai rajin kare muhalli a yankin Ogoni da aka zartarwa hukuncin kisa a 1995. Har ila yau afuwar ta shugaba Tunibu ta shafi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa wanda aka zartarwa da hukuncin kisa a 1986 saboda juyin Mulki....
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki. Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki. Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,” A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba...