Faransa : An yi Zanga-zangar adawa da isar da makamai da kayan aikin soja zuwa Isra’ila
Published: 26th, October 2025 GMT
A birnin Paris, an gudanar da wata zanga-zanga a filin jirgin saman Roissy-Charles-de-Gaulle game da shigar da makamai da kayan aikin soja na Faransa zuwa Isra’ila.
An shirya zanga-zangar ne bisa kiran wasu kungiyoyi da nufin bayyana rawar da Faransa ke takawa wajen samar wa sojojin Isra’ila makamai da kayan soji, musamman ta babban filin jirgin saman kasa da kasa na Roissy-Charles-de-Gaulle.
A cikin sanarwar manema labarai, da suka fitar masu shirya zanga zangar sun yi Allah wadai da jigilar kayan aikin sojan inda suka nemi a dakatar da duk kayan da Faransa ke fitarwa wadanda za su iya taimakawa wajen kai hare-haren sojojin Isra’ila.
Wannan yunkurin ya zo ne bayan da gidan yanar gizon bincike na Faransa mai suna Disclose ya bayyana cewa za a mika wani rukunin na’urori da kamfanin Sermat na Faransa ya kera, ga kamfanin Elbit Systems na Isra’ila, wadannan an yi su ne don jiragen sama marasa matuka na Hermes 900, wadanda sojojin Isra’ila ke amfani da su sosai a yankin Gaza.
Bayanai sun ce wasu kasashen Turai irinsu Spain, Netherlands, Belgium, da Italiya sun dakatar da fitar da kayan yakinsu zuwa Isra’ila tun bayan da yakin Gaza ya tsananta.
Faransa, a nata bangaren, ta ci gaba da ba da izinin sayar da makamai wanda darajarsu ta kai Yuro miliyan 27.1 a shekarar 2024.
A watan Janairun 2024, Kotun Duniya ta yi gargadi game da kisan kare dangi da Isra’ila ta aikata a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas : Ba za mu bari Isra’ila ta sami wata hujja ta ci gaba da yaki a Gaza ba October 26, 2025 ‘Yan Ivory Coast na jiran sakamakon zaben shugaban kasa October 26, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Shugaban Amurka Zai Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rudu October 26, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Ce: Iran, Rasha Da China Sun Aike Da Sako Mai Muhimmanci October 26, 2025 Ja’afari: Iran Tana Da Isassun Makamai Masu Linzami Masu Cin Zangogi Daban-Daban October 26, 2025 Dan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Ce: Dole Ne A Hakunta Isra’ila Kan Laifukan Da Ta Aikata October 26, 2025 Mayakan Kungiyar Kurdawa Ta PKK Sun Fice Daga Turkiyya Zuwa Iraki October 26, 2025 Iran Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kungiyar Tattalin Arziki TA “Eco” A Gobe Litinin October 26, 2025 Bahrain: Fursunoni 90 Suna Yajin Cin Abinci Saboda Neman ‘Yanci October 26, 2025 Shugaban Kasar Nigeria Ya Yi Sauye-sauye A Rundunonin Sojan Kasar October 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Akan Yara Da Matan Har Zuriya Mai Zuwa
MDD ta bayyana cewa a tsakanin kowadanne mutanen Gaza 4, daya daga cikinsu yana fama da yunwa.
Mai Magana da yawun kungiyar Agaji ta tarayyar turai, May Musa Sayegh, ta yi ta’aliki akan wannan adadin na masu fama da yunwa a Gaza, inda ta ce; Wannan shi ne hakikanin abinda yake faruwa a kasa, kuma ya shafi mata manya da ‘yan mata da kuma kananan yara masu yawa.”
May Musa Sayegh ta fada wa tashar talabijin din aljazira cewa; Sakamakon hare-hare na tsawon shekaru biyu da kuma rashin samun damar shigar da kayan agaji,musamman a arewacin Gaza aka fada cikin wannan halin.
Sayegh ta kuma ce; ta fuskar kiwon lafiya, al’amurra suna kara tabarbarewa, domin mutane suna rayuwa cikin bakin talauci, ga shi kuma ba a kai musu kayan agaji mafi karanci na bukatun yau da kullum.
Haka nan kuma ta yi ishara da yadda cutuka suke yaduwa saboda karancin ruwa da kuma rashin magani, da hakan yake haddasa asarar rayukan mata masu ciki da kuma kananan yara.
Bugu da kari,Sayegh ta ce idan har ba a shigar da taimako cikin yankin da gaggawa ba, kuma ya zama da yawa wanda zai ishi mutane, to wannan matsalar za ta ci gaba da wanzuwa.
A ranar 10 ga watan Oktoba ne aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce a kowace rana HKI take karyawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Shugaban Amurka Ya Soke Shirin Ganawa Da Takwaransa Na Rasha October 23, 2025 Venezuela Ta Sanar Da Mallakar Makamai Masu Linzami Samfurin “ Igla-s” 5,000 Domin Kare Kanta October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci