Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin
Published: 25th, October 2025 GMT
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa su na nazarin dokoki guda 69 da kuma buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙudirin ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278 bisa ga tsarin kundin mulkin 1999.
Barau, wanda shi ne shugaban Kwamitin Bita na Tsarin Mulki a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ne a taron haɗin gwuiwa da kwamitocin majalisar dattawa da kwamitocin majalisar wakilai kan gyare-gyaren dokokin tsarin mulki da suka gudanar a Lagos.
Ya jaddada cewa an dauki lokaci mai tsawo wajen tattaunawa da al’umma da masu ruwa-da-tsaki da ƙungiyoyi daban-daban, domin kawo waɗannan ƙuduri a gaban majalisar.
Ya kuma bayyana burin majalisar cewa za ta miƙa kashi na farko na gyare-gyaren tsarin mulki ga majalisun jihohi kafin ƙarshen shekarar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja
An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja.
Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar BeninAn gano gawarsa ne da safiyar ranar Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa an ƙone al’aurarsa, sannan an samu kwalin ashana a gefen gawarsa.
Shugaban al’ummar yankin, Malam Mahmud Dalhatu Iya, ya shaida wa Aminiya cewa iyalan mamacin sun riga sun gano gawar kuma an riga an binne shi.
Ya ce, “An sanar da ni cewa an ga wata gawa ta lalace a wani gini da ba a kammala ba a cikin rukunin gidajenmu.
“Mun kai wa ’yan sanda rahoto. Muna nan lokacin da wani ya zo ya ce shi abokin mamacin ne, ya kuma ya ɓace tun ranar Alhamis. An yi wa gawar sutura don yi mata jana’iza a lokacin da nake magana da ku.”
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “A yau, 7 ga watan Disamba 2025, da misalin ƙarfe 10 na safe, an samu rahoto cewa an ga gawa a bayan rukunin gidaje na Talba da ke kan titin Kpakungu.
“Jami’an ’yan sandan Kpakungu sun je wajen kuma sun gano gawar ta lalace cikin wani gini da ba a kammala ba.
“Daga bisani iyalansa suka tabbatar da cewa Auwal Yakubu ne, mai shekaru 45, mazaunin wannan yanki.”
Ya ƙara da cewa, “Ana zargin cewa an jefar gawar ne a wajen, domin an ruwaito ya ɓace tun a ranar 4 ga watan Disamba kafin a gano shi da safiyar yau.
“An kai gawar asibiti, kuma an fara bincike don gano musabbabin rasuwarsa.”