Rasha ta miƙa wa Ukraine sojoji 1,000 da suka mutu a fagen daga
Published: 24th, October 2025 GMT
Rasha ta miƙa wa Ukraine gawarwakin sojoji 1,000 da suka mutu a fagen daga, a cewar wata hukumar gwamnatin Ukraine da ke kula da lamurran fursunonin yaƙi.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa ita ma Rashar ta karɓi gawarwakin sojoji 31 daga ɓangaren Ukraine.
Messi ya tsawaita kwantiraginsa da Inter Miami Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zangaMusayar fursunonin yaƙi da kuma gawarwakin sojoji da suka mutu na daga cikin al’amuran haɗin gwiwa da har yanzu ke gudana tsakanin Kyiv da Moscow, tun bayan mamayar da Rasha ta kai Ukraine a Fabrairun 2022.
Rahotanni daga Kyiv sun ce musayar gawarwakin na daga cikin yarjejeniyar da ɓangarorin biyu suka cimma domin bai wa iyalai damar binne ’yan uwansu cikin mutunci.
“A yau aka gudanar da musayar gawarwaki,” in ji Hedikwatar Tsare-tsaren Ukraine kan Fursunonin Yaƙi a wani saƙo da ta wallafa a shafukan sada zumunta.
Ukraine ta bayyana cewa a musayar da aka yi a lokutan baya, Rasha ta miƙa mata gawarwakin sojojinta yayin da ita ma ke mayar da na ɓangaren Rasha a cikin wani tsarin da ƙungiyar agaji ta Red Cross ke taimakawa wajen sa ido.
A watan Yuli, Agusta da kuma Satumba ne Kyiv ta sanar da karɓar gawarwakin sojoji 1,000 daga Rasha, abin da ke nuna yawan asarar rayuka da ake yi a fagen daga tsakanin ƙasashen biyu.
Hedikwatar ta ce hukumomin tsaro za su fara aikin tantance gawarwakin da aka dawo da su a nan gaba kaɗan, tana mai gode wa Ƙungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC) bisa rawar da ta taka wajen tabbatar da nasarar musayar gawarwakin.
A watan Fabrairun bana, Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya shaida wa kafafen yada labaran Amurka cewa ƙasarsa ta rasa sojoji fiye da 46,000, sannan akwai dubbai da ake ɗauka a matsayin wadanda suka ɓata a fagen daga.
Wasu alƙaluma da kafafen labaran BBC da Mediazona suka tattara, sun tabbatar da mutuwar sojojin Rasha sama da 135,000 tun bayan fara yaƙin — duk da cewa sun ce akwai yiwuwar adadin ya zarta haka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rasha Ukraine gawarwakin sojoji
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kama Fitaccen Ɗan Bindiga Babawo Badoo Da Wasu 37 A Filato
Sanarwar ta ce, sojojin sun yi aiki da sahihan bayanan sirri, sun kama wanda ake zargin tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, da wata mujalla cike da harsashai na musamman masu tsawon 7.62mm har guda 10, wayar hannu, da kuma kudi naira 12,000.
“Sakamakon nasarar da aka samu ya haifar da babbar illa ga kungiyar masu tada zaune tsaye da ke aiki a yankin Arewa ta Tsakiya,” in ji sanarwar
ShareTweetSendShare MASU ALAKA