Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
Published: 18th, October 2025 GMT
“Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar.
A cewar rundunar sojoji, an gano gawarwakin Lance Corporal Femi da matarsa a cikin gidansu dake gini na 15, daki mai lamba 24, Corporals and Below Kuarters, a cikin sansanin.
Binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a lokacin kuma ya nemi izini daga babban jami’i domin ya kula da wasu harkokin kansa kafin ya dawo aiki.
“Rundunar Sojin Nijeriya tana matukar bakin ciki kan wannan lamari, sannan tana taya iyalan, abokan aiki, da abokan marigayin jimami kan wannan babban rashi.
“Rundunar soji kuma tana addu’ar Allah ya jikansu cikin salama,” in ji Nwachukwu.
An ajiye gawarwakin marigayin, sannan an fara gudanar da cikakken bincike don gano dalilan da suka haifar da wannan abin takaici.
“Brigadier Janar Ezra Barkins, kwamandan 22 Armoured Brigade, ya tabbatar wa jama’a cewa sakamakon binciken zai kasance a bayyane kuma za a duba shi sosai, tare da daukar matakan da suka dace don hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba,” in ji Nwachukwu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun tallafa wa mutanen Yobe da N23m bayan harin kuskure
Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta bai wa mutanen garin Buhari da ke Karamar Hukumar Yunusari a Jihar Yobe, tallafin Naira miliyan 23 tare da alƙawarin gina rijiyar ruwa mai amfani da hasken rana.
Wannan tallafi ya biyo bayan wani harin kuskure da jiragen yaƙin rundunar suka kai a watan Satumba 2021, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane takwas da jikkata wasu 30.
Wasu jiga-jigan ADC za su dawo jam’iyyarmu — Shugaban Jam’iyyar APC HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiyaBirgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritay), wanda shi ne mai bai wa Gwamna Buni shawara kan harkokin tsaro, ya bayyana cewa wannan tallafi ya nuna tausayin gwamnati da rundunar sojan sama ga al’ummar garin.
Ya ce, tun bayan faruwar lamarin, gwamnan Yobe Mai Mala Buni da Gwamnatin Tarayya suna ƙoƙari wajen taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
A madadin Babban Hafsan Sojin Sama, Komando U.U. Idris na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), ya ce rundunar ta bayar da Naira miliyan 23 ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma naira dubu 500 ga kowane mutum daga cikin waɗanda suka jikkata.
Ya ƙara da cewa, rundunar ta yi wa wadanda suka rasu addu’a, tare da fatan Allah Ya kiyaye faruwar irin hakan a nan gaba.
A nasa jawabin, Alhaji Ali Lawan, wanda ya wakilci al’ummar garin Buhari, ya gode wa rundunar Sojin Sama bisa wannan taimako.
Ya kuma roƙi jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen yaƙar ’yan ta’adda, domin har yanzu yankin na fuskantar barazanar tsaro.