Sheikh Naim Qassem: Hezbollah a shirye take ta fuskanci Isra’ila idan yaki ya barke
Published: 27th, October 2025 GMT
Sakataren Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, ya tabbatar da cewa Hizbullah ta shirya don fuskantar isra’ila, yana mai bayyana cewa duk da cewa ba su da niyar fara yaki, amma suna shirye su kare Lebanon idan yaki ya barke.
Sheikh Qassem a zantawarsa da tashar Al-Manar TV ya jaddada cewa idan aka tilasta musu yin yaki, tabbas za su fuskanci Isra’ilawa da dukkanin karfinsu, kuma ba za su bar Isra’ila ta mamaye kudancin Lebanon ba,ko da kuwa hakan zai kai ga shahadarsu ne baki daya.
Ya yi ishara da irin ayyukan wuce gona da iri da isr’ila ke yi akullum rana ta allaha kan kasar Lebanon a kan idanun duniya, wanda hakan ya yi hannun riga da yarjejeniyar dakatar dayaki da aka cimmawa tare da ita, a maimakon masu shiga su taka mata burki, har kullum Amurka kara matsa lambta take yi kan kasar Lebanon domin amincewa da sharuddan Isra’ila.
Bugu da ƙari, ya yi gargaɗin cewa “idan maƙiya suka ƙaddamar da yaƙi a Lebanon, ba za su cimma komai ba,” yana mai kira da a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta gaba ɗaya.
Ya ƙara da cewa “kowa zai amfana idan aka tabbatar da yarjejeniyar.
Sakataren Janar na Hizbullah ya bayyana cewa Hizbullah ba za ta iya hana barkewar yaki ba, amma kuma za ta hana makiya cimma burinsu a kan kasar Lebanon.
Dangane da binciken da ake yi kan kutsen makiya a cikin Hizbullah, Sheikh Naim ya yi shara da cewa kungiyar “tana ci gaba da bincikenta a kan wannan batu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Catherine Connolly ta lashe zaben shugaban Ireland October 27, 2025 Hamas ta sake jaddada wajabcin aiwatar da Shirin tsagaita wuta a Gaza October 27, 2025 Sudan: Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur sun karyata RSF kan kwace iko da El Fasher October 27, 2025 Araghchi : Iran na maraba da tattaunawar diflomatsiyya da Amurka amma cikin mutunta juna October 26, 2025 Ana Zaman dar-dar gabanin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Kamaru October 26, 2025 Faransa : An yi Zanga-zangar adawa da isar da makamai zuwa Isra’ila October 26, 2025 Hamas : Ba za mu bari Isra’ila ta sami hujjar ci gaba da yaki a Gaza ba October 26, 2025 ‘Yan Ivory Coast na jiran sakamakon zaben shugaban kasa October 26, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Shugaban Amurka Zai Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rudu October 26, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Ce: Iran, Rasha Da China Sun Aike Da Sako Mai Muhimmanci October 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba
A wani rahoton da jaridar Jerissalam Post” ta buga ta ambaci cewa; Tun bayan farmakin 7 ga watan Oktoba 2023, ana kara samun matalauta da talauci.
Rahoton ya yi nuni da cewa karuwar talaucin yana da alaka ne da yadda farmakin 7 ga watan Oktoba ya yi tasiri a cikin tattalin arziki “Isra’ila”.
Haka nan kuma rahoton ya ce, da akwai dubban iyalai yahudawa wadanda gabanin yaki, suke rayuwa cikin yanayi mai kyau ta fuskar tattalin arziki, yanzu sun zama matalauta. A dalilin haka cibiyar da ta shirya rahoton ta “ Latit” tana yin gargadi akan cewa; za a iya samun ci gaba da yaduwar talaucin, domin iyalai da dama suna gogoriyon yadda za su iya biyan bukatar yau da kullum, duk da cewa suna da cikakken aiki.
Ita dai kungiyar “Latit” ta ‘yan sahayoniya ce wacce aka kafa a 1996 domin fada da talauci da kuma rashin abinci.
Haka nan kuma rahoton ya bayyana cewa; Adadin iyalan da suke fama da talauci a cikin ‘yan sahayoniyar sun kai 867,000, saboda ba su da lamunin abinci. Adadin daidaikun wadannan iyalan sun kai miliyan 2.8, daga cikinsu da akwai kananan yara miliyan 1.18.
Haka nan kuma wani sashen na rahoton ya ce, talaucin yana karuwa ne da kaso 27-29%.
Da dama daga cikin iyalan ‘yan sahayoniyar suna rayuwa ne ta hanyar samun taimako da tallafi na abinci,domin suna amfani da kudaden da suke samu na aikin yi, domin biyan kudaden wuta da sayen magunguna.
Kaso 40% na tsofaffi suna fama da matsalar tabarbarewar rashin lafiya, da ya faro tun daga farkon yaki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka AU Ta yi Tir Da Harin RSF A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80 December 8, 2025 MِِِِDD: Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci