Leadership News Hausa:
2025-10-22@23:28:00 GMT
Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera
Published: 23rd, October 2025 GMT
Tun daga lokacin da kasar Sin ta fara kera jiragen kasa masu saurin gudu a shekarar 2007 da samfurin CRH1 mai gudun kilomita 250 cikin sa’a guda, ba ta tsaya ba har zuwa yanzu da ta kera wannan sabon na zamani samfurin CR450 wanda shi ma an yi masa tsarin da za a ci gaba da inganta shi.
Wannan fasaha wacce ta kara jaddada matsayin kasar Sin na ci gaba da zama jagora a fagen kere-keren jirgin kasa mafi gudu a duniya, ba kasar Sin kawai za ta amfanar ba har ma da sauran sassan duniya musamman a wannan zamani da kasar ta Sin ke kara bude kofarta ga kasashen waje da kuma neman cimma burin samar da al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya a duniya.
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan
ShareTweetSendShare MASU ALAKA