Babban Lauyan Jihar Kwara Ya Tabbatar da Gudanar da Adalci da Kare Hakkokin Mace
Published: 23rd, October 2025 GMT
Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kwara, Barista Senior Ibrahim Sulyman, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da inganta adalci, kyakkyawan shugabanci, da samar da damar samun shari’a ga kowane ɗan ƙasa.
Sulyman ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai na watanni uku (quarterly ministerial briefing) da aka gudanar a birnin Ilorin.
A cewarsa, Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kwara tana daga cikin ma’aikatun da ke ba da muhimmanci ga hidima ga jama’a, wadda ke da alhakin gurfanar da masu laifi a kotu, kare gwamnati, tsara da tantance takardun doka, da kuma ba da shawarar doka ga sauran ma’aikatun gwamnati.
Ya bayyana cewa ma’aikatar na aiki ta hannun sassa guda shida (directorates) da kuma cibiyoyi biyu (centres), waɗanda ke taimakawa wajen tabbatar da adalci da ingantaccen gudanar da ayyukan gwamnati a jihar.
Daga cikin nasarorin da ma’aikatar ta samu a wannan zangon, Sulyman ya ce sun haɗa da tsarawa, shirya, da tantance sama da yarjejeniyoyi da kudurori 100, tare da ƙara yawan kudaden shiga ga gwamnati.
Babban Lauyan ya yabawa ma’aikatan dukkan sassan ma’aikatar bisa jajircewarsu da gudunmawar da suka bayar wajen cimma waɗannan nasarori a cikin lokacin da aka tantance.
Ali Muhammad Rabiu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jihar Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Kwara Ta Ware Naira Biliyan 8 Don Biyan Haƙƙin Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya
Gwamnatin Jihar Kwara ta ware kimanin Naira Biliyan 8 da miliyan dari daya domin biyan haƙƙin fansho da giratuti na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka yi ritaya.
Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Dakta Hauwa Nuhu, ce ta bayyana haka a yayin taro da ma’aikatun gwamnati karo na uku, wanda aka gudanar a zauren taro na ma’aikatar kuɗi a Ilori.
A cewarta, za a raba Naira Biliyan biyar da miliyan dari shida ga tsoffin ma’aikatan jiha a matsayin giratuti, yayin da aka ware Naira Biliyan biyu da miliyan dari biyar domin tsoffin ma’aikatan kananan hukumomi.
Dakta Nuhu ta jaddada cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da biyan fansho da giratuti a hankali domin tabbatar da cewa sauran ayyukan ci gaban jama’a ba su tsaya ba.
Ta bayyana cewa adadin giratuti da fansho ya ninka saboda aiwatar da sabon tsarin albashi na Naira Dubu Talatin da Naira Dubu Saba’in, tare da daidaiton da aka yi ga masu ritaya.
Kwamishinar ta kuma tabbatar da cewa babu wani tsohon ma’aikacin karamar hukuma ddake bin gwamnati bashi, sai waɗanda suka ƙi bayyana a lokacin tantancewar da aka gudanar a dukkanin kananan hukumomi 16 na jihar.
Ali Muhammad Rabi’u