2025-10-19@08:46:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1094
«mashigar Rafah»:
Majiyar hatkwatan sojojin Najeriya ta musanta labaran da suke yaduwa kan cewa, an fasa gudanar da faretin cika shekaru 65 da samun yencin kan kasar a ranar daya ga watan Octoba ne saboda yunkurin yi wa shugaba Bola Ahmad Tunubu juyin mulki ne. Jaridar daily Trust ta Najeriya ta nakalto majiyar sojojin kasar na musanta aukuwar haka, kuma tace labarin jita-jita ne wanda bai da kanshin gaskiya a cikinsa. Babu wani kokarin juyin mulki a kasar, inji majiyar. Sojojin sun ce an fasa gudanar da faretin cika shekaru 65 da samun yencin kan kasar ne, saboda bawa shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu damar halattan wasu tarurruka masu muhimmanci a kasashen waje, kuma fasawar bai da dangantaka ko kadan da juyin...
Ofishin Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a ranar Asabar cewa “Mashigar Rafah a Gaza za ta kasance a rufe har sai abin da hali ya yi a nan gaba.” Ofishin Netanyahu ya kara da cewa, bude mashigar ya dogara ne bisa ga yadda Hamas ta aiwatar da tsarin yarjjeniyar da aka cimmawa wajen mika gawawwakin Isra’ilawa da ke hannunta. Wannan bayanin ya zo ne jim kadan bayan da ofishin jakadancin Falasdinu a Masar ya sanar da cewa za a sake bude mashigar Rafah da ke kudancin zirin Gaza a ranar Litinin mai zuwa. A nata bangaren, kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, matakin da Netanyahu ya dauka yana a matsayin keta sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware kimanin Naira Miliyan 400 domin gina sabbin tashoshin samar da ruwan sha na hasken rana a kananan hukumomi guda biyar na jihar. Manajan Darakta na hukumar ruwa ta jihar, Injiniya Zayyanu Rabi’u Kazaure, ne ya bayyana hakan a Dutse. A cewarsa, an tsara aikin ne domin a gina tashoshin a Hadejia, Ringim, Birnin Kudu, Kafin Hausa da kuma sabon rukunin gidaje na Kazaure. Injiniya Zayyanu Rabi’u ya bayyana cewa samar da ruwan sha yana daga cikin muhimman shirye-shiryen wannan gwamnatin a jihar. Ya yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon bayanta wajen tabbatar da samar da ruwan sha mai tsafta ga al’umma. Usman Muhammad Zaria
Gusau, ya ƙara da cewa binciken da ake yi kan wasu jami’ai 16 ba shi da alaƙa da wani juyin mulki, illa kawai don tabbatar da ƙwarewar aikin soja. Ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa dakarun soji suna nan daram da goyon bayan kundin tsarin mulki da kuma gwamnatin Shugaba Tinubu, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da wannan rahoton. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna October 18, 2025 Manyan Labarai Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi October 18, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn...
Wasikar Iran, Rasha da China ga Majalisar Dinkin Duniya dangane da kawo karshen kuduri mai lamba 2231 Mataimakin ministan harkokin wajen kasar mai kula da harkokin shari’a da kasa da kasa ya sanar da cewa, kasashen Iran, Rasha, da China sun aike da wata wasika ta hadin gwiwa zuwa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dangane da kawo karshen kudurin kwamitin sulhu mai lamba 2231. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya bayyana irin gagarumin yunkurin diplomasiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke yi na kawo karshen kudurin kwamitin sulhu mai lamba 2231 a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin...
Bayan dawowarsa kasar Sin, Yang ya ci gaba da koyarwa a jami’ar Tsinghua, inda cikin sama da shekaru 20 ya bayar da muhimmiyar gudummawa wajen kyankyashe, da horar da sabbin masu hazaka, da yayata musayar ilimi tsakanin sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai October 18, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka October 18, 2025 Daga Birnin Sin Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO October 17, 2025
A Madagaska jiya Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar ta rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa. Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha. Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar. A ranar Talata da ta gabata ne, Randrianirina ya sanar da juyin mulkin kwace Mulki a kasar yana mai danganta hakan da rashin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, da keta hakkokin bil’adama. A kuma...
Aƙalla makarantun gwamnati 188 ne aka rufe sakamakon mtsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya. Binciken da wakilanmu suka gudanar ya nuna cewa, an rufe makarantu da dama a yankin saboda hare-haren da ’yan bindiga suke kai wa ƙauyukan da kuma yadda wasu makarantun ke zama a matsugunin mutanen da rashin tsaro ya raba da muhallansu. Wakilanmu sun gano aƙalla an rufe makarantu 55 a Jihar Binuwai, 52 a Jihar Katsina, 39 a Jihar Zamfara, 30 a Jihar Neja, 6 a Jihar Sakkwato da kuma 6 a Kaduna, baya ga makaratu 52 da 55 da aka rufe a jihohin Katsina da Benuwai. Wannan adadi na iya zama sama da haka, saboda ba za a iya isa ga wasu wuraren ba....
A Madagaska jiya Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar ta rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa. Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha. Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar. A ranar Talata da ta gabata ne, Randrianirina ya sanar da juyin mulkin kwace Mulki a kasar yana mai danganta hakan da rashin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, da keta hakkokin bil’adama. A kuma...
Shuwagabannin kasashen Afrika da dama sun hadu da shugaban kasar Kenya a jiya Jumma’a don yiwa tsohon firai ministan kasar kuma shugaban jam’iyyar adawa ta kasar Raila Odinga Jana’iza. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa Odinga ya mutu a wani asbiti a kasar Indiya a makon da ya gabata yana dan shekara 80 a duniya, bayan dan gajeren rashin lafiya. Raila Odinga ya tsaya takarar shugaban kasa har sau biyar amma ba tare da samun nasara ba, amma ya taimaka wajen tafiyar da harkokin siyasa wanda ya daidaita tsarin damocradiyya a kasar Ken a cikin shekaru 30 da suka gabata. Da farko an ajiye gawar Odinga na wani filin wasanni a birnin Nairobi a ranar Alhamis...
An rantsar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaban gwamnatin sojin Madagascar, bayan ya jagoranci hamɓarar da shugaba Andry Rajoelina. Sabon shugaban Madagascar kuma ya jaddada cewa hawan sa, ba juyin mulki ba ne, domin ya samu goyon bayan kotun tsarin mulkin ƙasar. Gwamnonin APC sun yi taro a Jihar Kebbi ’Yan sanda sun ƙwato miyagun ƙwayoyi a Gombe Bayan ya sha rantsuwar kama aiki Kanal Randrianirina ya ce abubuwan da zai fi bai wa fifiko sun haɗa da ruwan sha da abinci da kuma kafa gwamnati. Tsohon shugaban Ƙasar Rajoelina wanda ’yan majalisar ƙasar suka tsige bayan tserewarsa waje a ƙarshen makon jiya, ya yi Allah wadai da juyin mulki kuma yaƙi amincewa da murabus duk da baya cikin...

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana October 17, 2025 Daga Birnin Sin Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki October 17, 2025 Daga Birnin Sin Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth October 17, 2025
Abin da ya rage yanzu shi ne za a zuba ido don ganin irin sauyin da zai kawo na tsaro a birnin tarayyar, sakamakon taɓarɓarewar tsaro da ya addinin garin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 Manyan Labarai Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa October 16, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025
Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin. Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ta dace, da kuma ƙarfafa hulɗa tsakanin shugabannin addini, gargajiya da na siyasa domin dawo da zaman lafiya da daidaito a al’umma. Da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, wanda Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya wakilta, ya kira malamai da shugabanni su haɗa kai wajen...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya wallafa sako a shafinsa yana cewa ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Vladmir Putin yakan yiyuwar za su gana da juna a birnin Bhudapast na kasar Haugary, domin lalubo hanyar kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban kasar na Amurka ya kuma bayyana tattaunawar da su ka yi a jiya Ahamis da Vladmir Putin da cewa ta yi amfani matuka, kuma na sami ci gaba. Har ila yau shugaba Donald Trump ya ce; Su biyun sun amince da cewa a mako mai zuwa manyan jami’an kasarshen biyu za su gana da juna,kuma ministan harkokin wajensa Marco Rubio ne zai jagoranci tawagar Amurkan. A gefe daya a yau Juma’a ne ake sa ran yin ganawa a...
A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa. A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran. “Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman...
A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa. A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran. “Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman...
Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki. Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa. Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar noma, inda ta ce, manoma mata da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da wadanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000. Shemau ta kuma mika godiyarta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin kokarin da take yi na bunkasa noman mata a Jihar Zamfara. Sauran hukumomin da kungiyoyin da suke tare da NAWIA...
An dage ci gaba da binciken har sai ranar 20 ga wata. Maris na shekara mai zuwa, a makon da ya gabata, dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Manchester domin gudanar da jana’izar Hatton, wanda ya kasance shahararren dan wasan dambe a kasar Ingila. Dan wasan gaban Oasis Liam Gallagher, tsohon dan wasan Ingila da Manchester United Wayne Rooney da kuma tsohon zakaran ajin masu nauyi na duniya Tyson Fury na daga cikin taurarin duniya na wasanni da suka halarci jana’izar Hatton. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc October 15, 2025 Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo October 14,...
Wani binciken tattara ra’ayoyi da aka gudanar a shekarar nan ta 2025, ya nuna kaso 72.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun gamsu da manufar Sin ta bude kofa, da kasuwarta mai amincewa da kyakkyawar takara. Kana kaso 79.8 bisa dari na ganin babbar kasuwar Sin ta samar da muhimman damammaki ga kasashensu na asali. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya October 16, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona October 16, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba...
Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kafa ƙananan masana’antu a karamar hukumar Gagarawa. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon kayayyakin bunkasa tattalin arziki ga wasu daga cikin al’ummar Gagarawa. Malam Umar Namadi ya yi bayanin cewar, masana’antun za su hada da na sarrafa shinkafa da sauransu. Yana mai cewar hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa marasa aikin yi a yankin. Kazalika, Gwamnan yace gwamnatin jihar za ta ware kudi a kasafin kudin shekarar badi don gina hanyar mota daga Medu zuwa Dandidi zuwa Madaka, domin saukaka sufuri ga al’ummar yankin. Baya ga kaddamar da tallafin, Malam Umar Namadi, ya bude wasu ayyukan ci gaba ciki har da makarantar Tahfizul Qur’ani ta...
Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana. Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata Oktobar kowacce shekara domin bikin wannan rana. Shekaru 170 ke nan da fara amfani da maganin kashe radadi, inda wasu likitoci su ka yi gwajin wannan magani a asibitin birnin Massachusetts na kasar Amurka, abin da ya kawo sauyi wajen yi wa marasa Lafia aikin tiyata daga shekara 1846. Malam Aliyu Umar Yusuf na sashen bada maganin kashe radadi na asibitin gwamnatin tarayya FMC...
A Madagaska gobe Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar zata rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa. Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha. Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar. Saidai kotun tsarin mulkin kasar ta sanar da cewa, ya kamata a gudanar da zaben sabon shugaban kasa cikin kwanaki 60. Tuni Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da kasar ta Madagascar daga kungiyar bayan juyin...
A Kenya dubban al’ummar kasar ne suka hallara a babban filin jirgin saman kasar domin tarben gawar tsohon Firaministan kasar Raila Odinga. Shugaban kasar, William Ruto da tsohon shugaban kasa Uhuru Kenyatta da manyan jami’an gwamnati na daga cikin wadanda suka tarbi gawar tare da iyalan Odinga. Raila Odinga ya mutu ne a ranar Laraba a Indiya yana da shekara 80 bayan ya fadi a lokacin da yake tafiya. An dai ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin shirye-shiryen jana’izar sa, wanda za a yi ranar Lahadi a mahaifarsa ta Bondo, da ke yammacin kasar. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email*...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma nuna iko na bangare guda. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Araqchi yana cewa yana daga cikin manufofin kafa kungiyar NAMA tabbatar da yencin ko wace kasa a duniya. Don haka akwai bukatar nuna wannan a aikace. Dangane da yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran a cikin watan yunin da ya gabata, Aragchi...
Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa. Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu sukarsu a wancan lokaci. Ya jaddada cewa El-Rufai da jam’iyyar APC ba za su iya tserewa daga alhakin halin da Nijeriya ke ciki na rashin tsaro ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci mai tawali’u, mai aminci, kuma mai kishin kasa wanda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa abin a yaba ne. Shugaban ya yaba wa Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma kuma shugaban kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati bisa “kishin sa na gaskiya, rikon amana, tsarin kasafin kudi, da dokoki masu tasiri da ke magana kan makomar kasarmu.” Da yake karin haske kan tarihin Sanata Wadada a Majalisar Dokoki ta kasa, Shugaba Tinubu ya lura cewa “a cikin shekaru biyu kacal a Majalisar Dattawa, kun bambanta kanku a cikin doka, wakilci, da kuma kulawa...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba waɗanda ke kashe mutane ba gaira ba dalili. Gwamnan, ya bayyana hakan ne a yau a wajen bikin yaye sabbin jami’an tsaron cikin gida (Community Watch Corps – CWC) guda 100, a karo na uku da aka gudanar a Katsina. Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan Radda, ya karyata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yada cewa gwamnatinsa tana tattaunawa da ’yan bindigar da ke ɓoye a dazuka. A cewarsa: “Babu wata tattaunawa ko sasanci da gwamnati ke yi da ’yan ta’adda....
Jagoran ’yan adawa na kasar Kenya kuma tsohon Firaministan kasar, Raila Odinga, ya mutu yana da shekaru 80 a lokacin da yake karɓar magani a ƙasar Indiya, kamar yadda majiyoyin asibiti da ’yan sanda suka tabbatar a ranar Laraba. Rahotanni daga Asibitin Devamatha da ke Kerala, kudancin Indiya, sun ce Odinga ya samu bugun zuciya mai tsanani a lokacin da yake yawo da safe kusa da otal ɗinsa a birnin Kochi. Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe An garzaya da shi zuwa asibiti nan take, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa lokacin da suka isa. Hukumomin ’yan sanda...
Shugaban Madagascar, Andry Rajoelina, ya rusa majalisar dokoki ta ƙasar a yayin da rikicin soja ke ƙara ƙamari tare da neman hambarar da gwamnatinsa. A ranar Talata ya sanar da rushe majalisar Dokoki ta Ƙasar, a daidai lokacin da ake fama da tarzomar soja da ta tilasta masa tserewa daga ƙasar. A cewar wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na Facebook, Rajoelina ya fitar da wata doka da ke umartar rushe majalisar dokoki nan take. Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da wasu dakarun soja na musamman suka goyi bayan zanga-zangar matasa da ke neman sauya gwamnati, lamarin da ya haifar da ƙoƙarin juyin mulki. Cirar kudin kwastoma: Majalisa ta gayyaci CBN da bankuna...
Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki. Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin da ma’akatan agajin suka shafe kimanin awa hudu ba su motsa ba saboda luguden bamabaman. Kwamandan hukumar soji da ke yankin ta bayyana cewa an kona motoci hudu tare da lalata wata a cikin tawagar kayan agajin, amma ba a samu asarar rayuka ba a harin da aka kai da jirage marasa matuka da manyan bindigogin atilare a garin Bilozerka. Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga...

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya yi gargaɗin cewa dogaro da soja kaɗai, ba tare da inganta rayuwar jama’a ba, zai ƙara haifar da rikice-rikice. Ya ƙara da cewa ingantacce tsaro na ƙasa yana farawa ne idan gwamnati ta ƙirƙiro damarmakin samun aiki da kuma mayar da amincin jama’a ga gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa October 14, 2025 Manyan Labarai Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan October 14, 2025 Manyan Labarai Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026 October 13, 2025
Shugabannin kasashen Amurka, Masar,Katar da Turkiya da su ka halarci taron na “ Herm-Sheikh” a kasar Masar sun sanya hannu akan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a Gaza. A jiya Litinin ne dai aka bude taron na Kasar Masar, wanda kuma ya sami halartar Fira ministan kasar Pakistan da kuma shugaban kasar Faransa. Da yake gabaatar da jawabi, shugaban kasar Amurka Donald Trump yarjejeniyar ta zaman lafiya ta kunshi bangarori da dama, kuma tana tattare da ka’idojin aiwatar da ita. Akan gawawwakin fursunonin Isra’ilawa, shugaban kasar ta Amurka ya ce ba a kai ga warwarewa ba baki daya, domin har yanzu ana ci gaba da kokarin gano inda suke. Shi kuwa mai masaukin baki, Shugaban kasar Masar Abdulfattah al-Sisi, ya bayyana...
Hukumar da ke shirya gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) ta hukunta Kano Pillars FC da tarar Naira miliyan ₦9.5, tare da rage musu maki uku da ƙwallaye uku, bayan magoya bayansu sun kutsa cikin fili a yayin wasan da suka buga da Shooting Stars a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano. Hakan ya sa NPFL ta rufe filin wasan tare da umartar cewa Pillars za ta ci gaba da buga wasanninta na gida a filin Muhammad Dikko a Katsina. A cewar NPFL, hukuncin ya fito ne bisa dokar C1.1, wadda ke hukunta hare-haren da ake kai wa tawagar baƙi da jami’an wasa. Hukumar ta ce wannan mataki yana nufin tabbatar da tsabtace filayen wasa daga tashin hankali da rashin...
An wallafa wasu kundi 2 masu kunshe da ra’ayoyin shugaba Xi Jinping na kasar Sin kan batutuwan da suka shafi mata da yara da kungiyar mata ta kasar, da kuma ra’ayoyinsa kan karfafa zumunci da akidu da al’adun iyali, cikin harsunan Rashanci da Faransanci da Spaniyanci da Larabci, bayan irinsu da aka wallafa cikin harsunan Ingilishi. Madabba’ar tattara bayanai da fassara ta kwamitin tsakiyar JKS ce ta wallafa kundin, wadanda ake sa ran za su taimakawa masu karatu na kasa da kasa kara fahimtar ra’ayoyin shugaba Xi da dabaru da shawarwarin da Sin ta gabatar game da daukaka daidaiton jinsi da raya dukkan harkokin da suka shafi mata a fadin duniya. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin...
Sufeton ƴansanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya maye gurbin Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya, CP Ajao Adewale, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba da yake fuskanta saboda rashin gamsuwa da aikinsa tun bayan karɓar ragama daga CP Benneth Igwe. Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa sauya shi ya shafi yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a Abuja, musamman bayan harin fashi da makami da ya yi sanadin mutuwar mai gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin ɗin ARISE, Somtochukwu Maduagwu, da mai gadi Barnabas Danlami, a Katampe, ranar 29 ga Satumba, 2025. Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna NAFDAC Ta Rufe Manyan Shaguna 2 Na...
A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau? A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai...
Garin Girfa (cinnamon), Garin kaninfari Clove) Yadda za a hada: Za’a samu garin girfa kamar cokali 5 garin kaninfari cokali 7 za a hade waje daya, sai a rika diban rabin karamin cokali ana zubawa a ruwan shayi ana sha sau 2 a rana ayi kamar sati daya. Za a samu waraka da yardar Allah. Ciwon Sanyi Abubuwan bukata: Hulba, Bagaruwa, Man Habbatussauda yadda za a hada: A hada Bagaruwa da Hulba a tafasa su, sai idan ya dan huce sai a zauna a ciki, sannan kuma za a shafa man Habbatussauda a gaban, a sashi kamar yadda za’a yi matsi. In sha Allah za a samu sauki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Adon Gari Ko Kin San… Dalilin...
Shugaban kasar Amurka Donal trump da shugaban kasar Masar Abdulfatta Assisi ne zasu jagoranci bikin rattaba hannu kann yarjeniyar Sulhu wacce ta kawo karshen yaki da kuma kissan kiyashin da HKI ta yi a Gaza na tsawon shekaru 2, daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa ranar Alhamis 8 ga watan Octoban shekara ta 2025. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews ya bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gutteres da shuwagabanin kungiyoyin kasashen Larabawa da Turai zasu halittu taron na gobe litinin a sharam Sheikh na kasar Masar. Labarin ya kara da cewa za’a gudanar da taron ne a gobe litinin, bayan azahar kuma ana saran shuwagabannin kasashe fiye da 20. Firai ministan kasar Burtaniya Keir Starmer,...
“Abin takaici ne ace Nijeriya tana karancin Mlaman makaranta da suka kai 194,876 a makarantun gwamnati a fadin tarayyar Nijeriya. Halin da makarantunmu na Sakandare suke ciki shi ma lamarin bata canza zane ba. Rashin isassun Malamai shi ma lamarin abin damuwa ne domin kuwa sannu a hankali hakan zai iya shafi samar da ingantaccen ilimi a makarantunmu kamar yadda sakamakon hakan ba zai haifar da da mai ido ba cewar, Amba”. Don haka ya ja kunnen Nijeriya cewa rashin isassun Malaman zai iya kawo cikas wajen kokarin da Nijeriya ta ke yi na cimma muradin ci gaba na 4 (SDG 4) da ya kunshi ingantaccen ilimi ba tare da wani bambanci ba, tsakanin gwamnatoci uku ba tare...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025 Labarai Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas October 2, 2025
Duk da Najeriya na cikin yanayin damina, wanda ake ganin a lokacin ta fi samar da wutar lantarki ga ’yan ƙasarta, amma jama’a a jihohin Kaduna da Kano na ci gaba da kokawa kan ƙarancin wutar. A duk shekara jama’a na more wutar lantarki a Nijeriya a lokacin damina saboda tashoshin ruwa na samar da wutar lantarki suna aiki da cikakken ƙarfinsu. Amma, wasu masana a ɓangaren wutar sun shaida wa wakilinmu cewa duk da matsalolin masu nasaba da lalata kayan aiki da kuma ƙin biyan kuɗin wuta da wasu masu amfani da ita ke yi, kamfanonin rarraba wutar (DisCos) suna yin iya bakin ƙoƙarinsu wajen cike giɓin. Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa ana ƙoƙarin daidaita rarraba wuta...
Jiragen saman yaki sun yi luguden wuta kan birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan, kuma rahotanni masu karo da juna suna cewa an kashe shugaban Taliban na Pakistan Kafofin yada labaran Afghanistan sun yi ikirarin cewa: Sojojin Pakistan ne ke da alhakin harin da aka kai a Kabul babban birnin kasar Afganistan a yammacin ranar Alhamis. Tashar Talabijin ta Tolo News da Khabar Online Afganistan sun ruwaito cewa: Sojojin Pakistan sun dauki alhakin hare-haren da aka kai cikin daren jiya a Kabul. Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya rubuta a dandalin X a yammacin ranar Alhamis cewa: An ji karar fashewar wani abu a birnin Kabul. Ya kara da cewa: “Babu wata damuwa, lamarin dai kamar yadda aka saba, ana ci...
Majalisar dokokin tarayyar Turai ta amince wa kasashen nahiyar su kakkabo jiragen yakin kasar Rasha wadanda suke keta sararin samaniyar wasu daga cikin kasashen Nahiyar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan da ta sami rahotanni daga wasu daga cikin kasashen gabacin turai kan cewa jiragen yakin kasar Rasha samfurin Mig 31 da Su 25 keta sararin samaniyar kasashensu. Firay ministan kasar Poland Donal Tusk ya ce kasarsa a shirye take ta kakkabo duk wani abu da ya shiga sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba. A taron majalisar don tattauna wannan batun dai wakilai 469 sun amince da bukatar a yayinda wasu 97 suka ki amincewa, sai kuma...
Tawagar da ke karkashin jagorancin, Barry Andrews ta kuma ziyarci hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), inda shugabanta, Mahmood Yakubu, ya yi gargadin cewa jinkirin da ‘yan majalisa ke yi wajen gyaran dokar zabe ta 2022 na iya kawo cikas ga shirye-shiryen gudanar da zabe a 2027. Wakilan, wadanda suke Nijeriya tun kusan makonni uku domin nazarin matakin aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahotonsu na bayan zaben 2023, sun kuma yi tattauna da babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Abbas, a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaransa, Leke Bayeiwu, ya shaida wa tawagar EU cewa rahotanninta kan zabukan shekarar 2023 ana la’akari da su a cikin sauye-sauyen gyara dokar zabe da na dimokuradiyya da...
Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Gaza Mohammad Al-Moughayyir, ya ce sojojin Isra’ila sun janye daga yankuna da dama a cikin birnin Gaza da arewacin zirin da kuma wasu yankunan kudancin yankin. A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, Motocin Isra’ila sun janye daga kudancin birnin da tsakiyar birnin zuwa yankunan gabashi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza October 9, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar October 9, 2025 Daga Birnin Sin Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar October 9, 2025
A bana, bikin Tsakiyar Kaka da Ranar Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin sun hadu, inda suka haifar da hutun tsawon kwanaki takwas. An yi hasashen cewa, adadin mutanen da suka yi tafiya a yankuna daban daban na kasar zai kai biliyan 2.432, tare da karuwar kashi 6.2% a kowace rana idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Adadin ribar da aka samu a manyan kantuna da gidajen abinci a cikin kwanaki hudu na farkon hutun ta karu da kashi 3.3% idan aka kwatanta da na bara, kuma har zuwa karfe 4:00 na yammacin ranar 8 ga watan, kudin shiga da aka samu daga kallon fina-finai yayin wannan biki ya wuce RMB Yuan biliyan 1.8 kwatankwacin fiye da dala miliyan 252....
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar iran Mohammad Eslami da manyan jami’a daga hukumar rasatom ta hadin guiwar ayyukan makamashin nukiliya sun gana a birnin Tehran kuma sun tattauna kan yadda za su yi aiki tare a bangaren shirin ta na nukiliya na zaman lafiya, Nikolai Spassky ya kawo ziyara iran ne a birnin Tehran tun bayan ziyarar da Eslami ya kai birnin mosko a ranar 24 ga watan satumba, inda bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, na yin aiki tare wajen gina karamar tashar nukiliya iran. Haka zalika bangarorin biyu sun tattauna kan yarjejeniyar da aka kula lokacin da Eslami ya kai ziyara da ya hada da yin aiki tare a cibiyar nukiliyar iran...
Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kafa tsarin ‘yansandan jihohi a kasar nan domin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.Abbas ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin dokar hukumar leken asiri da binciken sirri ta shekarar 2024, wanda kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja ranar Laraba.Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta Yamma/Asa, Honarabul Muktar Shagaya, ya ce, kawo sauye-sauye a fannin tsaro ya zama abinda aka fi mayar da hankali, kuma yanzu dole a tashi daga rubutu kawai zuwa aiwatar da cikakken tsari.Shugaban majalisar ya ce kafa ‘yansandan jihohi ta...

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025Daga Birnin SinKasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata October 7, 2025
Kasashen Iran, Rasha, Azerbaijan, da kuma Kazakistan sun rattaba hannu kan yarjeniyar samar da tsaro a ruwayen tekun Caspian wadanda suke tarayya a mallakarsu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kwamandojin sojojin ruwa na wadannan kasashe sun rattaba hannu a kan yarjeniyar a yau Laraba a birnin St. Petersburg na kasar Rasha. Kuma sun kara jaddada cewa ba zasu taba amincewa wata kasa a duniya ta shiga yankin da sunan tsaro ruwan tekun ba. Rear Admiral Shahram Irani, babban kwamandan sojojin ruwa na JMI ne ya wakilci JMI a bikin rattabawa yarjeniyar hannu. Ya kuma bayyanawa kafafen ya da labarai kan cewa manufar yarjeniyar ita ce takaita tsaron ruwan tekun Caspian a tsakanin kasashen da suke...
Alkaluman da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin wato China Railway ya gabatar, sun nuna cewa, ana sa ran jigilar fasinjoji kimanin miliyan 21 da dubu 750, ta jiragen kasa a kasar Sin a yau Laraba. Kana tun daga ranar 29 ga watan Satumban da ya gabata, wato ranar da aka kaddamar da aikin jigilar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye, a lokacin hutun bikin tunawa da kafuwar kasa da na Zhong-Qiu, zuwa jiya Talata, an riga an kwashe fasinjoji fiye da miliyan 160 ta jiragen kasa a kasar Sin.Yau ce ranar karshe a hutun na wannan karo, don haka ake sa ran ganin karuwar zirga-zirgar mutane da suke kokarin komawa gidajensu daga wuraren da suka yi bulaguro. Hakan ne...
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa. Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu...
Takardar mai kwanan watan Oktoba 6, ta samu sa hannun Prince Peters Adeyemi, babban sakataren NASU, da Comrade Mohammed Ibrahim, shugaban SSANU na kasa.ShareTweetSendShareMASU ALAKA LabaraiƁatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci October 7, 2025LabaraiTinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk October 7, 2025Ra'ayi RigaCikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka October 7, 2025
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) mai barin gado ya mika ragamar shugabancin hukumar a hukumance ga Misis May Agbamuche-Mbu, wacce za ta zama shugabar riko.Taron ya gudana ne a ranar Talata yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kwamishinonin zabe a hedikwatar INEC da ke Abuja.Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta ArewaMajalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A NijeriyaAgbamuche-Mbu, wacce itace kwamishina mafi dadewa a hukumar zabe ta kasa INEC, za ta ci gaba da kula da harkokin hukumar zabe har sai an nada sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta.Da yake sanar da ajiye aikin, Farfesa...

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
A cewarsa, gyaran yana taimakawa wajen samun bayanai daidai domin tsara ci gaba da kuma rarraba albarkatun ƙasa bisa adalci daga gwamnatin tarayya.“Wannan tsarin yana daidai da yadda ake yi a wasu jihohi, inda ake amfani da bayanan masarautu, yankuna da ƙauyuka wajen tsara ci gaba da rarraba kuɗaɗe,” in ji shi.Gwamnan ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɗa kan jama’a da tallafa wa ayyukan ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sabon tsarin cikin gaskiya.Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu da yadda suka gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.Tun da farko, shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi buƙatu 196, wanda 17 don kafa sabbin masarautu, 166 don sabbin yankuna, da...

Wani Mai Rajin Kare Hakkin Dan Adam A Spaniya Yayi Tir Da Isra’ila, Ya Bukaci A Dauki Mataki Kanta .
Tsohon magajin garin Bacelona Ada collaou da sauran masu rajin kare hakkin dan adam yan kasar spaniya dake cikin jiragen ruwan agaji na Sumud Flotilla da Isra’ila ta kama a baya bayan nan, sun yi tir da irin azabartar da su da isra’ila ta yi kuma sun sha alwashin daukar matakin shari’a a kanta, Shi ma shugaban bangaren hagu na jam’iyar podemos ya sanar da shirye shiryen maka prime minister Isra’ila Benjamen na tanyaho a gaban kuliya manta sabo, Matakin shariya da kungiyoyinn farar hula da sauran jam’iyun siyasa a kasar Spaina ta dauka yana kara nuna yadda duniya ke yin matsin lamba kan gwamnatin yahudawan sahyuniya, kuma zai sanya bangaren sharia na kasar spain ya gudanar da bincike na...
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni da a sake duba farashin kuɗin aikin Hajjin 2026, domin rage nauyin da zai rataya kan alhazai, sakamakon yadda Naira ke kara karfafa kan Dalar Amurka a kasuwa. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya mika umarnin Shugaban kasan ga Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), inda ya ce a cikin kwanaki biyu hukumar ta fitar da sabon tsarin farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin Kasar a yanzu. Da yake jawabi a fadar shugaban kasa bayan taro da shugabannin NAHCON, Shettima ya ce ya zama dole a samu hadin kai tsakanin gwamnoni da jami’an hukumar alhazai domin tabbatar da tsarin farashi mai sauki da adalci ga maniyyata. Shi ma Sakataren...
Tun bayan harin 7 ga watan Oktoba, 2023, da mayaƙan Hamas suka kai wa Isra’ila wanda ya hallaka sojoji sama da 60 , Isra’ila ta fara luguden wuta a Gaza.Tun daga wannan lokacin, yankin ya zama wurin tashin hankali da yunwa, inda mutane da dama ke mutuwa a kowace rana.Tags: FalasɗinawaGazaHamasIsra'ilayaƙiShareTweetSendShare Sadiq Related Kasashen KetareMe Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa? 3 days agoKasashen KetareWadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa? 1 week agoKasashen KetareBirtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa 2 weeks ago
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu. Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin. Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana. Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na...
Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa. Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph na National Accord da kuri’u 9 a matsayin shugaban kungiyar. Ya kuma bayyana cewa Mista Chris Nyamtu na gidan rediyon Najeriya ne ya yi nasara da kuri’u 21 yayin da Augustine Kuza na jaridar Pilot na Najeriya ya samu kuri’u 9 a matsayin Sakatare. Mista Abel Daniel na jaridar Guardian a matsayin mataimakin shugaba Awayi Kuje na NAN a matsayin Mataimakin Sakatare, Michael...
Wani saksmkon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar dimokuradiyya ta Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Isra’ilawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin Gaza, tare da bayyana hadarin da fursunoni ke fuskanta. Wannan adadi na kashi 66% ya karu da kashi 13% a kan sakamakon da aka fitar a shekara guda da ta gabata lokacin da aka yi musu tambaya iri ɗaya. Sakamakon ya kuma nuna cewa kashi 45% na Isra’ilawa sun yi imanin cewa ya kamata Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yi murabus nan da nan kafin karshen yakin, tare da dora masa alhakin abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Sakamakon ya nuna...
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya “WFP” ta bayyana cewa: Rage agajin jin kai na barazana ga miliyoyin mutane da suke fama da yunwa a Somaliya Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta yi gargadin cewa: Miliyoyin mutane a Somaliya na cikin hadarin fuskantar yunwa da rashin abinci mai gina jiki, saboda tsananin karancin kudade da ya tilastawa kungiyar ta WFP rage yawan mutanen da take tallafawa da taimakon abinci na ceton rai da sama da kashi biyu bisa uku. A watan Nuwamba, za a tilastawa Hukumar WFP ta rage adadin mutanen da ke samarwa tallafin abinci na gaggawa zuwa 350,000 kawai, wanda ya ragu da miliyan 1.1 a watan Agustan da ya gabata. Wannan...
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar da wani sabon rahoto kan cikar shekaru biyu da fara kaddamar da munanan hare-haren Isra’ila a kan al’ummar zirin, inda rahoton ya bayyana cewa har yanzu ayyukan kisan kare dangi na ci gaba da gudana a kan mutanen Gaza. A cewar sanarwar da aka fitar a wannan Lahadi, Isra’ila ta jefa tan 200,000 na bama-bamai a kan al’ummar Gaza, snnan kuma sama da mutane 76,600 ne aka kashe ko kuma suka bata ba a san makomarsu ba tun lokacin da aka fara yakin a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. A cikin shekaru biyu, an tabbatar da kashe mutane 67,139, yayin da kusan mutane 9,500 kuma ba a san makomarsu ba, amma...

Yawan Mutanen Da Suka Yi Zirga-zirga A Rabin Farkon Hutun Bikin Kafuwar PRC Da Bikin Zhongqiu Ya Kai Biliyan 1 Da Miliyan 243
Bisa labarin da ma’aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin ta bayar, a ranar 4 ga wannan wata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a kasar Sin ya kai miliyan 301 da dubu 291 da dari 1, wanda ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a rabin farko na hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin PRC da bikin Zhongqiu ya kai matsayin koli a tarihi, wato ya kai biliyan 1 da miliyan 243, wannan ya shaida cewa, an fi yin zirga-zirga a lokacin hutun. Game da hanyoyin zirga-zirga a lokacin wannan hutu, an fi zabar hanyoyin mota. Game da yankunan da aka fi sha’awar ziyarta, an...
A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a yau Lahadi da samun galabar Iran. Tun da fari kungiyar kwallon ragar ta Iran ta sami nasarori har sau uku a jere, da a karshe ta kai ga samun nasara akan mai masaukin baki kasar Uzbakestan. Mai bayar da horo ga ‘yan wasan Li Du Hi, ta bayyana jin dadinsa da nasarar da su ka samu, musamman saboda wannan ne karon farko aka sami wannan...
Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi. Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan yahudawan kudin da sun kai Shakel miliyan 25 wanda shi ne kwatankwacin Dala miliyan 7.54, ta hannun lauyoyinsu. Haka nan kuma jaridar ta ce hukumar dake kula da haraji da ke karkahsin ma’aikatar shari’a ce ta aiwatar da raba kudin a matsayin abinda su ka kira diyyar ayyukan t’addanci.! Jaridar ta kuma ce tun a 2019 ne wadannan ‘yan sahayonioyar su ka bukaci a biya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta ƙara da cewa: “A cikin baƙin ciki muke alhinin rasuwar Ambasada Muhammad Jabbi Maradun, fitaccen dattijon jiha kuma ɗan jiharmu ta Zamfara na gaskiya. “An haifi Jakada Jabbi ne a ranar 12 ga Nuwamba a shakrar 1943, a Ƙaramar Hukumar Maradun. “Ambasada Maradun ya taba zama jakadan Nijeriya a ƙasar Tunisia daga 1999 zuwa 2003. “Ya yi fice a yunƙurin samar da jihar Zamfara. “Bayan kafuwar jihar Zamfara, Ambasada Jabbi ya shiga gwamnatin soja ta farko a ƙarƙashin Kanar Jibril Bala Yakubu, inda ya riƙe muƙamin kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido. “Ayyukan sa na siyasa sun haɗa da jam’iyyun GNPP, NPN, da NRC, kuma ya kasance mai ruwa da tsaki a...
Mahaifiyar Yilwatda ta rasu a watan Agustan 2025, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, tana da shekaru 83. Da yake mayar da martani, Atiku ya ce shugaban kasar ya zaɓi ya yi ziyarar jana’izar siyasa maimakon ziyarar jama’ar da taɓarɓarewa tsaro ta shafa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka, a jiya jumm’a a hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida a nan Iran. Ya kumakara da cewa a lokacinda aka fara yakin shugaban kungiyar ta Hamas yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Iraki, yana dawowa ne ya ji labarin fara shi. Janar Qa’ani ya kara da cewa, amma duk da haka, shahida Nasarallah ya zauna...
A ranar 3 ga watan ne hukumar ciniki ta duniya (WTO) ta gudanar da taron shekara-shekara na majalisar kula da harkokin cinikayya karo na uku a birnin Geneva na kasar Switzerland. Kasar Sin ta yi amfani da wannan dama domin daidaita wannan batu, inda ta fallasa tare da sukar matakin “harajin ramuwa” na Amurka daga bangare guda da gitta kariyar cinikayya, inda ta yi nuni da cewa, matakan kakaba harajin da Amurka ta dauka sun haifar da illa ga harkokin cinikayyar duniya, kana ta bukaci Amurka ta mutunta ka’idojin WTO, tare da yin aiki da dukkan bangarori don karfafa gudanar da harkokin kasuwancin duniya cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba. Membobi irinsu Indiya, Brazil, Masar da Pakistan sun...
Turkiyya ta mayar da martani ga shugaban Amurka cewa: Ba za ta daina sayen iskar gas daga kasar Rasha ba Ministan makamashi da albarkatun kasa na kasar Turkiyya Alparslan Bayraktar ya tabbatar a wata hira da yayi da gidan talabijin a jiya alhamis cewa: Kasarsa ba ta da niyyar yin watsi da sayen iskar gas da take daga Rasha. “Ministan a wata zantawa da tashar CNN Turk ya bayyana cewa: Game da Turkiyya ba za ta iya ce wa ‘yan kasarta ku yi hakuri, iskar gas ta kare ba. Ya kara da cewa: “An tabbatar da tsaron iskar gas tana tabbata ne ta hanyar yin amfani tilas da wadannan hanyoyin, ba tare da nuna bambanci ba a lokacin hunturu mai...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa. Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta gudanar, ya hada shaguna 300 da wutar lantarki daga na’urorin hasken rana da aka sanya a cikin kasuwar, inda kowane shago kuma an saka masa fanka amfani da hasken rana kyauta. Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da kasuwar a hukumance, Malam Umar Namadi ya ce shirin zai saukaka harkokin kasuwanci, da rage kashe kudi, da kuma bunkasa ribar ‘yan kasuwa. ...
Shugaban Madagaska Andry Rajoelina ya bayyana cewa gagarumar zanga-zangar da akeyi a kasar, na da nufin “yi masa juyin mulki,” ne. A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mista Rajaolina, ya yi ikirarin cewa matasan da suka yi gangami a kan tituna, da tun farko suke yin Allah-wadai da katsewar wutar lantarki da ruwan sha, wasu ’yan siyasa ne ke amfani da su. A jawabi na tsawon mintuna ashirin da aka watsa kai tsaye a shafinsa na Facebook, wanda shi ne na farko tun soma fara zanga-zangar, Shugaban kasar ta Madagaska ya tabbatar da cewa matasan da ake wa lakabi da ‘’G Z’’, ‘yan adawa” ne ke amfani da su wajen neman kawar da shi daga mulki....
Firai ministan kasar Beljium Bart De Wever ya fadawa sauran tokororinsa na kasashen turai kan cewa bai amince a yi amfani da kudaden Rasha da aka kwace a kasashen turai don yakar kasar a Ukraine ba, sai tare da wasu sharudda. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Wever ya na fadar haka, ya kuma kara da cewa dokokin kasa da kasa sun hana a kwace kudaden wata kasa mai cikekken yenci, don wata bukata. Kafin haka dai kasashen turai da dama sun gabatar da shawarar kwace dalar Amurka bil;iyon $229 na kudaden ruwan da kadarorin kasar Rasha da ke turai suka samar don yakarta a kasar Ukraine, wannan duk da cewa dokokin kasa da kasa sun haramta...
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan. A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu. Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, sannan kuma ya baiwa al’umma tabbacin dawo da zaman lafiya cikin kankanin lokaci. Sanarwar ta kuma aike da sakon ta’aziyya da jaje ga daukacin al’ummomin da aka samu cikin wannan rikici — daga Ifelodun zuwa Irepodun, Isin, Ekiti, Edu, da Patigi. A cewarsa ana tanadin komai don rage illar hare-haren da kuma tabbatar da kawo...
Ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta fadi cewa akalla sama da falasdinawa 66225 ne suka rasa rayukansu, yayin da 168938 kuma suka jikkata a aci gaba da kiran kare dangi da HKI ke yi a yankin gaza tun daga watan oktoban shekarar bara da ta gabata. Akalla fararen hula 77 ne ake kaashewa 222 kuma suke jikkata a duk rana sakamakon hare hare da sojojin Isra’ila ke kawai kan fararen hula marasa karia a yankin Gaza. Fararen hula da dama ne ciki har da mata da yara kanana suka dimauce bayan da HKI ta harba hayaki mai sa hawaye da kuma bomb na hayaki da jirgi mara matuki na HKI ya kai a makarantu da gidaje domin tarwatsa alumma dake...
A yau Alhamis, kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, layin dogo na kasar Sin ya gudanar da balaguron fasinjoji miliyan 23.13 a jiya Laraba, wato ranar farko ta hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na tsawon kwanaki 8. A cewar kamfanin sufurin jiragen kasan, wannan adadi ya nuna wani sabon tarihi na yawan balaguro da aka samu a rana daya. Kamfanin sufurin jiragen kasan ya yi kiyasin cewa, za a yi tafiye-tafiye miliyan 19.3 a ranar Alhamis, tare da karin jiragen kasa 1,409 da aka samar. Yayin da bikin tsakiyar kaka ya fado lokaci guda tare da ranar kafuwar PRC a wannan shekarar, ana sa ran hutun da ake...
Gwamnatin Rasha ta jaddada cewa: Yarjejeniyar dabarun da kulla da Iran dole ne a aiwatar da ita Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar a yau Alhamis a cikin wata sanarwa cewa: Yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Rasha da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara aiki, tare da tabbatar da cewa kasashen biyu bisa tsarin yarjejeniyar suna fuskantar kalubale da barazana amma ba zasu yi wani tasiri ba. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar ta bayyana cewa: A ranar 2 ga watan Oktoba ne yarjajjeniyar huldar hadin gwiwa tsakanin Rasha da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadda shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Iran Masoud Peskov suka sanya wa hannu a ranar 17 ga watan Janairun shekara...
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta sanar da cewa; A kowace rana Falasdinawa guda 100 ne suke yi shahada saboda zaluncin sojojin mamayar Isra’ila Babban kwamishinan hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya bayyana cewa: A kowace rana sojojin mamayar Isra’ila suna kashe kimanin Falasdinawa 100 a zirin Gaza. Lazzarini ya ce ta hanyar dandalin X, “A takaice ana kashe mutane 100 a kowace rana a Gaza, sakamakon farmakin da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa ko kuma harbe-harbe a wuraren rarraba abinci da gidauniyar agaji ta Gaza ke gudanarwa.” Ya ci gaba da cewa, “A lokaci guda kuma, wasu na mutuwa saboda yunwa ko kuma rashin kula da lafiya”. Lazzarini ya kara da cewa...
Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu. Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi a jihar Edo. Gwamna Ahmed Usman Ododo ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da su haɗa kai da ƙananan hukumomin yankin, wajen bayar da tallafi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa. Gwamna Ododo ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin...
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai. Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa. Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta yi gargadi ga likitoci a babban asibitin garin Gusau, bayan da suka gano rashin zuwan su a wata ziyarar ba-zata. Dakta Maradun, wadda ta kai ziyarar bazata asibitin, ta ce ta firgita da ganin cewa babu wani likita da ke bakin aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abu da ke faruwa a baya. Ta yi Allah wadai da lamarin a matsayin...
Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya ce maido da tsarin takunkuman karya tattalin arziki a kan Iran da wasu kasashen yammacin duniya suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya. Nebenzya ya bayyana hakan ne a wata doguwar wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban rikon kwarya na kwamitin sulhun bayan da kasashe 15 suka kada kuri’ar sake kakaba takunkumi kan Tehran, wanda aka soke a karkashin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2015 tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, ciki har da Birtaniya, Faransa, da Jamus. Wakilin na Rasha ya jaddada cewa, an bullo da abin da ake kira tsarin dawo da takunkumai a...
Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba. Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram...
A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba. An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken...
Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane. Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya. Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli...
Rima hassan wani bafranshe mai nuna goyon bayan falasdinu kuma mamba a majalisar tarayyar turai kuma daya daga cikin tawagar Sumud flotilla ya sanar ta kafar sada zumunta cewa gobe ne ake saran tawagar flotilla za ta isa yankin Gaza duk da yake cewa Isra’ila ta tanadi tsauraran matakai na tunkararta. A daren jiya ma isra’ila takai kai hari kan tawagar ta Flotilla , wannan ya zo ne bayan da matukan jiragen ruwa guda biyu suka fitar da bayani cewa Isra’ila ta kai harin kan jiragen ruwansu guda biyu, inda avila yace sojojin Isra’ila sun yi amfani da yakin kwakwalwa ga wasu daga cikin tawagar flotilla inda suka yi musu kawanya Agefe daya mataimakin ministan harkokin wajen kasar Austreliya ya...
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, don haka na aike da jiragen ruwa masu makaman Nukiliya da shi ne makamai mafi hatsari.” Shugaban kasar na Amurka ya riya cewa kasarsa tana gaba da kasashen Rasha da China da ci gaban shekau 25 a fagagen kimiyya dakuma kera jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my...
Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar. A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa. Ya fara jawabinsane da jajanta wa wadanda suka rasa yan uwa da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Da yake jawabi ga matasan da suka fusata, ya bayyana cewa: “Na saurari muryoyinku, da bukatunku, Kuma ina ba da hakuri idan akwai mambobin gwamnati da ba su yi aikin da mutane suke tsammani […].” Shugaban ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa, “A bisa...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai. Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”. Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna kishin ƙasa da hadin kai da juriya, waɗanda ya ce su ne ke taimaka wa ƙasar wajen dunƙulewa tun lokacin samun ƴancin kai a 1960. A ranar 1 ga watan Otoban 1960 ne dai Najeriya ta samun ƴancin kai daga Turawan mulkin Birtaniya da suka yi mata mulkin mallaka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki. Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar Rigasa da ke Kaduna da misalin 12.42 na rana. Daga Kaduna kuma jirgi zai baro Rigasa da misalin ƙarfe 2.30 na rana ya isa Kubwa da ƙarfe 8.40 na yamma. Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani za a ware kowace ranar Laraba domin aikin kula da lafiyar jiragen da ke aiki a layin na Abuja zuwa Kaduna. Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba...
A wani taron da jakadun kasashen Fransa, Jamus da Ingila su ka yi, sun yi wa Rasha gargadin cewa, za su rika kai wa jiragenta na yaki hari, idan su ka keta hurumin samaniyar daya daga cikin kasashen mambobi na Nato. Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” ya watsa wani rahoto da a ciki ya bayyana cewa; Manyan jami’an diplomasiyyar kasashen uku na turai sun yi wani taron sirri a birnin Moscow, inda su ka gargadi Rasha akan keta hurumin samaniyar kasashen mambobi,suna masu cewa za su iya kai wa jiragen Rashan hari. Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” din ya ambato jami’an kasashen na turai da su ka halarci taron suna nakalto wannan gargadin, bisa cewa cikin ganganci ne jiragen na Rasha su...
Kwanaki kadan bayan da aka gudanar da zaben raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar, mahkuntan sojan kasar sun ayyana ranar yin zaben shugaban kasa da zai zama na farko a cikin shekaru 4 na mulkin soja. Sanarwar tsayar da ranar yin zaben shugaban kasar dai, an yi ta ne ta hanyar dokar soja a ranar Asabar din da ta gabata. Sakamakon kuri’ar raba gardamar da ak ayi a ranar 21 ga watan nan na Satumba, ta nuna cewa kaso 89% na wadanda su ka kada kuri’ar, sun nuna amincewa da sabon tsarin mulkin. Har ila yau, wata kididdiga ta nuna cea kaso 86% na wadanda su ka cancanci yin zabe ne su ka kada kuri’a. Jam’iyyun hamayyar kasar ta...