Leadership News Hausa:
2025-12-10@05:34:17 GMT

Hukumar NASENI

Published: 25th, October 2025 GMT

Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa.

Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi.

NASENI tana ba da ababen more rayuwa da tallafin manufofin, yayin da ɓangaren da ke kula da masana’antu, yana mai da hankali kan haɗin gwiwa, ƙirƙira da kasuwanci don kafa Nijeriya a matsayin cibiyar fasahar Afirka.

Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya ba a cikin juyin juya halin masana’antu da ke faruwa a duniya a halijn yanzu.

NASENI na zuba jari mai yawa wajen bincike a ɓangaren ayyukan da ake yi na yanayi mai dorewa a Nijeriya domin bunkasa tattalin arzikin ƙasa kamar yadda yake a tsare staren tattalin arziƙin shugaba Bola Ahamed Tinubu.

Hukumar NASENI ta haɗa kai da gwamnatin Jamhuriyar Czech domin raba jimillar dala miliyan 21.7 ga zababbun mutane 11 da za su ci gajiyar ayyukan Delta-2 don fara aiwatar musayar fasahohin zamani zuwa Nijeriya. Shirin Delta-2 shi ne samfurin haɗin gwiwar Hukumar Fasaha ta Jamhuriyar Czech (TA CR) ta hanyar da TA CR ke tallafa wa aiwatar da bincike da haɓaka masana’antu da cibiyoyi masu ƙima. An ƙaddamar da shi ne a cikin shekarar 2021, shirin Delta-2 yana ba da kuɗi kuma yana ba da damar bincike da haɓaka ayyukan ƙirƙire- ƙieƙire a fannoni uku da aka mayar da hankali: aikin gona, ma’adinai, da masana’antu gaba ɗaya.

Samar da famfon ban ruwa mai amfani da hasken rana na NASENI ya kawo sauyi ga harkar noma ta hanyar inganta noman rani. Yanzu haka manoman Nijeriya suna amfana ta hanyoyi daban-daban daga wannan fanfo mai sauƙin gaske wanda ke samar da ingantaccen ruwa na amfanin gona. Manoma za su iya amfani da famfon ban ruwa mai amfani da hasken rana don samar da amfanin gona akai-akai, wanda hakan zai bunƙasa yawan amfanin gona da kuma girbi da yawa a kowace shekara.

Yana sa manoma su rage dogaro da yanayin ruwan sama maras tabbas, don haka yana rage haɗarin gazawar amfanin gona. Yana kawar da dogaro da man dizal ko man fetur don ban ruwa tare da rage hayakin iskar gas da gurɓataccen muhalli. Hakanan za a iya amfani da shi a wuraren da basa tare da babbar hanyar wutaingantaccen hanyar grid ba. Ta hanyar amfani da famfunan ban ruwa mai amfani da hasken rana na NASENI, manoma suna ƙara haɓaka aikin noma sosai, da rage tsadar aiki, da samun ƙarin kuɗin shiga da inganta rayuwa idan aka kwatanta da famfunan ban ruwa masu amfani da man fetur.

Domin wannan ci gaba mai ɗorewa na ci gaban masana’antun Nijeriya da kuma tsara makomar al’ummar ta hanyar dogaro da kai, NASENI ce Gwarzon Kamfanin LEADERSHIP na shekarar 2025.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Daɓid Adeyemi October 25, 2025 Kiwon Lafiya Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu October 25, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia

Sojojin kasar Thailand sun sanar a yau Litinin cewa, son kai wani sabon hari akan iyakar da take da sabani da makawabciyarta Cambodia.

Wannan sanarwar ta sojojin Thailand ya biyo bayan da kasashen biyu suka rika zargin juna da cewa sun keta dakatar da wutar yaki, da shugaban Amurka Donald Trump ya shiga tsakani.

Sojojin Thailand sun ce; sabon fadan da ya barke ya yi sanadiyyar mutuwar sojan kasar daya, yayinda wasu 4 su ka jikkata. Haka nan kuma sojojin na Thailand sun zargi takwarorinsu na Cambodiya da fara tsokana ta hanyar bude musu wuta.

A halin yanzu sojojin na Thailand sun fara amfani da jiragen sama na yaki wajen kai hare-hare.

Tun a ranar 5 ga watan Yuli ne dai fada ya barke a tsakanin kasashen biyu saboda sabanin kan iyaka. Wancan fadan dai ya yi sanadiyyar kashe mutane 48 da kuma tilasta wa mutane fiye da 300,000 yin hijira.

Kasashen biyu dai suna da sabani ne akan iyakarsu ta kasa da tsawonta ya kai kilo mita 817,wacce aka Shata tun wajen 1907 a lokacin da Faransa ta yi wa Cambodia Mulkin mallaka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025  Macron Na Faransa Ya Yi Wa Najeriya Alkawalin Taimakawa Akan Matsalolin Tsaro December 8, 2025 Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka  Teke Fuskanta December 8, 2025 Majid Majidi Na Iran Ya Sami Kyauyar Girmamawa Daga Cibiyar Fina-finai Na “Eurasia Dake Kasar Rasha December 8, 2025 Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa December 7, 2025 Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi) December 7, 2025 Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’ December 7, 2025 Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila December 7, 2025 Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yaba Ma Iyaye Bisa Goyon Bayansu ga Shirin Rigakafin Shan Inna a Karamar Hukumar Ringim
  • Za a Yi wa Yara 194,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Karamar Hukumar Birnin Kudu
  • Iran da Saudiyya sun sake jaddada fadada dangantakarsu
  • Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon
  • An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba
  • Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia
  • Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa
  • Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano
  • Venezuela: Ba Mu Tsoron Kaudin Amurka Na Wuce Gona Da Iri