Shugaba Tinubu Ya Jaddada Kudurin Gwamnatinsa Na Ƙara Zuba Jari A Ilimi
Published: 24th, October 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ƙara zuba jari a manyan cibiyoyin ilimi domin shirya ɗalibai su zama masu iya fafatawa a matakin duniya.
Shugaban Ƙasan ya bayyana hakan ne a yayin bikin karrama masu kammala karatu na shekara ta 40 na Jami’ar Ilorin (UNILORIN) da ke Ilorin, Jihar Kwara.
A jawabinsa, wanda Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya Akure (FUTA), Farfesa Temidayo Oladiji, ya karanta a madadinsa, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin ƙarfafa ƙirƙira, bincike, da ilimin da ke gina ƙwarewa (skill-based education) a dukkan jami’o’in Najeriya.
Ya yaba wa jami’ar bisa tsayin daka da ladabi da kuma ingancin ilimi da ta dade tana nunawa tun daga kafuwarta.
Shugaban Ƙasan ya kuma sanar da cewa Jami’ar Ilorin ta kasance ɗaya daga cikin jami’o’in da aka zaɓa domin zama hedikwatar “Digital Innovation Hub” na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) — wani shiri da aka ƙaddamar domin bunƙasa ƙwarewar fasaha, ƙirƙira, da haɓaka bincike a jami’o’i.
A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar Ilorin, Farfesa Wahab Egbewole, ya shawarci waɗanda suka kammala karatu da su ci gaba da riƙe dabi’un jami’ar na ladabi, aiki tukuru, da gaskiya, domin su zama abin koyi a inda suka samu kansu a gaba.
Ali Muhammad Rabiu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara ilimi
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamishinan Ilimi Na Kano Ya Yi Kira Da A Karfafa Shugabancin Makarantu Domin Inganta Karatun Dalibai
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen taron horaswa na kwanaki biyu mai taken “Leading Learning for Gender Equality in Education” wanda British Council ta shirya domin wakilai daga jihohin Kano, Kaduna, Plateau da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).
Dr. Makoda ya ce, jagoranci mai ƙarfi da tsari a cikin makarantu shi ne ginshiƙin cimma ingantaccen ilimi. Ya kara da cewa, shugabannin makarantu su dinga tsara ayyuka yadda ya kamata, su rika sa ido kan darussa, da kuma gano wuraren da malamai ke buƙatar ƙarin horo ko ƙwarewa.
Ya kuma jaddada buƙatar jagoranci da ba da ƙarfafawa ga malamai a kai a kai, yana mai cewa gwamnatin jihar na da cikakken shirin ci gaba da horas da malamai a matakin firamare da sakandare, tare da tabbatar da cewa ana biyan su albashi kafin ko a ranar 25 ga kowane wata.
Kwamishinan ya gode wa British Council bisa shirya wannan taro, sannan ya shawarci shugabannin makarantu da malamai da su nuna godiya ta hanyar yin aiki tukuru domin ƙara bunƙasa tsarin ilimi a Jihar Kano.
Abdullahi Jalaluddeen, Kano