2025-12-05@08:31:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10
«tsayawa takara»:
An ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, da wasu mutum shida a ranar Litinin bayan sun kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu. Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, haɗa baki wajen yin laifi, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai miliyoyin Naira. APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa Lokacin da aka fara sauraren shari’ar, lauya mai kare gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya ce sun shirya fara gabatar da shaidu, amma lauyoyin Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suka nemi ƙarin lokaci,...
Da yake miƙa takardar naɗin, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo, ya taya sabon Sarkin murna, tare da kira gare shi da ya bi dokokin gwamnati da na ƙasa wajen gudanar da mulkinsa. Ya ce gwamnatin jihar ta tabbatar da naɗin ne bayan ta binciki cancanta, da halayya, da tarihin mulki na sabon Gung Zaar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025
Kobi ta ce, an samu buƙata daga wajen mutane bakwai, inda aka tantance su domin fafata neman sa’a, daga baya mutane uku suka janye suka bar mutane huɗu domin fafata neman nasara a zaɓen. “Bayan gudanar da zaɓen, Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (Rtd) shi ne ya yi nasara. “Za a gabatar da sakamakon nasarar da ya samu wa gwamnan domin amincewar da gabatar wa Gung-Zaar na farko takardar naɗinsa a matsayin Sarkin masarautar Zaar,” sanarwar ta shaida. Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da al’ummar Sayawa ke zanga-zangar adawa da yunƙurin gwamnatin jihar Bauchi ta Bala Muhammad wajen naɗa musu wani a matsayin Sarkin masarautar Sayawa wato (Gung Zaar). Masu zanga-zangar dai sun bayyana...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal, Abdussamad Dasuki, ya ce ba zai tsaya takara a zaɓen 2027 ba. Dasuki, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin bai wa matasan Najeriya damar shiga harkokin mulki. El-Clasico: Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2 Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2011 yake majalisar dokoki, kuma yana ganin zai fi dacewa idan aka bai wa matasa dama a dimokuraɗiyya. “Najeriyar da muke mafarki za ta tabbata ne kawai idan mun yi sadaukarwa,” in ji shi. Ya ƙara da cewa bayan tuntuɓar iyalansa da jagororinsa, ya yanke shawarar bai zai sake tsayawa takara ba don ya gaji ba, sai don bai...
Jam’iyyar APC reshen Jihar Borno ta rage wa mata kashi 50 cikin 100 na farashin fom ɗin tsayawa takara, makonni gabanin zaɓen kananan hukumomi da za a gudanar a ranar 13 ga Disamba, 2025. Da yake sanar da hakan a Maiduguri, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Bello Ayuba, ya ce an ɗauki matakin ne domin magance matsalar ƙarancin kuɗi da ke hana mata shiga siyasa da tsayawa takara. Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni “Wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da muke yi na samar da daidaito ga mata a fagen siyasa. “Muna son ganin mata da yawa suna jagoranci a matakin ƙasa, suna ba da gudummawa...
Lokacin da mai gabatar da shirin, Seun Okinbaloye, ya tambaye shi ko ya damu saboda yawancin ‘yan ƙabilar Ibo na goyon bayan Obi, Kalu ya cd, “A’a, kawai ban son yin magana a kansa.“Idan kana son na tattauna a kan Peter Obi, to ka gayyace mu duka mu biyun mu zauna a tattauna ta awa biyu; kai za ka zauna a tsakiya, shi a gefe ɗaya, ni kuma a ɗaya gefen. Sai mu tattauna.”“Peter Obi ba jagorana ba ne. Ni ne ɗan siyasa mafi shahara daga yankin Kudu maso Gabas. Na taɓa lashe jihohi biyu a ƙarƙashin jam’iyyar PPA, kuma na taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa.“Kuri’u na miliyan 4.9 na samu a shekarar 2007 har yanzu suna nan. Jam’iyyata ta...
Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, sun gana ranar Alhamis a Abuja, a yayin da ake ci gaba da hasashen kafa kwakkwaran kawancen adawa gabanin zaben shugaban kasa na 2027. Manyan ’yan siyasar na Kudancin Najeriya dai sun mamaye tattaunawa a bakunan jama’a a baya-bayan nan a matsayin wadanda za su iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar APC. Kodayake har yanzu Peter Obi yana cikin LP, amma yana mu’amala da jam’iyyar kawancen adawa ta ADC ke jagoranta. NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya 2027: Malamai sun gudanar da addu’o’in nasarar Tinubu-Barau a Kano Jonathan kuwa, wanda har yanzu dan jam’iyyar...
Majalisar tsarin mulkin kasar Kamaru ta amince da matakin haramta wa babban abokin hamayyar shugaba Paul Biya Maurice Kamto tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba. A watan Yulin da ya gabata ne dai hukumar zabe ta fitar da Kamto daga jerin sunayen ‘yan takarar da aka amince da su. Hukumar ta bayyana cewa an hana Kamto tsayawa takara ne saboda ya tsaya takara a karkashin tutar jam’iyyar Manyedem, wadda ita ma ta goyi bayan dan takara na biyu. Kamto ya daukaka kara a cikin kwanaki biyu. Sai dai shugaban majalisar tsarin mulkin kasar, Clement Atangana, ya amince da hukuncin haramta masa tsayawa takarar. Ba a iya samun damar jin ta...
Eze ya gode wa waɗanda suka kafa ADA saboda ƙoƙarinsu na ceton Nijeriya daga hannun shugabannin da ba sa bin tsarin dimokuraɗiyya. Ya ce sun nuna ƙwazo da ƙaunar ƙasa. Ya ce, “Kun nuna bajinta da kishin ƙasa ta hanyar ƙoƙarin ƙwato mulki daga hannun shugabannin da suka haddasa rikice-rikice, garkuwa da mutane, talauci, yunwa da kunya ga ƙasar nan.” Eze ya kuma yi addu’ar cewa Allah Ya taimaka musu su samu nasarar ceto Nijeriya daga hannun shugabanni marasa ƙwarewa da tausayi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
A ko da yaushe kasar Sin na tsayawa tare da kasashe masu tasowa a matsayinta na kasa mai tasowa kuma mamba na wadannan kasashe. Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, Lou Qinjian ne ya bayyana hakan a ranar Talata a taron manema labarai, inda ya ce, kasar Sin za ta rika shiga a dama da ita, kuma za ta kasance mai bayar da shawarwari kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Da yake tsokaci game da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigar da su daga kasar Sin, Lou ya ce, daukar matakin da Amurka ta yi bisa radin kai ya saba wa ka’idojin kungiyar...
