Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, Hukumar ta ce, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a Masar ranar Litinin, “Dole ne duniya ta ga abinda ya kasance a Gaza.

Kungiyar ta ce a yanzu dole ne a bar duniya ta ga irin barnar da aka yi, wa matsugunai, da kuma haddassa wahalhalun ga bil adama sanadin yakin da Isra’ila ta yi na kisan kare dangi a Gaza, wanda ya kashe kusan mutane 68,000, yawancinsu mata da yara.

“Kafofin watsa labarai na duniya, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya, kotun ICC, dole ne su sami damar yin amfani da bayanan kisan gillar da Isra’ila ke yi,” in ji kungiyar kare hakkin bil’adama.

A tsawon shekaru biyu na kisan kiyashi, Isra’ila ta katange Gaza, tare da takaita ayyukan jin kai a zirin, da kuma kai hare-hare ta sama da kasa ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya jefa fararen hula cikin mummunan yanayi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kenya : An dawo da gawar Raila Odinga gida October 16, 2025 Iran Ta Bukaci Kasashen Kungiyar NAM Su Hada Kai Don Fuskantar Rashin Bin Doka Da Oda A Duniya October 16, 2025 Iran: Yawan Karafan Da Ake Sayarwa Zuwa Kasashen Waje Ya Kai Dalar Amurka Billion $4 October 16, 2025 Falasdinu: Masu Gadin Gidajen Yari A HKI Sun Sun Daki Marwan Barghouti Har Ya Suma October 16, 2025 Venezuela Ta Bada Sanarwan Sabbin Matakan Tsaro A Kan Iyakar Kasar Da Colombia October 16, 2025 Tarayyar Afirka AU, Ta Jingine Samuwar Madagaska Daga Cikin Kungiyar October 16, 2025 Iran Ta Jaddada Cewa: A Shirye Take Ta Tattauna Amma Ba Zata Amince Da Juya Akalarta Ba October 16, 2025 Kasashen Iran Da Tunusiya Sun Jaddada Karfafa Alaka A Tsakaninsu A Bangarori Da Dama October 16, 2025 Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Shari’ar Neman Hukunta Isra’ila Kan Batun Gaza October 16, 2025 Gwamnatin Kamaru Ta Gargadi Dan Takarar Da Ya Shelanta Kansa A Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe October 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano

’Yan bindiga sun harbe wata tsohuwa har lahira a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Yankamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.

Sun kai harin ne a daren ranar Asabar, a lokacin da mutanen ƙauyen ke kwance.

Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32

Yayin kai harin, ’yan bindigar sun kuma sace aƙalla mutum uku.

Yankamaye, wani ƙaramin ƙauyen manoma ne, ’yan bindiga da ke tserewa daga maƙwabtan jihohin Kano ne suka fara kai musu hare-hare.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’ai domin bin diddigin maharan.

Mazauna ƙauyen sun ce ’yan bindigar sun isa ne a kan babura inda suka ajiye su daga nesa, sannan suka shiga ƙauyen a ƙafa.

A yayin taron majalisar zartarwa da aka gudanar kwanan nan, Gwamna Abba Yusuf, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar tsaro.

Ya kuma ce hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da ɓarayi shanu a wasu yankunan Arewacin jihar, babban abin damuwa ne.

Gwamnan, ya ce suna aiki tare da hukumomin tsaro don magance barazanar da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Ya bayyana ƙananan hukumomin da abin ya shafa; Kunchi, Tsanyawa, Gwarzo, Kabo, Sumaila, Shanono, Tudun Wada, Doguwa, da Rogo.

Amma ya ce hukumomi na ci gaba da ayyuka domin toshe hanyoyin shigowar ’yan bindiga da kuma kare al’ummomin ƙauyuka.

“Duk da wasu ƙalubale da ake fuskanta a nan da can, jama’a su kwantar da hankalinsu, gwamnati tana aiki domin magance duk wata barazana ga zaman lafiya,” in ji Yusuf.

Gwamnan, ya kuma goyi bayan matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ayyana dokar ta-ɓaci a harkar tsaro a faɗin ƙasar nan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano
  • Shugaban Najeriya Ya Mika Sunaye Sabbin Jakadun Kasar su 32 Ga Majalisa Domin Tantancewa
  • Hizbullah Ta Bukaci Shugaban Cocin Katolika Na Duniya Yayi Tir Da Hare-haren Isra’ila
  • MDD Ta Bukaci Isra’ila Da ta Kawo Karshen Mamayar Da Tayi wa Yankunan Falasdinawa
  • Kamfanin Kera Jiragen Sama Na Airbus Ya Bukaci  A Dawo Da Jiragen Sama Samfrin  A320 Saboda Gyara
  • MDD ta yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa
  • Shaikh Niam Qasem: Hizbullah ce Za ta Mayar Da Martani Lokacin Da Ya Dace Kan Kisan Kwamandanta
  • Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Ta Soki Shirin Donald Trump Na Bayyanata A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
  • Isra’ila Na Barazanar Sake Shiga Wani Sabon Yaki Da Kasar Lebanon