An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro
Published: 12th, October 2025 GMT
Sufeton ƴansanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya maye gurbin Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya, CP Ajao Adewale, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba da yake fuskanta saboda rashin gamsuwa da aikinsa tun bayan karɓar ragama daga CP Benneth Igwe.
Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa sauya shi ya shafi yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a Abuja, musamman bayan harin fashi da makami da ya yi sanadin mutuwar mai gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin ɗin ARISE, Somtochukwu Maduagwu, da mai gadi Barnabas Danlami, a Katampe, ranar 29 ga Satumba, 2025.
Wata wasiƙar cikin gida daga shalƙwatar ƴansanda ta tabbatar da cewa CP Miller Gajere Dantawaye ne aka naɗa sabon kwamishinan ƴansanda na FCT, yayin da DCP Wilson Aniefiok Akpan aka tura shi zuwa jihar Kogi.
Wasiƙar, mai lamba TH.5361/FS/FHQ/ABJ/SUB.6/213, ta bayyana cewa wannan sauyin na ɗan lokaci ne har sai hukumar aiyukan ƴansanda ta ƙasa (PSC) ta amince da cikakken naɗin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025
Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025
Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025